Hadin Turaren Magani Domin Tsari Daga Kishiya

 Hadin Turaren Magani Domin Tsari Daga Kishiya 



 GIDAN SAI DA KAMSHI

FARAR HUMRA
BAKAR HUMRA

SABULUN GYARAN JIKI
GYARAN NONO
TURAREN KAYA/DAKI/JIKI_

KI GYARA JIKINKI UWARGIDA TURAREN GAF-GAF NA TSUGUNO TURAREN JIKI DA KAYA

kisani uwargida ba wai sai maigida yana da wadata ne zakiyi tinanin neman
ababen da zasu gyara maki jikiba domin kina tinanin duk wani abu na gyaran
jiki tsada ne dashi.

sai dai *sirrin◦rike◦ Gida* na mai tabatar maki ba haka bane, domin zaki
iya gyaran jikinki cikin sauki da kudi kankane.

1. sabulun salo zaki hada da sabulun ditol sai zuma matuka zai gyara maki fata, sai dai yana da mahimmanci ki san yanayin fatarki.
 In har mai saurin daukan zafi ce sabulun salo kar ya yi yawa.  





② sabulun dove nevea, garin zaitun, habbattu sauda, jar dilka kurkur, sabulun
gana, sabulun dudu osun, lemun tsami, zuma mai kyau, madaran tirare iri biyu
mai matukar kamshi madara gari duk zaki goge sabulun sai ki hadasu guri
daya ki dama zasu hade ki sanya su a fridge ko guri mai sanyi.

▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
③ bushashen zogale,curry, alovera, da na'ana'a zaki hadasu ki dan sanya man
zaitun amma ki tabbata kadanne zaki dinga shafawa fatanki zatafi kyau da
kyalli.

▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
④ yawaita shan kayan itace mai sanya fatarki kyau
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
⑤ yalo/data (garden egg) na matukar boye shekaru domin yana sanya fatanki
tatsaya danya shar tana nuna kasa da shaikarunki..
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
⑥ cin nama da zuma ko nama da nono na gyara fata kuma yana taikamakawa
maza gurin mazakuta.
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
TURAREN GAF-GAF NA TSUGUNO

・ itacen gaf-gaf
・ sukari
・ jawul
・lemon tsami
・ misik
・farce
・ hawi
・ garin sondol
・gallo
・madarar turaren zuzan
・madarar turaren sondol rose
・madarar turaren binta sudan
・madarar turaren sondol
・garin sondol
・madarar turaren mena

kamar yadda zaki yi turaren al'ud wanda na koya yanzu zaki yi,sai dai farcan bayan kin kona daka shi zakiyi yayi laushi, shi kuma itace gaf-gaf din idan kika siyo zaki ganshi kamar kashi, sai kin jika kin wanke, sannan ki baza ya bushe, sannan ki farfasa aturmi, sannan kiyi kamar yin turaren al'ud sai ki dinga
turara gabanki da shi ana turaren jiki madashi, amma gollon da hawi ma
dakawa zakiyi yayi gari ki zuba wani a gun soya ruwansukarin ki juya wani
bayan kin gama dai al'ud.
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
              TURAREN JIKI DA KAYA

 itacen hawi da inik

yan sirara ne kamar saiwa, amma wasu suna da kauri, dukkan kayan hadin
turaren al'ud da shi zaki yi amfani, kamar yadda aka yi turaren wuta na al'ud haka zakiyi, sai dai zaki iya canja kalolin madararon tuaren da kike so, zaki dinga turara jikinki da shi da kayan sawarki.
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
  GIRMAN NONO

◦ ganyen mai da tsohuwa yarinya
◦ saiwar sabara
◦ganyen sabara
◦ gadali wanda ya fidda da a jikinsa, to dan da ya fito za'a dauka & dawa ko alkama.

