Hadin Maganin Ɓaure Mai Kyau

 Amfani 15 Na Baure Ga Lafiyar Dan Adam



Baure 


Tsawon shekaru masu yawa da ska wuce, ‘Baure wani nau’i ne na dangin kayayyakin marmari da ya shahara a duniya ta fuskar dandanon shi da kuma amfani ga lafiyar jikin dan Adam. Masana ilmin kimiyya da fasahar abinci wato Food Scientist and Technologist, sun bayyana cewar muhimmancin Baure wajen magance wasu cututtuka masu yawa, wannan ya fara ne daga ciwon sikari zuwa cututtukan fata. ‘Ya’yan Baure ‘Baure shi ya kunshi sunadarai masu yawa wadanda kuma suke gina jiki da suka hada da fiber, antiodidants, bitamin A, bitamin C, bitamin K, B bitamin, potassium, magnesium, zinc, copper, manganese da kuma iron.:


Wani binciken da aka gudanar a cikin shekarar 2016 ya tabbatar da cewar, sinadarin ficusin da dan itaciyar baure ya kunsa na taka rawar gani wajen magance radadin ciwon sikari. Ga dai wasu kadan daga cikin tasiran da baure ke yi wajen magance cututtuka da kuma bunkasa lafiyar jikin dan Adam:


1- Maganin kwarnafi da tashin zuciya.

2- Hawan jini.

3- Bunkasa lafiyar zuciya da jini.

4- Ciwon daji wato cutar Kansa.

5- Rage nauyin jiki.

6- Inganta lafiyar mazakunta da kuma ni’imar ma’aurata.

7- Ciwon basir mai tsuro wato dan kanoma.

8- Cutar farfadiya.

9- Tace mafitsara.

10- Yana da amfani wajen inganta lafiyar fata. 1

11- Maganin zazzabi.

12-Ciwon Kunne.

13-Cututtukan fata (karzuwa, makero, maruru, kirc da kuma, kyasfi).

14-Bunkasa lafiyar hanta.

15-Cutar asma da dangin cututtukan da suka shafi hunhu.

16-Inganta karfin kashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post