Babban Dalilin Da Yasa Akayi Wannan Canjin Kudin Najeriya
Dalilin da yasa gwamnatin Nigeria ta bullo da maganar chanjin kudi shine: Tana so ta karfi da yaji a koma kan tsarin cashless policy ne.
Saboda haka idan mutum wai yana mafarkin cewa wataran sababbin kudaden nan zasu dawo su cika gari kamar tsofaffin, to ya yaudari kansa.
Gwara ma tun da wuri kada ka batawa kanka lokaci kawai ka karbi zamani, wannan tsarin ko ba dade ko ba jima sai yazo ya same ka. Shiyasa kawai kabi.
Akwai bankuna na Fintech masu masifar sauri da ake amfani dasu kamar dai sauran bankuna, suna da masifar saurin tsiya fiye da ordinary bankunan mu.
Da yawa akwai wadanda ke ganin sufa babu yadda za'a yi su iya ajiya a wannan bankunan, saboda ai ba'a ganin su a gaske. Amma maigidana kwata-kwata abin ba haka bane.
Irin wadannan bankuna ba'a samun matsala dasu irin wacce kake samu da bankunan mu, musamman gurin tsansfer dss. Suna da masifar sauri.
Sannan matuqar ka gansu suna aiki a nigeria, to fa sunyi rejista ta CBN ne kamar yadda sauran sukayi. Kuma ko guduwa sukayi, toh CBN zata biyaka kudinka, cikin jinginar kudin da kowane banki suke ajiyewa kafin a barsu suyi operating a kasar.
Misalin su akwai Kuda Bank, wanda jiya da yau suke gyararraki ya dan tsaya aiki. Akwai Opay, wanda shi idan ma aka maka transfer tun kafin transfer din tazo zasu maka albishir din zuwanta. Sai kuma irin su palmpay dss.
Abokina zamani ne kawai, duk da gwamnatin kasa ta saka al'ummar ta cikin masifa da bala'i duba da yadda basu bayar da isasshen lokaci ba. Magana ta gaskiya a nan gurin gwamnatin kasa ta ki duba masalar al'ummar ta.
Amma fa magana ta gaskiya idan mu kalli rashin amfanin abu, to muyi adalcin kallon amfanin sa. Tsarin cashless policy ci gaba ne, kuma tsari ne da in Sha Allah nan gaba idan abun ya tafi yadda yakamata Naira zatayi darajar ban mamaki.
Musamman yunkurin da CBN tayi na daina amfani da tsarin payment na yan jari hujja irin su MASTER CARD da VISA dss. Anyi tsarin payment na kasar, wanda zai bawa kasar iko akan kudinta ba wai turawa ba.
Magana ta gaskiya kenan, amma nasan akwai wadanda fadar hakan bazai musu dadi ba saboda adawar siyasa. To mu dai gaskiya daga bangaren mu zamu fade ta koda fadarta na nufin yabo ga makiyin mu.
Wallahu Ya'alamu......
Author: Muhammad Abdulrahman Sheka
Copying
Shieykh.......✍️
Post a Comment