Sabon Hadin Tumfafiya Domin Magungunan Mata Daban-daban

Sabon Hadin Tumfafiya Domin Magungunan Mata Daban-daban 



Tunfafiya abace wacce kusan kowa yasanta, sannan yawancin mutane akan gaya musu cewa ba'a son zuwa wurin da take saboda tanada aljanu amma, kuma duk da hakan tanada matukar amfani ga lafiyar jikin dan Adam.

Tunfafiya kan fito a wurare daban daban, amma mafiya yawanci anfi samunta a daji kokuma wani kango daya dade mutane basa zuwa. Haka zalika mutanen da can sunfi amfani da Tunfafiya wajen maganin cututtuka a jikiinsu saboda sun fimu sanin mahimmancinta.

                 MAGANIN CIWON HAKORI

Sai a nemi ganyen tunfafiya mai kyau da fatar lemon tsami sai a tafasashi sosai ya tafasu a zuba dan gishiri sai a dinga kuskure baki dashi,

Zuwa kwana uku.

               MATSALAR KURUMTAKA

Za'a samu rawaya wato yellow na ganyen tunfafiya sai a markadashi sosai, a tafasashi sosai a barshi yayi sanyi sai a tace shi sai dinga wanke kunne dashu tsawon Sati biyu ko uku zaa samu lafiya da yardar Allah.

                       BASIR MAI TSIRO

Zaku samu ganyen tunfafiya kushafa man shafawa a jiki saiku karashi a wuta yadanyi zafi saiku dinga dannawa a dubura inda ciwon ya fito, zuwa kwana bakwai. 

                                MAKERO

Ana diga ruwan tunfafiya wanda idan anciro ganyenta za’aga yana fitar da wani farin ruwa. Za’a samu mai ciwon makeron sai a kankare yadan fara jini sai a diga wannan farin ruwan a kai, za’a dinga yin haka duk bayan kwana biyu ko uku har a samu lafiya.

                 MATSALAR ALJANU

Zaa samu ganyen tunfafiya da garin Habbatus-sauda sai shanya ganyen tunfafiyar idan ya bushe, sai a hada da garin Habbatus-sauda dinga yin turare dashi safe da yamma zuwa kwana tara.

                           KARIN BAYANI

Muna bada magungunan inganta lafiyar maza da mata harda yara kanana.

Muna cikin jahar kaduna malali low cost kaduna Norht Local government Area kaduna State Nigeria Kuma muna aikawa kowannne gari afadin duniya ga duk Wanda yasayi maganin.

Post a Comment

Previous Post Next Post