Yadda Ake Koran TSaka Da Kyenkeso Da Kuma Jaba A Gida
Duba da hatsurran dake tattare da wadannan halittun guda Uku, sai muka ga ya dace mu zo da bayanin tiryan tiryan kan yanda ake korar tsaka da kenkeso da kuma hana ga baki daya a cikin gida.
Ta'ammali da tsaka a cikin gida masifa ce,mun yi rubutu kan dimbin illolin da take haifarwa a gida,ko baya ga haka halitta ce munafuka da addinin musulunci yaiyi umurnin idan an ganta a kashe ta.Akoi lada ga Wanda ya aikata haka.
Shi kuma kenkeso yana dauko kwayoyin cuta daga najasa a toilet ya zo ya cudanyasu ga abinci,ruwan sha,ko abin shan da aka ajiye.
Halitta ce da take da tsawon rayuwa zata iya daukar shekara da shekarru tana rayuwa a bayi,tana haddasa cutukan polio,cholera, typhoid,da matsanancin basir,da gudawa marar misali.
Duk abinci ko wani abin shan da ta fada a cikinsa to ka zubda wannan abin kada ka kuskura ka ci ko ka sha,wallahi hatsari ne ga lafiya matuka.
Sabuwar Hanyar Da Zaki Karawa Kanki Ni'ima
Danna Nan Domin Cigaba Da Karantawa
Domin korar tsaka a gida,ka nemi gishiri ka gauraya da garin tafarnuwa sai ka marmasa a kowace korkoda a gidanka,tsaka zata bar wajen a cikin gaugawa.
Shi kuma kenkeso,ka nemi albasa guda daya,da cokali daya na baking soda (sodium biocarbonate) bafa baking powder ba,sai a kula.
Sai ka yayyanka albasa ka gauraya da bakin soda din ka ajiye a korkodar kitchen ko a toilet, zaka ga yanda kenkesai zasu mutu.
Post a Comment