Yadda Ake Rabuwa Da Kaushin Kafa Har Abada Da Yardar Allah

Yadda Ake Rabuwa Da Kaushin Kafa Har Abada Da Yardar Allah 




Akwai wani abu da masana suka aminta dashi shine mace me dumin jiki musamman hanaye da kafafu ana samunta da danshi ajikinta, (ni,ima) atakaice mayuyacin al'amarine asamu mace irin wannan ta zauna batada ni,ima ko kuma tana yawan bushewa, da akwai wani masanin halayyar dan adam wanda ke zaune a kasar sudan wato (mursi al'bhagdi) yayi magana akan kaushi nau,ine na bushewar jiki wanda hakan yana hana ruwa bubbugowa daga jikin dan adam fiyeda wanda bashi dashi, wannan hujjace babba da take nuna namiji zaifi bukatar mace me danshi a kafafu hannaye da dumin jiki, 

kowacce mace tanada ni,ima saidai yanayin shan maganin mata ya banbanta kalar ni,imarta, saidai wata kuma tanada arancin ni,ima sai tanashan magani zata samu, dan haka a takaice idan kinada halitta me kaushin hannu da kafa kina jarraba magungunan laushin kafa da hannu,

hanyoyi 6 da akebi don samun laushin kafafu da hannaye

(1) KHAL TUFFAH

ana tafasa ruwan sai azuba masa man zaitun ana wanke kafa dashi,

(2) MAN RIDI

ana shafawa kafin a kwanta da safe awanke da ruwan dumi,

(3) MAN KADANYA

shi kuma sai an narkashi a zuba man zaitun aciki ana shafawa,

(4) AYABA

Ayaba ana markada bawon asamu leda a saka kamar meyin kunshi idan ya kwana acire a wanke,

(5) ZUMA

Ana amfanida sakar zuma kafin a kwanta a goga da safe a wanke da ruwan dumi,

(6) ALBASA

zaki raba jar albasa gida biyu saiki samu wani kyalle ko leda ki daure Rabin albasan a wajen wannan ruwan jiki Yana taba wajen kibarshi yayi kamar sa'o,i uku saiki cire ki wanke da ruwan dumi.

Post a Comment

Previous Post Next Post