Yadda Ake Hadin Zuma Wanda Zai Gyaraki Sai Kinfi Amarya Ko Sabuwar Budurwa

Yadda Ake Hadin Zuma Wanda Zai Gyaraki Sai Kinfi Amarya Ko Sabuwar Budurwa





Ataimaka da Sharing Dan Allah Domin Karuwar Al'umma.

Zuma :Takunshi abinci mai gina jiki, dakuma Vitamin Kala daban daban daban wannan sinadarai Sun hada da :

1.VITAMIN(A)wanda yake shi yana daga cikin sinadari wanda yake karama dan adam gani, wanda yake rashin samun sa ajiki, zai iya sawa asami matsalar larurar I danu, musamman rashin ganin da daddare, dakuma bushewar fatar jiki,kaga yaro ko babba yaki girma, kuma barashin ci, babu rashin sha, sai dan rashin Vitamin (A). 

2.VITAMIN(B)(complex) wanda yake shikuma rashin samun sa ajiki hakan zai iya sanya wa akamu da cutar rashin hankali, da rashin cin abinci, dakuma daurewar ciki. 

3.VITAMIN (B2)(Riboflavin) shima wanda yake rashin samun sa ajiki, yana kawo tsufa da wuri, da kuma larurar idanuwa. 

4.Vitamin(B3)(Pantothenic acid) wanda yake shikuma samuwar ajiki yana karama dan adam karfin hankali, dakuma basira, rashin sa kuma yana iya sawa akamu da cutan hauka, ko cutan kuraje. 

5.Vitamin(B5)(Niacin omictinic acid) Rashin samun sa ajiki yana iya haddasa cutan fata, ko gudawa, kikaga mutum hankalin sa sama sama, da rashin narkewar abinci, da rashin basira. 

6.vitamin(B5)(Pyridoxine) Rashin samun sa ajiki zai iya haddasa ma mutum yawan jin tsoro, dakuma rashin karfin gabobi sosai, ko kamuwa da cutan hauka, ko cutan asthma, da makamantan su. 

7.Vitamin (B12)(cyanocobolamine) da(Folic acid) Rashin wadannan sinadaran ajiki yana iya haddasa animiya, da rashin jini, wanda yin tsanani hakan zai iya sanya wa akamu da cutar shan Inna ko cutan Farfadiya. 

8.Vitamin(E)wanda yake shikuma wannan ana samunsa sane acikin zuma fatar saka, wanda yake rashin samun sa ajiki yana rage karfin namiji,kasala,dakuma cutar tautau, kyasfi dadai sauran su. 

9.Vitamin(C)wanda yake shikuma rashin samun sa ajiki yana iya haddasa cutan sanyi, irin su asthma, zazzabi, mura da sauransu. 

10.Vitamin(K)shikuma samunsa ajiki yana rage ma mata yawaitar zubar da jini alokacin alada,dadai sauransu. Wannan bincike ne nawasu likitocin muslunci, cewa dukkan wadannan sinadaran zaa iya samun su acikin zuma, don haka wanda yasami mai kya kuma yarika amfani daita, zai rika samun wadannan faidodi masu yawa, domin Allah (swt) Yace zuma akwa waraka acikin ta zuwa ga alumma. 

Allah Madaukakin Sarki ya tara magunguna masu yawan gaske a cikin zuma, duk maganin da mutum yake buqata yana nan a cikin zuma. Ita Qudar zuma tana samun abincinta ne daga furannin itatuwa daban-daban, kuma dukkan magunguna ana hada sune da itatuwa.

Allah Ya ba ta basirar zuwa nisan kiwo domin neman abincinta, wanda take zuqowa daga jikin itatuwa da dama wainda suke haduwa su zama magani domin amfanin dan Adam. 

Bayan ta fita zuwa nisan kiwo sai Allah Allah Ya nufe ta da dawowa gidanta ba tare da tabaceba, Allah Madaukakin Sarki yace:Abin sha yakan fita daga cikinsu da launoni daban-daban, akwai magunguna a cikinta (zuma)..

1-Takan maye sukarin da mutum ya rasa a jiki sabo da aikin wahala.

2)Magani ce mai qarfi, wadda take kashe qwayoyin cuta a cikin abinci.

