Abubuwa Goma Da Yakamata Ka Sani Game Da Ciwon Apendix Da Yadda Ake Magancewa

 Abubuwa Goma Da Yakamata Ka Sani Game Da Ciwon Apendix Da Yadda Ake Magancewa 



1. Afendis wato "appendix" a turance, wani ɗan zunɓutu ne mai kamar jela a mahaɗar ƙaramin hanji da babban hanji. Girmansa yai kama da girman yatsan hannu.


2. A ina afendis yake? Afendis yana nan a ciki a kwiɓin dama daga ƙasan cibiya kaɗan.


3. A likitance, afendis ba shi da wani takamaiman aiki a jiki ɗan Adam. Sai dai wasu masanan na cewa afendis na ɗauke da wasu ƙwayoyin garkuwar jiki.


4. Ciwon afendis wato "appedicitis" a turance, ciwo ne a afendis sakamakon kumburin afendis saboda wasu dalilai.


5. Abubuwan da kan haddasa kumburin afendis sun haɗa da: harbin ƙwayoyin cuta kamar bakteriya, toshewar bakin afendis daga dunƙulallen turɓayan abinci ko kashi, ciwon daji/sankara da sauransu.


6. Alamun ciwon afendis sun haɗa da:


 - ciwo a kwiɓin dama ƙasa da cibiya ƙaɗan.


 - ciwo a kewayen cibiya wanda daga bisani kan zarce zuwa kwiɓin dama.


 - ciwon da ke ta'azzara yayin tari ko wani yunƙuri.


 - ciwo yayin da aka danna kwiɓin dama da cibiya.


 - tashin zuciya da amai.


 - Rashin sha'awar cin abinci.


 - matsakaicin zazzaɓi, da sauransu.

 


7. Ciwon afendis na buƙatar tiyatar gaggawa domin cire shi, musamman idan ya riga ya fashe ko kuma ana tsoron fashewarsa a kowanne lokaci.


8. Barin ciwon afendis ba tare da an cire shi ta hanyar tiyata ba na da haɗarin gaske, domin fashewarsa na nufin fantsamar ƙwayoyin cuta da ke ƙunshe ciki zuwa dukkan sauran kayan ciki.


9. Hanyar kariya daga ciwon afendis: babu wata sahihiyar hanyar kariya daga ciwo afendis; sai dai masana kimiyyar abinci na ganin cewa ciwon afendis bai cika kama masu cin datsar hatsi, gayayayaki da 'yayan itatuwa ba - wato masu ƙaurace wa sarrafaffen abinci kenan.

 

10. Yaushe ya kamata ka ga likita? Da zarar ka fara jin wasu daga cikin alamun da aka ambata a sama garzaya asibiti domin duba ka.

Post a Comment

Previous Post Next Post