Wani Ciwon Da Ke Damuwar Kananan Yara A Lokacin Sanyi (Yadda Ake Magance Ciwon Kyanda)

 Wani Ciwon Da Ke Damuwar Kananan Yara A Lokacin Sanyi (Yadda Ake Magance Cutar)



CIWON BAKON DAURO [MEASLES]


Ciwon kyanda ko bakon dauro ahausance shine abunda ake Kira measles a turance. wani nau'in ciwo ne da yara da dama kanyi fama dashi saboda busasshiyar iska ta hunturu ko hazo dake kadawa. Musamman irin wannan yanayin da ake ciki a Nigeria.


Wato su kwayoyin cutar iska suke bi sai ashakesu yayin da akai tari ko atishawa. 


Shi ciwon Kwayar cutar VIRUS ke haddasashi shyasa yake da hatsari domin virus abune mai wahalar magani kamar yadda ake gani a masu HIV.


Kwayoyin cutar sun fi kama yara ’yan kasa da shekaru biyar (5) wadanda garkuwar jikinsu batayi kwari ba. An kiyasta cewa adan tsakanin watannin kadan yara fiye da dubu biyu da dari hudu 2400 ka iya riga mu gidan gaskiya musamman garuruwan mu na Arewa.


ILLAR CIWON KYANDA


- Kyanda na kashewa mururus

- Tana jawo makanta

- Tana jawo kurumta

- Tana sa mutum ya zama bebe

- Tana ta6a kwakwalwa


ALAMOMIN CIWON


Alamomin ciwon suna zuwa ne mataki-matiki. Wato shine da farko yaro za aga yafara da:-





1- Ciwo kamar mura, harda majina


2- Aji dan Tari ya fara biyo baya.


3- Idanu su rika yin ruwa suna ja, 


4- Daga nan sai zazzabi mai zafi.


5- Yaro ya kasa cin abinci. 


6- Daga nan sai a ga wasu kananan kuraje sun feso masa duk jikin, har cikin baki. 


Wadannan kuraje sukan yi kaikayi sosai. Daga nan kuma ko dai jiki ya yaki kwayoyin cutar ko kuma suci gaba da jawo lahani. 


MISALI; daga makogoro har cikin kunne sukan iya shiga su kawo ciwon kunne. 


- A ido ma sukan iya huda farin nan na ido, aka Yaro ya fara lumshe idanu baya son haske. 


- Idan suka shiga kirji kuma su kawo numoniya. 


Sai andauki matakin karawa yaro karfin garkuwar jiki kafin ya iya shawo kansu. 


Sannan duk wannan yakan dauki misalin sati biyu yaro na fama.


Yara masu karyayyar garkuwar jiki kamar masu ciwon kanjamau da ciwon suga kenan sunfi shan wahala, tunda jikinsu yakan dau lokaci mai dan tsawo yana yakarsu.


Amma idan yaro yana da kwarin garkuwar jiki baza ama gane kyanda bace, domin ’yar mura kawai zai yi ta kwana uku zuwa hudu ya warke.


Wasunsu ma ko murar basayi, amma zasu iya sawa wani ciwon.


HANYOYIN KARIYA


1. Hanyoyin kariya daga wannan cuta kan fara tun daga lokacin da aka haifi yaro. Idan aka ba jariri nonon uwa zalla har wata shida batare da ruwa ba to garkuwar jikinsa za tafi ta sauran yara karfi, ta yadda bazai rika saurin kamuwa da cutuka sosai ba. 


2. Sai kuma kai yara allurar riga-kafin kyandar [measles vaccination] domin kare yara daga kwayar cutar, wacce akeyiwa yaran daga watanni tara. 


Domin yawanci wadanda suke yin ciwon zaka samu ba'a yi musu allurar riga-kafin ba.


2. Sauran hanyoyin kariya sun hada da saurin kai mai ciwon asibiti 


3. Ware masa wurin kwanciya daban dana sauran yaran gida don kada ya yada musu.


4. Samar masa soson wanka nasa na daban don kada ruwan majina kona kurajen jikinsa susa kwayoyin cutar da jikin soson ya dauka aje ana sawa wanda yake lafiya. 


5. Sai kuma yawan wanke hannayen sauran yaran gidan da sabulu. 


6. Idan yaron babbane Ko makaranta mai ciwon bai kamata abari yaje ba na tsawon ’yan wadannan kwanakin da yake ciwon, don kada ya yada ta.


7. Idan karamine kema bai kamata ku fita unguwa ba dashi a irin wannan Hali saboda gudun yaduwar ciwon, tunda yawanci kwayoyin cuta iska suke bi.


8. Adena kwantar da mai ciwon a rigingine ma'ana kansa yake kallon sama! Wannan kuskure ne abun na iya shafar kwakwalwa, saboda haka akwantar agicciye hannun dama ko hagu.


9. Idan da dare ciwon ya fara kafin awayi gari akaji zazzabi me zafi, kila harma da Tari to musamman in ansan akwai labarin ciwon acikin gari, za'a iya bawa mai ciwon Paracetamol matakin farko don sauke zazzabin. Sai kuma Amoxicillin domin kiyaye faruwar secondary infection na wani sashin. Gari na wayewa a nufi asibiti.


10. Ake wanke ma masu fama da ciwon fuska akai-akai.


11. Asami sinadarin Vitamin A ake ba mai ciwon, musamman ranar farko da ciwon ya bayyana, rana ta biyu da kuma rana ta takwas koda sauki ya samu lokacin.


ALLAH YA KARE AMIN


SIrrin RIke GIda 



Post a Comment

Previous Post Next Post