Abubuwan Da Ke Haddasa Kaikayin Matse-Matsi Da Kuma Yadda Ake Magance Su
Da mace da namiji su abu daya ke kawo musu. Amma tunda namiji ne bari nafi jingina tambayar dakai.
Kaikayin matse matsi abune mai takura toh saide hanyoyin shigarsa yawanci tanan ake samun hanyar fitarsa.
Hanya biyu ce Kode ka dauko ta hanyar saduwa; ko kuma amfani da bayan gida mara tsafta musamman toilet din mu irin na karkara masu karancin tsafta sannan sama da mutum 10 na amfani dashi,
Ko kuma toilet na masu wadata irin wanda ake zama akai. Ko kuma masu yin open defecation masu zuwa kashi gonaki, ko cikin ginin da ba akammala ba.
Don haka idan kana da aure ta yiwu jikin matarka ka dauka, ita kuma yafi mata sauki ta dauko a bandaki me karancin tsafta acikin gida ko gidan wasu saboda mafitsarar mata bata da zurfi.
Idan kuma mutum baida aure amma Yana da alaka da mata masu zaman kansu nan ma zai iya dauka.
Don haka kai kadai ko kasha magani bazai barka ba, dole sai matarka Tasha, inkuwa kai kadai ne to zakaje asibiti abaka magani, sannan dole kake kula da tsaftar wajen fitsarinku, ake hada gishiri da omo ana wanke bandakin.
Sannan kake canza boxer dinka sau 2 zuwa uku arana, kake kuma sa gishiri a ruwan wankin,
Kake tsarki da ruwan dumi, idan ma bana dumin to na sanyin kake sa gishiri ciki.
Sannan abunda na manta tsafta lallai ake aske gashin gaba akai akai wannan ma na jawo kaikayin.
bayan ka karbo magani a asibiti ka kara da shafa MICONAZOLE OINTMENT 2% idan basu Hadama dashi ba zai taimaka, musamman in akwai kananun kuraje.
Post a Comment