Amfanin Daddawa A Jikin Dan Adam

 Amfanin Daddawa A Jikin Dan Adam 


Wannan Wani Ilmi Ne Da Yakamata Kowacce Macce Ta Sani Musamman Yammatan Zamanin Da Ake Yiwa Gorin Basu Iya Abinci Ba. 


Kada Kiyi Wasa Da Koyon Abinci Ko Sanin Wani Sirrin Abinci Yana Kara Miki Kima Matsayinki Na Macce 



Daddawa a Hausar mafi yawan jahohin Arewacin Nijeriya, a Sokoto suna kiran ta da suna Daudawa. A harshen Englishi ana kiran ta da locust bean cake.


Kabilar Tibi suna kiranta da suna ‘Nune, Yoruba suna kiranta da ‘iyere’, su kuma kanuri suna yi mata suna da ‘runo’.


 A harshen Igbo suna ce mata ‘Ogiri’ su kuma fulani suna kiranta da ‘ makari’.


Wadannan harsuna suke nuna cewa kusan kowace kabila a Nijeriya tana amfani da Daddawa wadda a mafi yawa ake yi da diyan dorowa.


Ko a baya ga Nijeriya, kasashe masu yawan gaske a Afirika suna da wannan itaciyar da ake sarrafa diyanta a maida su daddawa, kamar Sudan, Sierra Leon, CotediCboire , Senegal, Chad, Gambia, Cameroon, Zaire, Guinea bissau, Ghana, Mali, Niger republic, Burkinafaso, Togo, Uganda da kuma Benin republic.


A mafi yawa mun dauka cewa talaka marasa karfi kawai ke amfani da daddawa, ba tare da la’akari da amfanin ta galafiyar jiki ba.


Wani zai gommace ka ba shi naman naira dari biyu da ka bashi daddawa ta naira dari biyar, bai san yana hanawa jikinsa wasu muhimman sinadirrai masu amfanar jiki a badini ba.


Wasu sun dauki daddawa kayan wari wadanda kayan gyaran abincin talaka ne kawai.


Abubuwa da dama masu amfanar jikinmu mukan yi watsi da su kodan rashin dandanonsu a baki ko rashin kamshin da suke da shi.


A hakika daddawa tana da matukar amfani kwarai da gaske.


Ga kadan daga cikin muhimman abubuwan dake kumshe a cikin Daddawa.


-Kashi 29 na lipid.


-Kashi 35 na protein.


-kashi 16 na carbohydrate.


-fat. -calcium. -Ash. -fibre.


-Carotenoids(Bitamin A. -Ascorbic acid (bit.C).


Daddawa tana dai-daita sinadiran cholesterol.


Daddawa tana taimakawa dan inganta lafiyar idanu.


Daddawa tana taimakawa dan narkar da abinci.


Daddawa na maganin bugun jini da yawan haihawar jini.


Wannan ya biyo bayan binciken da wasu masana su ka yi wanda aka wallafa a mujallar nan mai suna ‘science Journal dake a birnin Dakar, na Senegal.


Inda suka baiwa beraye don su ga ko tana dai-daita gudanan jinni a jiki.


Daga karshe dai sakamakon ya nuna cewa yawan amfani da daddawa yana taimakawa don rage bugun jini a jiki.


Ana amfani da ganyen dorowa bayan an tafasa shi sai a yi wanka da ruwan yana magance zazzabi da yawan kasala da ciwon jiki.


Tana dai-daita aikin abinci a cikin ciki.


Tana fada da kwayoyin cuta.


Tana dauke da sinadiran tannis wadanda ke da amfani wajen tsaida gudawa.


Sassaken itaciyar na maganin gyambon kafa kona fata a jiki. Harwa yau ana amfani da sassaken a maida shi gari a dunga amfani da shi dan maganin kuturta.


A kasar cotediboire suna amfani da ganye da sassaken dorowa dan maganin zafin jiki na zazzabi da kuma wasu magunnan iska.


Idan kana fama da yawan tashin zuciya a duk sanda ka ci abinci to dunga amfani da daddawa ka gani.


Idan kana fama da karamcin gani to ka zanka shan miyar daudawa.


Ganinka zai inganta. Daddawa tana inganta lafiyar ciki.


Tana gyara yawu ta yanda za ka rinka cin abinci kana jin dandanonsa.