a hada wannan ganyen da saiwoyin a dake su yi laushi, sannan a sami garin
alkama ko dawa, a zuba ruwa kofi daya a tukunya a sa garin maganin cokali
daya a ruwa idan ya tafasa sai a dama kunu, wato (salala) da wannan garin
dawa ko na alkama, a dinga sha.
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔ 
  GYARAN KAFA TUNDA SANYI


maganin kaushin kafa yana hana ni'ima 
・ man kadanya
-・ man zaitun
-・ safa
-・leda

ki hada man kadanya da man zaitun gurin guda ki kwaba guri guda, idan zaki
kwanta sai ki shafe tafin kafar ki dashi, sannan ki zira kafar a leda ki daure ki
saka a safa dan kar ledar ta kwance yayin da kike bacci, da safe idan kin tashi sai ki wanke kafar da sabulun ki sa dutsen wanke kafa ki goge kafarki sosai,
idan kina haka kullum ko kin dinga fashin kwana daidai, zaki gyara miki kafa, kaushi ya fita kafar tayi kyau, ta yi taushi.
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
   MAGANI WARIN JIKI, KASHI , BAKI

 lemon tsami
 farar kanwa

ki matse lemon tsaminki kamar guda a
uku masu ruwa sannan ki zuba garin
farar kanwarki akai, kikwaba tayi kauri, sannan ki shafa a hammatarki, idan
kuma duk jikinki ne yake wari, sai ki shafe jikinki, idan yayi kamar minti uku
sai ki je ki yi wanka ki wanke jikinki sosai amma fa kar ki barshi ya dade a
jikinki, minti biyu zuwa uku za ki wanke..
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔②▔▔▔▔▔▔
 lemon tsami
ki goge a hammatarki ki barshi zuwa rabin awa, sai kije ki yi wanka( abinda
yasa kuka ji ina fadin a goga a hammata, dan duk wani warin jiki daga
hammata yake fita ko dakua ba ta hammatar aka same shi ba).
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
③ alimun
ki daka alimun ki tankade yayi laushi ki dinga shafawa a hammatarki, kamar
hoda, idan kina shigarana ko kinyi gumi baza a dinga jin warin jikin ba.

4 sabulu
▾ lemon tsami
 ▾ zuma
▾ alim

"ki sami kalar sabulun da kike wanka da shi ki goga ki daka alimun ki tankade ki zuba a kai ki matse lemon tsami kadan, ki sa zuma cokali biyar, ki
hada ki kwaba ki dinga wanka da shi, dukkan jikinki.

▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
⑤ turare madara me kamshi sosai kamar kala uku

 dakakken alim dinki wanda yayi laushi sosai
ki kwabe su sosai, ki dinga shafawa a hammarki, duk sanda zaki shafa ki sa
danyatsanki ki juya sosai, garin alim din ya hadu da madarar turaren sannan ki
shafa bayan warin jikin har kamshin jiki yake sakawa.

▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
 

YADDA AKE HADA HUMRA FARA, BAKA, CULUCTURE, TURAREN WUTA. NA KAYA DA NA TSUGUNO

  BAKAR HUMRA

'yan'uwa mata in a yi muku tuni da ku rike turare da kyau, dan turare maganadisu ne na jan hankali, amfanin da turare a jikinki, sutturarki, gidanki
yana sa megida ya kara samun nutsuwar zama da ke, kuma ko yaushe zai
dinga son kasancewa da ke..
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
                  BAKAR HUMRA

❑ mahala
❑ hawi
❑ farce
❑ turaren marakana
❑ turaren sondol na ruwa dan awo
❑ turaren amarya
❑ madarar turaren abaraidadi
❑ madarar turaren suzan
❑ turaren me sanyin ruwa kalar da kike so mara mai ko

☛ yadda zaki yi ki dake mahala dinki, bayan kin soya sama-sama sai ki dake
ta ta yi laushi, shi ma hawi ki dake ki tankade ,ki jika farcenki a ruwan omo
ko clean, idan yayi kamar awa biyu da jikawa, sai ki dora farce da kika jika da
ruwan clean ya yi ta dahuwa, har sai yayi kamar awa biyu ko uku ruwan na
tafasa da farcen a ciki, sannan ki sauke ya huce, sai ki sami reza ko brush din
goge baki ki dinga kankare farcen da rezar ko brush din, daya bayan daya,
wannan nama-naman da ya taso na jikin farcen sai ya fita gaba daya, idan kin
gama kankarewa sai ki shanya farcen ya huce, sannan ki zuba farcen a kasko
kiyi ta juyawa a kan wuta har sai farcen ya kone yayi baki, sannan ki dake
yayi laushi sosai yadda zaki hada shi ne ki zuba ruwan turarenki na marakana kwaiba daya ta
awon mankuli, sannan ki zuba turaren sandol na ruwa gwangwanin madarar
ruwa guda daya, turaren amarya ma gwangani daya, turare me sanyi ruwa mara maiko kalar da kike so gwangwani daya, ki sa madarar turaren aborai dadi
cikin kwaibar fiya-fiya ta madarar suya ma cikin kwalbar fiya-fiya ki sa garin
mahala cokali biyu na abinci garin hawi cokali biyu garin farce ma cokali biyu
ki juya sosai, bayan kin gama hadawa sai ki rufe humrar ki barta ta tsumu a
gun mai zafi ko ki dora kaya a kanta inda ba zata sha iska ba har zuwa sati
daya ko biyu ko sama da haka, idan ta tsumu sosai ta yi kamshi zaki iya yin humra da ruwan turaren amarya wato ya fi yawa turaren marakana kuwa sai ki sa gwangwani daya yadda dai kike so, wannan dakakken su farcen zaki ga in kin zuba kwalba suna yin kasa, amma zai saka humrar ta dinga kara tsumuwa tana kara kamshi
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
      FARAR HUMRA

