Yadda Zaki Tsufa Da Nononki Tun Yarinyatarki Har Zuwa Tsufanki

 Yadda Zaki Tsufa Da Nononki Tun Yarinyatarki Har Zuwa Tsufanki



YADDA ZAKI TSUFA DA NONUWAKI

Nonuwa, ko nono ko kuma mama kamar yadda wasu suke cewa, wasu kulatai ne guda biyu da suke tsira daga kirjin mace da zaran ta soma balaga, ma'ana fitowarsa yana cikin alamomin balaga na mata.


Bayaga halitta ne da Mahalicci yayi domin alamta balaga ga mace, har ila yau yana cikin alamomin dake bambamta jinsi na mace dana namiji, domin duk macen data haura munzalin balaga kuma akaga cewa babu wani tsiro na nonuwa daga kirjinta ya zama matsala. Haka nan namijin da duk aka ganshi da nonuwa a kirjinsa tamkar mace, to ansan da matsala. Haka kuma nonuwan dama yafi na hagu tsayi na kowace mace.


Haka nan kuma Allah Ya halicci nonuwa a jikinki mace ne domin ta samu wajen adana abincin jinjirin da zata haifa, ganin ruwan nonuwan mace shine abincin da jinjiri yake iya amfani dashi a matsayin abinci na wani lokaci mai tsawo kamin ya soma cin wani abinci mai nauyi.


Har ila yau shine abu na farko dake bayyanar da kyau 'ya mace da zaran sun soma fita daga kirjinta kuma suka kai munjalin girmansu. Don haka nema masana kwalliya da kyele-kyele suke cewa macen datake da cikenken nonuwa tafi kyau idan tayi kwalliya fiye da wacce bata da cikan kirji. Anan manufa shine baya ga abubuwan da muka ambata a baya, nonuwan mace suna da da kawata mata kyaunta fiye da mara shi.


A bangaren jima'i kuma, nonuwan mace yana dauke da kusan kashi 35 wajen samar da dadin dake cikinsa, domin idan kika kasa mata kashi 100, 70 daga cikinsu sha'awarsu na saurin motsawa ne da zaran anyi musu wasa da nonuwansu. Tabbasa da wadannan dalilan kadai ba zamu ga cewa, nonuwa a jikin mace ba karamin hikima da baiwa Allah Yayi a halittansu ba, don haka ya zama dole ga mata su bi duk wata hanyar da zasu bi na halas domin ganin cewa suna kula dasu.


Sai dai kuma shi kansa nono a jikin mace kowacce da irin yadda Allah yayi mata nata halittan, wasu matan harsu tsufa su koma ga Mahaliccinsu basu saka rigan nono saboda kankantar nonuwansu, wasu kuma rigan nonon ma bayan isansu saboda girmansa. Wasu nonuwan madaidaita ne marasa faduwa komin tsufan mace, wata ko da zaran ta soma haihuwa sun zama silifa. Gasu nan iri -iru, mai kan tasa, mai bakin aku, babba da jaka da dai sauransu. Koma wani iri ne a kirjinki mijinki yana sha'awar ganinki dasu shi yasa ma watakila ya aureki dominsu, don haka ya zama wajibi ke kuma ki kular masa dasu sosai da sosai.


Wasu mata nada jahilcin cewa, idan mace tana yawan shayarwa nonuwanta suna iya kwanciya da sauri. wasu matan ma cewa suke muddin mace tana barin mijinta yana yawan wasa da nonuwanta suna iya kwanciya tunma bata tsufaba. Tabbas haihuwa yana iya jawo nonuwan mace su kwanta, sai dai kuma a yadda kimiya na zamani ya shigo a yanzu, mace tan iya haihuwa 'ya'ya dozun ba tare da nonuwanta sun kwanta ba. Kuma tana iya mikar da nonuwan nata bayan ta gama haihuwa ko kuma a duk lokacin datake bukatar yin haka.