Tana taimakawa garkuwar jiki dan samun damar yakar kwayoyin cuta a sanadinta na samuwar bitamin C.


Daddawa tafi aiki a cikin miyar kuka musamman idan an saka nama.


Amfani da miyar kukar da aka girka da daddawa tare da tafarnuwa na magance basir da cuttukan ciki da fungal da sauran kwayoyin cuta.


[Home]African locust beans is the popular name to many people around the world, it belongs to the plant family Mimosaceae of the Leguminosae, it is often called “Neatehtu” among the Wollof tribe in The Gambia and Senegal, “Dawa- Dawa” by the Hausa, and “Ogiri” by the Igbos of Nigeria. African locust beans have been used as a seasoning and adding flavor in cooking soups and stews. It is boiled and fermented through a process that requires continues boiling until is ready for fermentation.


It is a very popular ingredient in traditional African cuisines, it grows in long slender pods when premature, it is green and dark brown when mature. It contains a sweet pulp and seeds, the yellow pulp which contains the seeds that are used later to prepare the African locust beans after been cooked and fermented before you can consume it or used in our daily soups and stews. African locust bean is a black strong smelling seasoning which is rich in lipid, protein, and carbohydrates. African locust beans help in boosting your immune system, relieve diseases like diarrhea, diabetes and reduce the chance of heart attack. It is also used as a remedy to counteract the effects of poison like snake bites and scorpion stings.  


African locust beans is a multipurpose tree, the bark of the African locust bean tree is also used as a vapor inhalant to relieve toothache and ear issues. It is also used as a remedy for leprosy, bronchitis, skin disorders, sores, ulcers, malaria, hypertension, and many sicknesses. The bark is also combined with lemon heal wound and ulcer. African is a blessed continent to have such a tree of great importance because of the herbal and food benefits is associated with the African locust bean tree and by-product. It is a good source of income for rural dwellers in Africa as everything within the African locust bean tree is of great importance.


African locust bean has been put on research and tested on rats to find the impacts and it is shown that it can control blood pressure because it helps in reducing arterial blood pressure when you eat the right quantity. It is also a good substitute to spicy or seasoning cubes and contains tannin and astringents substances found in many plants.


1. Good vision


Due to the natural ingredients and nutrients found in African locust bean, therefore, consuming it will help to have a better vision especially people with eye issues like cataract, minus eyes and myopia.


2. It can treat stroke


Stroke is when the blood supply to the brain is suddenly interrupted which is fatal. Research shows that consuming a good amount of African locust bean will definitely help you against such sickness.


3. Reduce cholesterol


Cholesterol which can cause some blockage within the blood vessels can lead to heart issues. Eating locust beans can help your body control the amount of cholesterol found in our bodies.


4. Treat Diarrhea


Because of the amount of tannin found in African locust bean, it will heal diarrhea, which is a gastrointestinal disorder with the symptoms of frequent watery bowel movements. Consuming African locust beans will help you relive diarrhea.


5. Treat hypertension


Hypertension also referred to as high blood pressure occurs when is a long-term medical condition in which the blood pressure in the arteries is persistently increasing above the normal level. Therefore consuming a good amount will help people with hypertension.


6. Helps control blood sugar level


The human body requires sugar to produce enough energy but it should be stable otherwise if unstable of high will cause diabetes. Therefore consuming African locust bean will help you control blood sugar level. 


7. Improve digestion


Eating a good amount of African locust beans can improve digestion. Good digestion will give you a healthy body as the excretion process in the body will be facilitated which will prevent constipation.


8. Healthy weight


Underweight is not healthy and vice-versa which is sometimes not easy to be normal weight or just gain weight for underweight. Eating African locust bean will help you gain weight in a natural way.


9. Heal Wounds


As mentioned above it can be used to treat ulcer wounds internally by eating the beans as well as external wounds. The leaves when pounded can be applied on wounds and the bean can be paste on the wound to heal the wounds.


10. Reduce Fever


Consuming a good amount of African locust bean can reduce fever. It was traditionally used to reduce high fever which is still practiced in some rural African communities and also send away evil spirits because of its unpleasant smell.


African locust beans consist of many vital nutrients which are cherished by the body. Therefore consuming healthy African locust beans will give you good health.

Post a Comment

Previous Post Next Post