Amfanin Man Ridi Ga Lafiyar Bil'adama:

 Amfanin Man Ridi Ga Lafiyar Bil'adama:



Amfanin man ridi ga kiwon lafiyar dan-adam na da yawan gaske sai dai mutum ya ambaci iya wadanda Allah Ya sanar da shi, sakamakon yadda har yanzu ake gudanar da bincike kan magungunan da za a iya samu daga man ridi. 


Daga cikin amfanin man ridi ga lafiyarmu har da inganta lafiya da karawa gashi kyau, haka nan ana amfani da man ridi wajen gyaran fata, man ridi na taimakawa wajen kara karfin kashi, da kula da lafiyar zuciya, baya ga amfani da man ridin da ake wajen rage damuwa. Har ila yau, man ridi na taimakawa wajen inganta lafiyar jarirai da kuma ba su kariya daga wasu cututtuka da sauran su.


Saboda haka wannan shafi na ku mai farin jini na "Lafiyar Iyali" ya himmatu don kawo mu ku irin tarin baiwar da Allah Ya yiwa ridi, da kuma irin amfaninsa ga lafiyar dan-adam.


1. Gyaran Gashi


Al'ummomin daban-daban na amfani da man ridi wajen gyaran gashi tun shekaru aru-aru da su ka gabata. Baya ga haka, a wani bincike da aka gudanar kan amfanin man ridi ga lafiyar dan-adam ya nuna cewa, man ridin na kunshe da wasu sanadarai da ke taimakawa wajen hana zubewar gashi da kuma wanzuwar launin gashi.


2. Man Ridi Na Inganta Lafiyar Kashi


Binciken masana ya gano yadda ridi ke kunshe da sanadaran 'Copper da kuma calcium' wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen girma da karfin kashin dan-adam. Wannan na nufin cewa, matukar mutum ya rinqa zuba man ridi cikin abincinsa na yau da kullum, ba shakka ya kama hanyar samun lafiyayye kuma kakkarfan kashi. Har ila yau man ridi na taimakawa mutanen da shekarunsu su ka fara ja, su samu kwarin kashi.


3. Man Ridi Na Inganta Lafiyar Hakori


Man ridi na taimakawa mutane su samu kariya daga wasu cututtukan hakori da dasashi. Wannan dalili ya sa, likitocin hakori ke bai wa jama'a shawarar amfani da man ridi domin riga-kafin kamuwa da cututtukan hakori da kuma inganta lafiyar bakinsu gaba daya. Likitocin sun ce, mutum zai iya samun kariya daga ciwon hakori ko dasashi ta hanyar kurkurewa bakinsa da man ridi. Sun tabbatar da cewa, kurkurewa baki da man ridi na sanya hakoran mutum su kasance farare, kuma ya na hana rubewar hakori da dasashi.


4. Man Ridi Na Inganta Lafiyar Jarirai


Wani bincike da aka gudanar a wata jami'a mai suna, "University College of Medical Sciences", dake birnin Delhi, na kasar Indiya ya nuna cewa, idan ana amfani da man ridi wajen shafewa jikin jariri zai samu ingantacciyar lafiya, kuma ya na taimakawa wajen girman jaririn. Har ila yau shafewa jikin jariri da man ridin na taimakawa wajen saukin gudanuwar jini sannan kuma jaririn zai samu yin barci yadda ya kamata.


5. Maganin Ciwon Gyambon Ciki


Ana amfani da man ridi don maganin gyambon ciki. Yadda mai wannan larura ta gyambon ciki zai yi shine, ya samu man ridi sai ya hada shi da madara ya gauraya su ya ke sha sau 2 q kullum, wato safe da yamma. Zai ke sha da safe kafin ya karya kumullo, haka nan da dare zai sha awa guda kafin a kwanta barci.


6. Man Ridi Na Kara Ruwan Nono


Ana amfani da man ridi don kara ruwan nono ga mace mai shayarwa. Idan mace na fama da matsalar karancin ruwan nono sai ta hada man ridi da garin hulba ta ke sha sau 2 a rana wato safe da kuma yamma. Don karin bayani dangane da wannan matsala karanta makalarmu mai taken 'Amfanin hulba ga lafiyar dan-adam.


7. Ana Amfani Da Man Ridi Domin Riga-kafi


Bincike ya tabbatar da cewa ana amfani da man ridi wajen riga-kafin kamuwa da cututtuka, musamman ma cututtukan da kan shafi gabobi.


Wasu daga amfanin man ridi sun hada da:


8. Kariya daga ciwon-daji (Cancer)


9. Gyara fatar jarirai da sanya su

natsuwa da bacci


10. Hana rubewar hakori, kogon

hakori da sauransu


11. Kariya daga ciwon asma da

cututtukan numfashi


12. Rage hawan-jini


13. Rage yawan sinadarin

"Cholesterol"


14. Kariya daga ciwon-suga


15. Inganta lafiyar kwalkwalwa da

sauransu.

Post a Comment

Previous Post Next Post