Yadda Ake Karin Girman Kugu Da Karin Ni'ima Da Miyar Kubewa

 Yadda Ake Karin Girman Kugu Da Karin Ni'ima Da Miyar Kubewa





1. Ana amfani da kubewa wajen maganin ciwon sugar wato Diabetes. Saboda abinda ake kira (fiber ) a cikinta, na amfani wajen daidaita yawan suga a cikin jiki, wandakuma ke rage karfi ciwon sugar ko ma

maganinsa.


2. Masu ciki kan iya amfani da kubewa domin ingancin lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki domin kubewa na kunshe da dimbin Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki (cells) da kuma ( folates) don haka kubewa na hana haihuwar jariri mai dauke da wasu nakasu a jikinsa kuma na sa jaririn ya girma a ciki kuma da koshin lafiya yadda ake so. 


Haka kuma jaririn da ke ciki zai iya amfana da dimbin Vitamin C dake cikin kubewa domin kare lafiyarsa.


3. Kubewa na maganin ciwon koda. Wani bincike daga jami?ar Jilin ta kasar Sin ya tabbatar da wannan. Binciken. Ya nuna cewar wadanda suke ci ko shan kubewa a kullun sun nuna nasarar rashin lalacewar koda musamman wadanda ke da ciwon sugar domin kusan kasha 50 na masu matsalar koda sun samu matsalar ne saboda suna da ciwon sugar.


4. Kubewa na kara lafiyar dubura (colon) wato karshen babban hanji.yana wanke hanji da tumbi sosai don haka yana maganin kumburin ciki. 


Kuma Vitamin A da ke cikin kubewa na taimakawa lafiyar wani abu kamar majina (Mucous membranes) na cikin babban hanji.


5. Kubewa na maganin Asthma da wasu cututtukan numfashi. Yana dauke da Vitamin C da ke taimakawa hanyoyin numfashi.


6. Kubewa na kara ingancin fatan jikin mutum yay i laushi da santsi kamar yaukin kubewa. Ka ga mutum kullun kamar yaro ko yarinya a fatarsa.


Yana kuma taimakawa wajen mayar da fatar da ta lalace (Meosis).


7. Yana matukar maganin Anaemia wato karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai. Kuma yawan amfaani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har yayi maka lahani ba (blood coagulation).


8. Yawan sha ko cin kubewa na matukar rage nauyin jiki ga wadanda suke jin kiba ya musu yawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post