turaren alajin na ruwa ko na marakana ko na matan arewa
✭ jan ambur
✭ farin ambur
✭ misik
✭ madarar turaren kwamando
✭ madarar turaren suzan
✭ madarar turaren sarkin turare
✭ madarar turaren sandol
✭ madarar turaren ismiyaki

zaki yi ki daka farin ambar dinki wanda ake sayarwa a kasuwa guda uku,
sannan ki daka jan dan kanti guda uku, sai ki zuba a kan ruwan turaren alajin
ko marajana ko matan arewa roba daya, ki sami misik dinki guda hudu ki
zuba a kofin silver ko a tukunyar silver ki dora a kan garwashi zai narke, idan
ya narke sai ki yi sauri ki juye a cikin ruwan turaren da kika zuba garin
abubuwan, sannan ki daka misik din ki sa cokali uku sannan ki zuba madarorin turaranki ko wanne cikin kwalbar fiya-fiya ki jua sosai ki rufe ya tsumu, wannan garin misik dinda ambar din shi zai dinga kara tsuma humra ta
dinga kara kamshi za ki iya rufewa kwana bakwai ko zuwa sati biyu ta tsumu
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
       TURAREN WUTA NA DAKI


amma shi wannan yadda ake hada shi dabban ba da kyau kuma da irin
kamshinsa duk da itacen irin daya ne , abin bukata sune:

◦ farce
◦ sukari
◦ lemon tsami
◦ jawul fari
◦ misik
◦ garin sandol
◦ madarar turaren jamila
◦ madarar turaren wanis
◦ madarar turaren sabon yayi
◦ madarar turaren binta sudan
◦ madarar turaren kamfani
◦ madarar turaren naludu
◦ madarar turaren dan duwala
◦ madarar turaren kafin kafi
◦ madarar turaren sandol
◦ madarar turaren abarai dadi
◦ turaren ruwa mai maiko

yadda zaki yi ki sami itace al'ud dinki daya, ko biyu sai ki jika shi da madarar
turaren jamila da madarar turaren wanis, da madarar turaren sabon yayi, sannan
ki sa turarenki mai maiko na ruwa irin wanda ake aunawa a dogwayen kwalabe
sai ki jika da wadannan turaruka ki rufe ki bar shi ya jiku har yayi kwana, bakwai bayan sati daya sai ki bude itacen alud din da kika jika da turare, idan kuma kilo daya ne sai ki sa gwangwani daya, idan sukarin gwangwani biyu ne sai ki zuba ruwa cikin karamin kofi ki matsa lemon tsami hudu a kai, ruwan sukari, idan kuma gwangwani daya ne sai ki zuba ruwa rabin karamin kofi ki matsa lemon tsami biyu a kai sannan ki saka garin jawul cokali daya da ruwan lemon tsami da sukarin ki sa misik kwaya uku a ciki, sannan ki debi garin farcen da kika barza ki zuba kadan a kai amma shi ma farcen zaki gyara shi
kamar irin gyaran da aka ce za'a yi masa a hadin humra, sai dai shi bayan an
soye barje shi ba daka shi lukwi ake yi ba idan kin zuba sai ki bar shi yayi ta
dahuwa har sai ruwan sukarin ya fara ja,sannan ki zuba itacen al'aud din naki
a kai kiyi ta juyawa idan ya dahu sosai sai ki sauke ki juye a faranti ki baza
sannan ki zuba garin sandol dinki a kai da garin dakakken misik da garin
dakakken jawul...
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
       YADDA AKE HADA TURARE.


