Yadda Rake Take Karawa Mace Ni'ima (Amfanin Rake A Jikin Mace)


 Amfanin Rake Guda 15 Ga Lafiyar Dan-adam


Tun shekaru aru-aru da su ka shude, mutane ke amfani da rake don magance matsalolin lafiya daban-adaban. Al'ummun dake kasashe ma su zafi kuwa sun mai da shan rake a matsayin wani al'amari na al'ada. Duk da haka, mafi yawan mutane na shan rake ne saboda zakinsa kadai, ba tare da sanin amfanin raken ga lafiyarsu ba. A gaskiya, rake na da wasu sanadarai ma su taimaka wa kwarai da gaske wajen inganta lafiya.


Ba shakka rake na kunshe da ruwa mai yawa, hakanan rake ya yi fice wajen zaki mai sanyaya rai da kuma sanya nishadi, hakan ne ya sanya Hausawa ke danganta maganar wanda ke shan rake a matsayin santi.


Bugu da ƙari, rake na ƙunshe da sanadaran carbohydrates da amino acid, da kuma mahimman sanadaran, bitamin da su ka hada da Vitamin C, Vitamin B1, B2, B6, da calcium, phosphorus, iron, da succinic da fumaric, malic da citric organic aci.


Ganin cewa, a dai-adai wannan gaba, mai karatu ya fahimci irin muhimmman sanadarai da rake ke kunshe da su, yanzu haka za mu mayar da hankali ga amfanin rake ga lafiyar dan adam.


1. Bunkasa Garkuwar Jiki


Kasancewar rake tushen samar wa jiki sanadaran bitamin da kuma wasu sanadarai ma su gina jiki kamar nau'in sanadaran chlorophyll, protein, fiber, da sauransu, ya sanya rake ya zama mai taimakawa wajen bunkasa garkuwar jikin dan adam, hakan ya sa raken ke samarwa jiki rigakafin kamuwa daga wasu cututtuka da ka iya zama barazana ga lafiyarmu.


2. Inganta Lafiyar Haƙori


Kamar yadda mu ka ambata a sama, rake na kunshe da sandarai ma su yawan gaske da ke da tasiri wajen inganta lafiyar jikinmu. Daga cikin wadannan sanadarai har da ma su inganta lafiyar haƙori kuma su sanya hakoran kasance ma su karfi. Saboda haka ne ya ke da kyau ga duk mai son samun kakkarfan hakori mai cike da lafiya sai ya mayance wa shan rake.


3. Maganin Warin Baki


Binciken ya ci gaba da karin bayani cewa, baya ga sa karfin hakori da rake ke yi, hakanan dai raken na maganin warin baki. Saboda haka duk wanda ya zama al'adarsa ce shan rake akai-akai bakinsa zai kasance cikin tsafta da kuma daddadan numfashi. Zai yi wahala ka samu mai irin wannan al'ada da warin baki.


4. Riga-kafin Kamuwa Da Mura


Wani bincike ya nuna cewa, shan rake yau da kullum na taimakawa wajen hana kamuwa da mura, sanyi da kuma kaikayin makogwaro.


5. Rage Hadarin Kamuwa Da Cutar Daji


Mahimman sandaran Iron, magnesium, calcium da kuma potassium da rake ke kunshe da su ne ya sanya ya ke ragewa jikinmu hadarin kamuwa da ciwon daji. Wannan na daya daga cikin dalilin da ya sa a ke bai wa jama'a shawarar yawan shan rake don su amfana da wannan fa'ida ta sa.


6. Samar wa Jiki Karin Ruwa


Yawan shan rake musamman a lokacin zafi ya na kashe ƙishirwa sannan ya samarwa jiki ƙarin ruwa.


7. Gyaran Fata


Wani sanadari mai suna Alpha hydroxy aci (AHA) da ake samu a cikin rake na da kyau wajen gyaran fata. Saboda haka ne, masana a fannin kiwon lafiya ke bada shawarar yin amfani da rake wajen gyaran fata saboda yadda raken ke maganin tauyewar fata da kuma bushewar ta. Yin amfani da rake yau da kullum zai tabbatar da cewa fatar jikinka/ki ta kasance mai haske santsi da kuma laushi.


8. Inganta Lafiyar Koda


Kamar yadda masana su ka gano cewa, ruwan rake ya na da kyau wajen samar wa jiki karin ruwa, hakan kuma sai ya sa rake ya kasance mai amfani wajen inganta lafiyar koda, ta wajen hana cutar nan ta duwatsun koda, wato "Kidney Stone". Wani binciken masana kimiyya ya tabbatar da cewa rashin shan isasshen ruwa shike haifarda cutar ta duwatsun koda. Saboda haka yawan shan rake tsawon wani lokaci mai tsawo zai iya hana kamuwa daga wannan cutar ko kuma ya haifar da warkewa daga cutar ga wanda tuni ya kamu da ita.


9. Rage Amai Ga Mata Masu Juna Biyu.


Shan ruwan rake na iya taimaka wa mata masu ciki samun saukin amai. Mata masu ciki da ke shan wahala saboda yawan amai zasu iya shan rake don samun saukin wannan matsala. Yadda za su yi kuwa shine, a matse ruwan raken sai a zuba garin cittta cikinsa ta sha sau daya tak a rana.


10. Maganin Kumburi Ga Mata Masu Ciki


Matan da ke fuskantar matsalar kumburi za su iya amfani da rake don samun saukin kumburin, matukar za su sha ruwan raken da aka matse sannan aka tace shi. Idan kina fama da wannan matsala za ki sha ruwan raken da yawa a rana.


11. Inganta Lafiyar Zuciya


Haka dai daga cikin amfanin rake ga lafiyar dan adam, akwai inganta lafiyar zuciya kuma ya na hana kamuwa daga cututtukan zuciya da kuma bugawar zuciya saboda yadda raken ke rage adadin sanadaran 'cholesterol' da 'triglycerides' a cikin jikinmu.


12. Hana Cushewar Ciki

Saboda yadda rake ke kunshe da sandaran potassium mai yawa a cikinsa, ya sa yake taimakawa wajen saurin narkewar abincin da muka ci. Masanan su ka ce, ba wai kawai rake na taimakawa wajen narkewar abinci ba ne kadai, amma kuma zai iya hana ciwon ciki da kuma cushewarsa.


Hakanan, daga cikin amfanin rake ga lafiyar dan adam, har da;


13. Yawan shan rake na kara inganta lafiyar kwakwalwa.


14. Shan rake na kara inganta lafiyar ido da kara karfin gani.


15. Rake na daidaita adadin sugan dake cikin jini.


SHARE & LIKE

Post a Comment

Previous Post Next Post