Yadda zaka samu fata me haske ba tare da kayi Bilicin ba.
Yawancin mutane musamman mata na sha’awar farar fata. Sau da yawa za ka tarar masu farar fatar ma na son kara wa fatarsu haske, kuma garin hakan,sai su sanya fatarsu cikin rudani wato abin da ake cewa a ‘garin gyaran gira a rasa ido’.
Akwai hanyoyi da yawa da ya kamata a bi wajen kara wa fata haske. Za a iya hakan ta hanyar amfani da nau’o’in mai na zamani da sauransu.
Zafin Rana kan kodar da fata kasancewar tana dauke da zafin ‘Ultra biolet rays’, a lokaci guda gumi da kura da kuma yawan shekaru na sa fata dafewa.Sinadarin melanin da ke jikin fata ne yake haifar da baki musamman ma idan ya yi yawa a jiki. sinadarin‘melanin’ na kare fata daga wahalhalu. Shi ya sa sauda yawa fararen mata sun fi yawan laulayi.
Dukan maya mayun da ke kara hasken fuska na dauke da sinadarin rage ‘melanin’ daga fata. Aloe bera da lemon tsami na rage bakin da ke jikin fata. Sannan banda su ga wasu hanyoyin da zaa samu farar fata
Yadda za ki yi amfani da ’ya’yan itace don rage bakin da ke jikin fata ayi haske ba me cutarwa ba
za Ki iya bare bawon lemu na zaki sai ki busar da shi wato ki shanya a rana . Idan yabushe, sai ki nika, sannan ki hada da nono (ko madara), daga nan sai ki kwaba,ki rika shafawa a jikinki da safe da yamma. Duk sadda kika shafa bayan lokac Sai ki wanke da ruwan dumi. Wannan zai kara wa fatarki haske.·
Wata hanyar kuma ta yin fari ZaKi iya neman itacen Sandal wood wanda ake turaren wuta da shi, sai ki hada da shi a hodar sandalwood din. Ki kwaba sosai, sannan sai ki rika shafawa sau biyu a rana; safe da yamma. Ki bar hadin ya bushe, bayan tsawon lokaci se ki wanke. domin hakan zai sanya fatarki ta yi haske.·
Wata hanyar yin hasken kuma shine amfani da Dankalin Turawa shima yana da sinadarin kara hasken fata. Za ki iya markada shi, sai ki rika shafawa kafin ki kwanta barci. Wannan hadin shi ma yana taimakawa wajen kara wa fatarki haske.
Post a Comment