Bayan Kwalliya Wani Abu Da Yakamata Kisani Game Da Lalle

 Matsayinki Na Cikakkiyar Macce Yakamata Kisan Fa'idar Lalle Guda 9



Rashin Sani Hakan Zai Iya Saki Ji Kunya Allah Ya Kiyaye 


Bayan kwalliya, karanta anfanin lalle 9 ga ya mace:


- Lalle na cikin wani sinadarin da ke dauke da alfanu iri iri, kuma addini ta kwadaitar da muyi lalle akwai sirrika acikin sa.


- Menene Amfanin Lallai?


 lalle wasu zasu dauka zanen henna nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake magana akai.


1) Na farko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama.


2) Yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafa sannan yana maintaining dumin mace, bi ma ana


yana inganta ni’imar mace ba tare da ya gushe ba.


3) Ga duk mace mai infection, ta tafasa lalle in ya dan huce sai ta yi sit bath dashi na sati biyu


in Allah ya yarda zata warke.


4) Ana iya sha ruwan lalle cokali 1 don wankin dattin ciki amma banda masu ciki.


5) Don gyaran Fata; lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi


natural toner ne wanda ba bilicin yake yi ba amma yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata.


6) A bangaren gyaran fuska, tana sa fuska tai kyalli, laushi, da haske in an kwaba da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan.ki kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum 30 mins kafin wanka sai Kinga bambanci a cikin sati biyu Insha Allahu.


7) Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man


zaitun za kiga canji.


8) Ga masu fama da pimples, yar’ uwa ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskar ki bayan watanni kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga hasken fuska da laushi.


9) sannan gamai son kamshin fata, Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket ki sa garin lalle ta jika tai já zir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki Bayan kinyi wankan sabulunki sai ki dauraye jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki in sha Allahu.


Ku ci gaba da bin mu a Facebook: 

SIrrin RIke GIda 

Post a Comment

Previous Post Next Post