Menene Uric Acid,ya Ake Samun Sa Da KUma Illolin Sa A Jiki.
Yana da kyau ku karanta bayanin nan, Sannan kuyi share ga Alumma.
MAGANIN SA :
GANYEN MANGWARO ( 12 ):
za'a dafa Ana sha safe da yamma Kofi daya
Masu tambaya menene uric acid,wani sinadari ne da ake samu a cikin nau'ikan abinci ko abinsha da yake da purine a cikin sa.
Yayin da kaci wannan nau'in abu mai purine a ciki hanta ita ce ke tacewa tare da raba abinda kace zuwa kowanne sassa,wannan purine yana fitar da uric acid.
Shi kuma uric acid koda ita ce take tace ahi daga jikin mutum,idan yayi yawa ko kuma koda bata iya tacewa yadda ya kamata zaibi hanyiyin jini ya ya haifar da matsala.
Kuma matsalar da yake haifarwa shine a gabobi da jijiyoyin mutum,zaka rika fama da rikewar gaba ko gwiwa.
Sannan idan yayi yawa a jini yana haifar da gout,wani kumburi ne a kafa,musamman babban yatsan mutum ya rika zafi yana ciwo.
Idan uric acid yayi yawa yana hana mutum tafiya ko tashi ko motsi yadda yake so.
Akwai masu fama da wannan matsala ta uric acid amma basu sani ba suna dauka sanyi ne.
Saboda haka a rika zuwa asibiti kafin neman magani.
Allah yasa mu dace.
Post a Comment