Yadda Ake Amfani Da Tafarnuwa Domin Maganin Infection, Karin Ni'ima Da sauransu

 

 AMFANIN TAFARNUWA GA DAN ADAM 

Tafarnuwa da Manta na da matukar na gaske da ba kowa ne yasan da haka ba, suna samar da waraka tare da magance wasu cututtuka da dama na mata da maza.

Ga Kadan daga Amfanin Tafarnuwa da Manta Ga Mata

1) SHAYAR KARAMI::

Idan mai shayarwa tana so nononta ya wadaci jaririnta kuma kada ciwo ya kama nonon nata sai ta ci dabino bakwai sannan ta sha man tafarnuwa cokali daya.

2) CIWON CIKI & KULLEWAR MARA:

Bayan haihuwa, sai a sami ruwa mai dumi kofi daya a zuba man cikin cokalin shayi daya sai ta sha

ta yi haka kwana uku

3) HAILA,FITSARI,JININ BIKI:

Wanda ke yin ba haya da kyar ko fitsari da kyar ko wajen fitar jinin haila sai an sha wuya ko jinin biki, sai ta rika shan karamanin cokali daya da safe daya da rana daya da dare, zata warke sai dai budurwar da take da budurcinta Idan ta fiya yawan yin amfani da man tafarnuwa zata rasa budurcinta.

Amfanin Kwai A Jikin Dan Adam Yadda Yake Gyara Kwakwalwar Yaro Ya Karo Hazaka 

4) MUHIMMIYAR FA’IDA:

Idan mace tana bukatar maniyyinta ya yawaita sai ta sami madarar saniya kofi daya ta zuba man ta sha kofi daya da safe, kofi daya da dare, matar da tayi haka zata bai wa mijinta sha’awa da mamaki matuka.

Amfanin Man Tafarnuwa Ga Maza


1) KAIKAYIN MARAINA KO AZZAKARI:

Idan namiji yana jin kaikayi a jikin marainansa ko azzakarinsa to, sai ya sami garin farar kanwa cikin babban cokali daya, ya dafa da ruwa kofi biyu, idan ya tafasa sai ya zuba man tafarnuwa babban cokali biyu ya gauraya sannan ya sauke, idan ya huce sai ya wanke gabansa gaba daya da ruwan zai sami sauki.

2 ) WANDA BAYA IYA SADUWA DA IYALI:

Wanda baya iya saduwa da iyali fiye da sau daya ko kuma da ya soma sai ya ji ya gaji, to sai ya sami dabino mai kyau guda ya dafa da ruwa mai kyau, idan ya tafasa sai ya tace da farko zai dafa da ruwa kamar kofi hudu 4 bayan ya tace sai ya debi kofi uku ya sake tafasawa yana cikin tafasa sai ya zuba man tafarnuwa babban cokali biyu 2 sai ya barshi akan wutar ta yadda ruwan zai dawo kamar kofi biyu 2 idan ruwan ya huce sai ya rika sha babban cokai biyu sau hudu a rana, ya yi kwana 7 yana yin haka…

3) GAME DA GWAIWA KO TINJERE KO KANJAMAU KO FITAR WANI RUWA DAGA AZZAKARI .

Wannan ruwa akan ganshi da yauki-yauki kuma rawaya-rawaya, wannan ruwa ba ciwon sanyi bane, alamu ne da suke nuna cewa gwaiwa na tafe.

Maganin wadannan abubuwa shi ne a sami zuma mai kyau tatacciya kofi uku (3) a sami man shanu kofi (2) a sami man tafarnuwa cikin babban cokali hudu a hada su guri daya a dafa, su cakuda sannan a sauke, idan sun huce sai a rika sha cikin babban cokali biyu (2) sau hudu a rana.

5) MAGANI SANYI:

Game da kare kai daga kamuwa da sanyi ba zai kama mutum ba ta kowace hanya, idan ma ya kama to za a rabu yadda za a yi shine, farko idan kai mai yawan shan shayi ne, duk sanda zaka sha shanyin sai ka diga man tafarnuwa a ciki, ko kuma ka sami ruwan zafi a kofi ka diga masa man tafarnuwar ka sha, ka rinka yin haka akai-akai kuma duk sanda zaka yi wanka ka diga man tafarnuwar a cikin ruwa mai dumi ko mai sanyi




Post a Comment

Previous Post Next Post