A yanzu haka likitoci na zamani sun samo hanyoyi da dama domin ganin mata masu sha'awan ganin sun tsufa da nonuwansu sunyi amfani dasu. Wasu kwayoyi ne na hadiya, wasu man shafawa ne, wasu kuma aikin tiyatane ake yiwa mace na irin duk yadda take bukatar ganin nonuwanta sun kasance.


Sai dai kuma duk matan data yanke shawarar gyara nonuwanta ta wadanan hanyoyin, ya zama dole ta tuntubi likita ne domin samun sha'awarar irin wanda zai dace da ita domin kaucewa daga samun wata illa na rashin neman shawaran.

Duk da yake kyaun nonuwa halitta ne na Allah mahalicci, baya ga kuma hanyoyin kimiya da masana suka gano na yadda suke gyara ko kwaskwariman nonuwa a yanzu, da akwai kuma wasu hanyoyin da mace takan iya binsu domin kula da nonuwanta kamar haka.


Cin abinci mai: Duk macen datake samun abinci mai kyau mai gina jiki tana iya gyaran nonuwanta ta wannan hanyar, domin duk tsufar mace muddin tana koshe, kuma cikin koshin lafiya, tana iya tsufa na nonuwanta a girjinta. Yana da kyau mata su rika cin abinci masu gina jiki irinsu kayan marmari, madara, kifi, nama da ire irensu.


Kula da girman Jiki: Dole ne macen datake bukatar ganin nonuwanta suna da kyaun ta kaucewa yin girman jiki sosai, haka kuma kada ta bari ta rame. domin wadannan abubuwa biyu da suka yi yawa suna jawo dalilin zuban nonuwa a kirjin mace. Domin yin kiba yakan jawo fatarki ta sake, wanda hakan kuma zai jawo dalilin kwanciyar nonuwan naki. Rama kuma yakan jawo rashin fatar da zata rike nonuwan har agansu a tsaye. Don haka wadannan abubuwan biyu dole mata su kula dasu muddin suna bukatar tsufa da nonuwansu.


Rigan Nono: Dole ne mata su rika la"akari da irin rigunan nono da suke amfani dasu, kada ki rika amfani da rigar nonon daya matsaki, haka kuma kada ki rika sanya wanda ya miki kadan, domin hakan yana jawo jijiyoyin dake rike da nonuwan su sake ko kuma su kasa rike nonuwan yadda zai yi kyau gani.


Motsa Jiki: Wasannin motsa jiki suna karawa mai yinsu lafiya, haka kuma yakan sa nonuwan mace su zama da kyaun gani, domin a kullum jini yana samun damar kewayawa a jikin macen datake yawan motsa jiki. Musamman ninkaye da wasu 'yan sarsarfa bana takura ba. Haka kuma idan kina iya maida hannayenki ta bayanki ki turo kirjinki gaba, kiyi haka a kullum kamar sau biyar, hakan yana karawa jijiyoyin nonuwanki karfi da kuma gewayawar jini anan, ta bakin wata mai aikin motsa jiki ga mata. Shi kansa tausa ga mace wani hanya ne dake karawa nonuwanta kyau.


Wanka. Yin wanka da ruwan zafi bashi da kyau ga macen dake fatan ganin ta tsufa da nonuwanta. Domin ruwan zafi yana rage karfin fatar mace wanda hakan na iya jawo nonuwanta su zube da sauri. Sai dai wanda da ruwan dubi shi yafi mai makon ruwan zafi.


Kwanciya: Babu kyau mace ta rika kwanciya a ruf da cikin yadda zata danne nonuwanta, hakan yana yiwa nonuwan mace illar da zai yi saurin zuba. Haka nan kuma yawan bayyana nonuwanki cikin rana shima yana jawo saurin zubansa, don haka mata su rika kaucewa yawan bayyana nonunwasu ciki zafi rana.


Ki zama mai yawan shan ruwa wannan shima zai taimaka miki so sai domin ganin kin tsufa da nonuwanki. Ga masu neman karin bayani suna iya tuntubata ta domin yi musu karin bayani.

Post a Comment

Previous Post Next Post