3)Tana maganin 6acin ciki,da zawo, da gyambon ciki.

4)Tana maganin cutar hanta, da taimaka wa matsarmama wajen aiki.

5)Tana maganin cutar zuciya, tana qarfafa tatar zuciyan.

6)Tana maganin cutar da take haifar da qarancin jini, tana qarfafa qwayoyin jinin.

7)Tana maganin cutar qarancin barci, takan taimaka wajen saurin barci.

8)Tana maganin ciwon kai.

9)Tana maganin cutar ga6u66a.

10)Tana maganin raunin namiji da mace, takan taimaka wurin saurin samun juna biyu.

11)Takan taimaka wurin karfin qashin Yaro, da fitowar haqori.

12)Tana maganin tari, da gyara maqogwaro.

13)Tana maganin wahalar daukan ciki, da radadin jinin al'ada, takan taimaka wa masu ciki wurin haihuwa, ta hana tsukewar mahaifa wurin haihuwa, ta qara yawan nono.

14)Tana hana cancer nono, ana aiki da ita wurin maganin cancer.

15)Ana aiki da ita wurin maganin cututtukan ido.

16)Tana maganin cututtukan fata, kamar borin jini, qyasfi, qanzuwa, marurai da sauransu, a kan yi aiki da ita ga wanda ya qone.

17)Tana maganin cututtukan huhu, ko sanyi da sauransu.

18)Tana qara wa fatar mata qyalqyali, tana hana saurin tattara.

19)Tana hana tattaruwar majina a huhu, masamman ga masu shan taba.

20)Tana maganin cutar qoda, da saifa, da maraina, takan yi maganin tsakuwan qoda.

21)Takan yi maganin cutar harshe, da ru6an haqori, da tsagewan la66a.

22)Takan taimaka ga masu cutar suga.

23)Tana maganin kumburin ciki da qullewarsa da cutar basir.

24)Takan taimaka wurin maganin fitsarin kwance.

AMFANIN ZUMA GA

LAFIYA ( A TAKAICE ) Zuma (honey) wani irin abincine mai zaki kamar shigen suga wanda kudan-zuma ke samarwa daga furen itace ko

shuka -wato wani romon sinadari dake cikin furen itace ko shuka da kudan-zuma ke

tsotsowa (nectar) domin sarrafa ruwan zuma.


Mutane na amfani da zuma a matsayin abinci ko magani.


Sabili da muhimmancin zuma, a cikin surorin Alqur'ani maigirma akwai surah mai sunan kudan zuma - wato Surat An- Nahl. Allah (S.W.T.) ya bayyana mana muhimmancin zuma ga rayuwar 'dan adam a cikin wannan surah " ...waraka ce ga mutane." (An Nahl: 69).


Hakika kuma Manzon Allah (S.A.W.) ya bayyana mana muhimmancin ta a wasu hadisai. Don haka, zuma nada amfani ga lafiya kamar haka:


1. Tana kashe cutar bakteriya da fangas (bacteria & fungus) da kuma bada kariya daga

kamuwa da ciwon-daji. Bincike ya nuna cewa zuma mai duhu-duhu tafi wannan amfanin.


2. Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa ko sha. 


3. Tana taimaka ma mai-mura, tari , atishawa da sauran matsalolin sanyi.


4. Maganin gudawa ce.

5. Maganin gyambon ciki - Ulcer. 

6. Tana karfafa garkuwar jiki.

7. Tana rage hadarin kamuwa daga cututtukan zuciya, musamman idan aka hadata da Kirfat (cinnamon).


8. Tana sanya kuzari a jiki. 

9. Tana rage nauyin kiba. Shan ruwa mai-`dumi da lemun tsami tare da zuma kafin aci komi da safe zai taimaka wajen rage `kiba.


10. Tana saukaka narkewar abinci ga masu fama da rashin narkewar abinci.


11. Tana rage kumburi mai sanya waje yayi kalar ja da radadin ciwo (inflammation).


12. Tana inganta lafiyar kwalwa.

13. Tana gyara fata da rage kurajen fuska (pimples) idan ana shafawa.


AMFANIN ZUMA A RAYUWA

1. Zuma na kare mutane daga kamuwa da cutar siga wato Diabetes da turanci sannan kuma yana hana tashin cutar wa mutanen da ke fama da shi. 


