Amfanin Ganyen Gwanda A Jikin Macce Yana Matse Ciki Da Wajen Macce

 Amfanin Ganyen Gwanda A Jikin Macce Yana Matse Ciki Da Wajen Macce 



Ganyar gwanda na kumshe da sinadiran lipid, calcium, iron, bit C, bit B6, folate, Thiamine, magnesium, phosphorus, potassium, sodium, zinc, Bit A, bitamin E, Bitamin D, D2, D3, Niacin da sauransu.


Ganyar gwanda a binciken wassu masanan kiwon lafiya da sukayi ( Dr. Nam Dang da Dr. Gajawik A) sukace na dauke da sinadarin lycopene sidari ce wacce take kashe kwayar cutar daji.


Molecular Nutrition and Food Research tayi bincike kuma ta gano ganyar gwanda na dauke da sinadiran papain da chymopapian masu rage kumburi a sassa da dama na jikin dan’adam.


A sakamakon arziki na wannan sunadarai, idan ana dafa ganyar gwanda ana shan ruwan ta da izinin Allah zai magance wadannan matsaloli:


1- Ganyar gwanda na habaka garkuwar jikin dan’adam.


2- Tana cire kasala tare da karfafa gabobi da lakar jikin dan Adam.


3- Tana saukaka narkewar abinci da kuma tace shi daga cututtuka.


4- Tana inganta lafiyar zuciya tare da ba ta kariyar cututtuka.


5- Tana hana kamuwa da ciwon sukari ta hanyar daidaiton sinadarin Insulin a jikin dan Adam.


6- Ganyar gwanda tana taimaka wajen kashe kashe tsutsotsin ciki.


7- Ganyar gwanda na narkar da sinadiran cholesterol da yawansu a jiki illa ne.


8- Tana azurta jikin dan Adam da wadataccen jini.


9- Tana Hana kumburin jiki haka kuma tana kara lafiyar hantar dan Adam.


10- Ganyar gwanda na wanke kazamta da wani abu mai cutarwa da ya yi laulayi a kan babbar hanji.


GARGADI:

kada mai juna biyu ta yi amfani da ganyar gwanda domin tana motsa na'uda, haka kuma kada ta wuce kofi guda biyu a rana, domin yawan shan ruwan ganyen na kawo hajijiya da gani dishi dishi.


Post a Comment

Previous Post Next Post