Turare mai kamshin dadi.maisuna.ruda maigida
Kayan hadi

・ halud kg3 sendal kg 1
・ hawi kg half
・ farcen gwangwanin tumatir
・ miski cokali 4
・ sarki turaren babba 1
・ binta saddan babba 1
・ hafsa 1
・ bokur 1
❒ kafi kafi
❒ assasarubiya 1
❒ oassion 1
❒ massarubiya 1
☐ ledus sahi 1
☐ Onte man shw 1
☐ sanyin turaren cheri 1

karamin sandal 1 madarar turaren ambar
da farko zaki dora farce a wuta da ruwa.idan ya tafasa na tsawon minti 30
saiki wanke da omo da soson waya idan ya wanku saiki baza ya bushe saiki
dakashi sama sama sannan ki dora tukunya awuta ki zuba suga gwangwani 2

da ruwa cokali 8 idan ya narke yayi ja ya tsinke yayi tsululu saiki zuba halud
da hawi da sandal kici gaba da jujjuyashi sosai.idan yasoyu da ruwan suga
saiki juye acikin babbar kwano.kibari yayi minti 20 sannan ki daka miski kar
yayi danshi sosai ki zuba ki daka jawi shima kar yayi danshi sosai.ki zuba
saiki zuba madarar turaren duka ki zuba farce shimaki jajjagashi ki rufe tsawon awa 48 sannan kizuba a kwalba ko roba.

Duk inda kinka wuce ko kinka zauna saikin bar kamshi.koda yaushe dakinki
cikin kamshi.duk wayannan abubuwan dana lisafa za'a iya samun su.duk inda
ake sayar da magungunan musulunci.

▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
     HUMRA


Humra turare ne wanda aka samo asalinsa daga Arabs (Larabawa)

 kuma Bare-bari suka dauka a matsayin kwaikwayon,al’aadar.

sannan ta yadu a kasar Hausa, kusan duk mata sun,karbe shi sakamakon irin ingancinsa tare da cikakken muhimmmancinsa. 

Turaren Humra na dauke da sinadarai masu
kamshi, ana kuma hada shi ne da saiwoyi da nau’oin turarruka daban-daban, kuma ta kan zo a nau’in bakar humra ko fara har ma da koriya.

Abubuwan da ake hada bakar Humra da su
▾ Ruwan turare (Alchohol) litre 1
▾ Madarar turare 1/6 litre
▾ Ambir 4 (gwayar shi)
▾ Garin sandal cb 2
▾ Garin Humra cb 3
▾ Garin soyayyen kaninfari ck1
▾ Mahalan (gari) ck 1/2
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
        Yadda ake hada bakar Humra:

 ①. Za’a sami ruwan turare a zuba masa nikakken ambir

②. Sai a kawo garin nikakken

 tankadadden sandal da garin Humra da soyayyen garin kaninfari, da garin mahalan, a zuba a hada su a girgiza, a kawo madarar turare irin nau’in da ake
bukata a zuba, zai iya kasancewa fiye da daya ko fiye idan sun hadu sai a zuba a cikin kwalabar turare a rufe.

              Farar Humra da Koriya

Ita ba’a sa mata garin Humra, shi ne kadai babu, a cikin koriyar Humra kuma kala ake sa wa koriya, ita ma din kadan, kuma babu garin Humra a cikinsa. 
Wannan kawai shi ne bambanci tsakaninsu.
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
       BAKAR HUMRA


◆ Mahala
◆ Farcen,hawi
◆ Turaren sandal
﹆ Madarar turare kamar kala ukku
 Turaren bahur ko aladin

Ki dake mahala ko aladi, ki dauko mahala da hawi da farco ki tankade su ki hade su guri guda sai ki dauko wadannan turarukan ki hada wuri guda sai ki kawo dakakkun kayan ki xuba a kansu xaki ga sunyi kasa, shine yake sasu tsamuwa amma farcon sai kin wanke kin soya, idan ba dakakke bane kika samu
▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔▔
     FARAR HUMRA


・ Hawi
・ Madarar matan arewa
・ Ambar
・ Miski cokali hudu
・ Ruwan turaren matan arewa

Da farko xaki daka hawi ya daku sosai sannan sai ki dauko kasko ko ki soya sama- sama kar ki barshi ya kone idan kuma bai soyu ba wari yake, sannan sai kuma ki cika amur da miski su daku sai ki xuba a cikin maxubi sai ki xuba madarar turaren matan arewa sai ki xuba sauran kalolinmadarar turaren

Post a Comment

Previous Post Next Post