Babban Kalu-Balen Da Mata Ke Fuskanta Saboda Tsarki Da Ruwan Sanyi
KIN SAN MAHIMMANCIN TSARKI DA RUWAN ZAFI?
ILLAR TSARKI DA RUWAN SANYI
ruwan sanyi yana sanyaya gaban mace, kuma yana kashe kwayoyin halittar jikinta sannan ya kan daskarar da ni'imar mace kuma ya sanyata jikin ya kasance kullum a sanyaye.
RUWAN ZAFI
yana sa mace ta kasance da dumi a koda yaushe kullum yana amfani wajen kashe kwayoyin cututuka gaban mace, yana kuma amfani wajen narkar da ni'imar mace Don haka mace dole sai ta dage..
SHAWARA GA MATA
YANA DA MATUKAR MUHIMMANCI MACE ta zama tana gyara jikin mai gidanta, saboda shi gyaran jiki abune wanda yake da muhinmanci ga dan adam, ya zauna yana gyara jikin shi yana kuma kulawa da tsaftar fatarsa . Sau da yawa za'a samu mace tana da gyaran jikinta amma shi namiji babu ruwanshi ko kuma a samu wani lokacin shi namijin yana kula da na shi jikin amma ita mace bata yi, idan an samu ke mace kina gyaran jikinki shi namiji baya yi a matsayinki na matarshi abinda ya kamata kiyi, ki rinka kwatanta masa kada ki barshi a cikin datti,
abdulahi dan abbas(RA) yace ina tsayawa na yiwa matata kwalliya kamar yadda zata yi min kwalliya dubi rayuwar MANZON ALLAH(S.A.W) da iyalinsa aisha tace idan annabi yaci kwalliya yasa kayansa zai fita masallaci ni nake sa masa turare, don haka yana da kyau ace kuna yiwa juna kwalliya sosai sannan ku rinka zabawa juna kayan sawa, kowa a cikinku yasan kalar kayan da dayan yafi so ya tabbatar sune yake sa masa yake gani, wannan yana daga cikin abin da ke kara sawa ku shaku da junan ku sosai
KI RIKE WADANNAN SIRRIKAN DOMIN KI ZAUNA DA MIJINKI LAFIYA
- KI guji binciken wayar mijinki kada ki rinka daukar wayarsa ba tare da izininsa ba
domin dai ko ba komai 'yan magana suna cewa kazantar da baka gani ba tsafta ce
* guji yin zargi akan mijinki na da daman mata ki sa zuciyarki kowane lokaci mijinki na da daman kara aure tunda addini bai hana masa ba, madadin ki ta bin diddiginsa yana neman mata ki dage da yi masa addu'a domin samun kariya daga fadawa zina
- ki daina yawan sa ido da bin diddigi me mijinki yake yi domin da yawa daga cikin maza sanya musu ido a kan duk wata harka tasu tana kawo matsala tsakanin miji da mata..
* ki guji yawan korafi an yi min wannan gobe an yi miki kaza kada ki kasance mace mai yawan fushi a gun mijinki ki rinka bari sai an yi miki laifi kin tara sannan sai ki fada kuma shima ba a cikin gadara zaki fada ba
* ki guji hana mijinki saduwa da ke domin kun samu sabani, hakan kuskure ne da zai ji ya tsani saduwa da ke ko da kuwa lokacin baku samu sabani ba hakan sai ya sanya sha'awarki ta fita daga cikin zuciyarsa
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :
Post a Comment