2. Zuma na maganin mura, kawar da matsalolin da ke kama ido kamar jan ido, kaikayin ido,kumburin ido da sauransu. 


3. Zuma na kuma warkar da rauni ko kuma kuna a jikin mutum. 


4. Zuma na rage yawn mantuwa musamman matan da suka daina haihuwa. 


5. Yana kuma maganin cutar Ulcer. 

6. Zuma na warkar da cutar dake kama hakarkari wato Pneumonia da turanci. 


7. Zuma na taimaka wa mutanen(maza ko mata) dake fama da matsalar rashin haihuwa.


8. Zuma na kuma maganin ciwon ciki. 

9. Zuma na gyara fatar mutum. 

10. Zuma na warkar da tari.


BAYANI AKAN SIRRIN ZUMA


 haƙiƙa ita zuma tana daga cikin manya-manya abubuwan da ake magani da su kuma itama kanta magani ce domin ya zo a cikin alƙur'an mai girma.


  *Inda Allah (S.W.T) yake cewa:*


Yana futowa daga cikinta (ita zuma) wani abun sha Wanda yake mai launuka daban-daban hakika a cikinsa akwai waraka ga mutane.


Yana daga cikin kalar zuma


FARAR SAƘA DA BAKAR SAKA


Da sauransu Kuma ko wacce tana da magani ta Haka nan yazo a cikin hadisi Manzon Allah (S A W) yana cewa : na hore Ku da ababan waraka guda biyu (2) *ZUMA DA ALKUR'ANI*

(ibn majah da Hakim suka ruwaito )


Bayan haka an ruwaito cewa: wani mutum yazo wajan Manzon Allah (S.A.W) ya ce : yaa Manzon Allah nazo ne in gaya maka cewa dan uwana yana fama da ciwon ciki, sai Manzon Allah ya ce jeka ka shayar da shi zuma, sai ya Tafi ya shayar da shi zuma amma bai warke ba, sai ya koma wajen Manzon Allah (S.A.W) ya sake cewa jeka ka shayar da shi zuma, sai ya je ya shayar da shi, amma bai warke ba, sai ya komo wajen Manzon Allah sai Manzon Allah yace da shi hakika Allah yayi gaskiya cikin dan uwanka yayi karya, jeka ka sake shayardashi zuma, da yaje ya sake shayar dashi zuma sai ya warke.


Wannan hadisi yazo cikin bukhari da Muslim


Hakanan wannan yana daga cikin abun da ya kamata mu fa'idantu da shi cewa shi magani ba'a yi masa gaggawa, Ana so adinga mai-maitawa da haka har ubangiji ya kawo saukin cutar.


Hakanan yana daga cikin sirrin zuma zaka ga yawan cin magani Ana cewa hada shi da zuma farar saka.


YARO

yana daga sirrin zuma in an haifi yaro ya Kai kamar wata hudu (4) kullum a dinga diga masa a baki sau uku (3) a Rana saboda ta Kara masa wayo da basira da kaifin hadda in ya girma.


Sannan tana sa kashinsa ya Kara kwari.


MAI JEGO

yana daga sirrin zuma mace mai jego ta dinga shan zuma a kullum itama sau uku (3) a Rana , kafin ta haihu da bayan ta haihu saboda samun cikakkiyar lafiya da ita da yaronta.

            

CIWON CIKI

 yana daga sirrin zuma idan mutum yana fama da yawan ciwon ciki mai daurewa, ya dinga karanta ayatul-kursiyyu kada (7) a cikin zuma yana sha a kullum in sha Allah zai rabu da shi.


YAWAN KUKAN YARO

 yana daga sirrin zuma idan yaro yana yawan kukan banza na babu gaira babu dalili ko yawan kuka idan ya farka daga bacci sai a samu zuma mai kyau marar hadi a tofa BISMILLAH (9) a dinga bashi ya lasa insha Allah 


NUTSUWA KO HUTU

yana daga sirrin zuma idan mutum yana so yasa mi natsuwa da Hutu da nishadi kyakkyawa a cikin kokon zuciyarsa ya dinga shan zuma tare da man habbatussauda da safe da kuma kafin yaya kwanta bacci.


