Abubuwa Uku Da Ake Yi Da Gwanda Domin Mata Hadi Mai Kyau
Amfanin Gwanda 12 A Jikin Dan Adam
Gwanda
Gwanda wata dan itaciya ce daga jerin ‘ya’yan itace da ganinsu ma ya isa ya sa ka dauka ka kai baka. Ferarriyar, lafiyayyiyar, nunaniyar gwanda na da daukar ido da sanya sha’awar shan ta. Ko shakka babu wannan fa’ida ce da duk wani abinci da ya cika sunansa abinci ya kamata ya samu. Shi yasa ake shawartar iyaye mata da a duk lokacin da suka tashi shirya abinci ga yaransu, musamman ma yaran da ba sa son cin abinci sosai, to, sai su kawata abincin da kaloli ta yadda zai dauki ido tare da motsa sha’awar cinsa.
Bayan ga kasancewar gwanda abinci mai daukar ido, gwanda na da zaki a baka, dadi da karawa kuma da tsoka mai taushi ta yadda gutsara da taunawarta ba ya wahalarwa. Har ila yau, gwanda ba ta da wuyar samu. Ana iya samun gwanda a duk kwanakin shekara, kuma babu wani yanayi da ya ke sa tsadar gwanda ta kai mutum ya kasa sayenta.
Banda wannan kuma ga wasu dalilai har dozin guda za su sa ka sanya gwanda a jerin abincin da ka ke ci a kowace rana:
Dalili na 1:
Gwanda na dauke da sinadarin fibre da na bitamin c da ke hana wani nau’i na kitse da ke taruwa har ya toshe hanyoyin jini ginuwa. Wannan kitse ana kiransa da suna Cholestrol a turance. Sinadarin Cholestorol da na lipid wadanda suna da nasu amfanin a jiki, in suka yawaita suna toshe hanyar jini wanda hakan ke komawa ga sai zuciya ta wahala kwarai kafin ta gudanar da aikinta, wanda hakan kuma kan juye zuwa ga ciwon zuciya.
Dalili na 2:
Gwanda na taimakawa wajen rage kiba ko taiba, saboda kowace gwanda mai matsakaicin girma na dauke da Calories 120. Calories wani nau’i na zafi ne da ke samawa jiki karfi tare da narka taiba. Kasancewar gwanda abinci maras nauyi kuma dauke da sinadarin dietary fibre da ke taimakawa wajen rage nauyin jiki da kuma yawan bukawa ga abinci, gwanda abinci ce da duk mai bukatar rage kiba ya kara a abincinsa na yau da gobe.
Dalili na 3:
Gwanda na dauke da kaso 200 na adadin bitamin C da jikinka ke bukata a kullum. Wannan bitamin C da ke cikin gwanda na taimakawa wajen haifar da kwayoyin halittar antibodies (wasu kwayoyin halitta da ke cikin jini da ke yakar kwayoyin cutar da suke jikinmu da ma wadanda su ke shiga jiinmu a kullum ta hanyar iskar da mu ke shaka, abinci da ruwa da mu ke ci ko sha da ma wadanda ke shiga jikinmu ta kafar gashin jikinmu). Yana da kyau mu fahimci cewa, iya adadin antibodies da ke cikin jikinmu, iya karfin yakar cutar da jikinmu zai iya.
Dalili na 4:
Duk da kasancewar gwanda dan itaciya mai zaki, gwanda na dauke da sinadarai da ke dakile ciwon sikari da hana shi tasiri. Masu dauke da ciwon sikari za su iya amfani da gwanda a matsayin abincin da ba zai tayar da ciwon ba kuma ma yake da tasiri wajen dakushe kaifin cutar haka ma wadanda ba su dauke da cutar za su yi amfani da gwanda wajen karesu daga kamuwa daga cutar.
Dalili na 5:
Gwanda na da yalwar sinadaran bitamin A, beta-carotene, zeaxanthin, cyptoxanthin da kuma lutein. Wadannan sinadarai suna taimakawa wajen wanzar da lafiyar ruwan ido da kuma hana shi gurbata. Sinadarin bitamin A da ke cikin gwanda na taimakawa wajen sanya karfin ido a lokacin tsufa sama da yadda karas da tumatiri ke bayar wa.
Dalili na 6:
Dimbin sinadarin bitamin C da ke cikin gwanda na bada kariya ta musamman ga cutar da ke kama gabobin mutum ta sanya su yi ta radadi da ciwo da ake kira da arthritis a turance. Bincike ya nuna cewa mutanen da ba sa cin nau’ikan abincin da ba sa dauke da bitamin C su ke da hatsarin kamuwa da cutar Arthritis.
Dalili na 7:
Gwanda na dauke da sinadarin papain da ke taimakawa wajen inganta lafiyar sashen jiki da ke da alhakin narka abinci. Sau tari muna cin wani abincin wanda ka iya jinkirta narkewar abinci a cikinmu ko ma ya kawo wani tarnaki ga sashen narka abinci na jikinmu. Sinadarin papain da ke cikin gwanda na taimakawa wajen hanzarta narkewar abinci a jikinmu ya kuma inganta lafiyar ma’aikatar narka abinci na jikinmu.
Dalili na 8:
Haka kuma, sinadarin papain da ke cikin gwanda na taimakawa mace da ke fama da ciwon mara a lokacin al’ada. Ga mace mai fama da irin wannan ciwo na lokacin al’ada, sai ta yawaita cin gwanda gabanin zuwan al’adarta. Hakan zai taimaka wajen rage ko cire irin radadin da ta ke ji a yayin al’adar
Dalili na 9:
Gwanda na dauke da yalwar bitamin E da bitamin C da kuma sinadarin beta-carotane. Wadannan sinadarai na da tasiri wajen hana fata yamutsewa da tattarewa da yin yaushi. Shan gwanda a kullum wata hanya ce da za ta hana tsufanka bayyana. Za ka kasance a kowane lokaci tamkar shekaru biyar kasa da shekarunka na hakika.
Dalili na 10:
Baya ga inganta lafiya da gwanda ke karawa, bitamin A da ke cikin gwanda na samar da wani sinadari da ke habaka girma ko tsirowar suma (gashi), tare da sanya sumar ta yi santsi, sheki da duhu. Kana ta samawa fatar kai danshi ta yadda amosanin kai ba zai samu gindin zama ba.
Dalili na 11:
Yawan amfanin da dan itaciyar gwanda na taimakawa wajen kashe kwayoyin cutar da ke taruwa su gina sankarar da ta shafi al’aurar da namiji ta haifar masa da gwaiwa (prostate cancer) da kuma sankarar da ke kama ‘ya’yan hanji (colon cancer).
Dalili na 12:
Wani bincike na jami’ar Alabama a Amurka ya nuna cewa gwanda na daya daga cikin kayan abincin da ke yaye ko huce gajiya
Post a Comment