MACE MAI HAILA

yana daga ainihin gudarin sirrin tatacciyar zuma ga mace mai haila da ta samu ta dinga samun ruwan zafi kofi daya (1) ta zuba zuma a ciki ta dinga sha zata ji banbanci.


TASHIN ZUCIYA

idan mutum zuciyarsa tana tashi da zarar yaji zata tashi, sai ya dibi zuma cikin cokali daya ya sha insha Allah .


CIWON HANTA

yana daga sirrin zuma dan magance ciwon hanta, shi ciwon hanta yana da alamomi yawan kasala ko da yaushe yawan jin bacci da yawan amai da kuma yawan jin ciwo a kirji, sai a samu zuma da lemon tsami da man zaitun a hada guri daya a dinga diba Ana sha sau uku(3) a Rana insha Allah


HAIHUWA CIKI SAUKI

hakanan yana daga sirrin zuma a haihu cikin sauki , in Ana nakuda asha zuma kamar cokali goma sha biyu (12)


WARIN BAKI

yana daga sirrin zuma dan Hana warin baki kullum mutum yasha da safe bakinsa zai daina wari.


 FITSARIN KWANCE

yana daga sirrin zuma fitsarin yara na kwance, sai kullum a dinga basu zuma sau biyu (2) a rana zasu daina insha Allah.


CIWO

Haka nan yana daga sirrin zuma dan magance ciwon da ya Dade bai warke ba sai a dinga shan zuma Ana kuma shafawa a wajan ciwon.


NAUYI ABINCI

yana daga sirrin zuma tasa abinci mai nauyi ya narke da wuri idan ansha ta bayan cin abinci.


 HADUWAR KASHI

yana daga sirrin zuma in kashi ya tsage ko ya karye bayan an gyara sai a shafa ta a wajan kuma a na sha.


 CUTUKAN ZUCIYA

 yana daga sirrin zuma magance cutukan zuciya za'a samu lafiyayyen nono a hada da zuma da kar nafal Ana sha safe da yamma.


GYARA MURYA

yana daga sirrin zuma In ana cinta da yara citta a ko da yaushe.


 YAWAN TARI

 yana daga sirrin zuma mutum yana yawan tari sai ya samu zuma mai kyau da lemon tsami da yar'citta da dan ruwan zafi Ana sha insha Allah


HAIHUWA

 Allah shine mai bada haihuwa koda duk za'a baki magani duniya 


Amma kina iya gwadawa insha Allah


yana daga sirrin zuma ainihin kututun gundarin amfanin zuma ga mace bakarara sai a samu ainihin gudarin tuwan zuma a hadashi da madara Ana sha kullum har tsawon wata (2) babu fashi insha Allah


CUTAR FARFADIYA

Haka nan ma zuma na magance cutar farfadiya, idan aka samu zuma mai kyau marar hadin,cikin cokali (6) da safe sannan adinga shafa man zaitun da man habbatussauda a duk daukacin jiki.


Sannan a dinga karanta masa ayatul-kursiyyu a ruwan zamzam kafa (7) Ana bashi yana sha sannan ragowar a shafe masa jikinsa gaba daya, a yi ta yin haka ba fashi sai anyi kamar wata (1) insha Allah


ASMA

yana daga sirrin zuma tana magance cutar ASMA in Ana Shanta ajere-ajere har tsawon wata guda.


GYAMBON CIKI DANA HANJI

haka kuma zuma na magance gyambon ciki Dana hanji sai a samu zuma mai kyau marar hadi a hada da hulba da ruwa zafi tafasasshe a dinga sha bayan ya huce kafin cin abinci Allah zai bada lafiya.


Wannan yasa masana ilimi magunguna suka bayyana fa'idojin ta marasa iyaka.


Inda mutum ya lasheta kafin yaci komai tana 

➜ gusar da 


➜ majina

➜ wanke ciki

➜ gyara dattinsa da gusar dashi


Wato yana futowa cikinta (itaZUMA wani abin sha Wanda yake mai launuka daban-daban hakika a cikinsa mutane.


Post a Comment

Previous Post Next Post