Hadin Kanun Fari Da Madara Maganin Karin Ni'ima Da Kuma Infection Cikin Sauki

 Hadin Kanun Fari Da Madara Maganin Karin Ni'ima Da Kuma Infection Cikin Sauki 





IDAN KA KARANTA KA TURAWA SAURAN YAN UWA DOMIN SU ANFANA:

Da yawa mutane suna neman magani ne,amma sai su tsallake asalin magani su tafi neman wani abu daba bisa rashin sani.

A yau insha Allahu zan sanar daku 2 daga cikin amfanin shan Garin kaninfari da madara ta ruwa ko nono

1. Yana magance matsalar saurin kawowa.

Matsalar saurin kawowa matsala ce da take damun mafi yawan magidan ta a wannan lokaci musamman ma wadan da basu da manyan shekaru,wanda hakan a tare dasu babbar illa ce da kuma barazana a zamantakewar su da abokan zaman su.

2. Matsalar  infection.

Infection wanda aka fi kira da sanyin mara,shima yana daga cikin ciwokan dake dakun jama'a mata da maza yan mata da zawarawa kai harda matasa.

Shin ta wacce hanya zaa iya magance wadannan matsaloli da kaninfarin???


ZAA NEMI.

1. Garin kaninfari.

2. Madara ta ruwa/nono

Zaa samu garin kaninfari rabin karamin chokali a zuba a ciki karamin kofi na madara ta ruwa ko nono a juya sosai sannan a sha,ana sha ne sau daya a rana na tsawon kwana 3 kacal 



Abubuwan da ya kamata a yi don rage kaushin fata:


Akwai abubuwa da dama da suka kamata a yi domin rage kaushin kafa ko rabuwa da shi baki daya. Kaushin kafa yana yawan fito wa mutum ne a lokacin sanyi sakamakon abubuwa kamar; yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi. Akwai nau’o’in mai da dama da ake sayar das u domin magance matsalolin kaushin fata amma yawancinsu suna da tsada. Domin bin hanya mafi sauki wajen magance wadannan matsaloli na fata sai ku karanta abubuwan da na lissafo muku.


A rika diga man zaitun a cikin man shafawa. Yin hakan na sanya fata laushi kuma yana rage kaushin fata.


Lemun tsami da sukari suna taimakawa wajen fitar da fatar da ke da gautsi a jiki sannan suna sanya fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti uku sannan a wanke.


Za a iya kwaba fiya sannan a shafa a jiki a bari na tsawon minti 15 sannan a wanke kafin a shiga wanka a kullum. Ko kuma a hada jus din fiya a rika sha domin magance kaushin fatar daga jiki.


A rika amfani da man kwakwa a fatar jiki. A dora man kwakwa a wuta ya dan yi dumi sannan a shafer fatar jiki kaf da shi na tsawon minti 30 kafin a shiga wanka a kwanta. A rika yin haka kullum.


Shan madara kofi daya kafin a kwanta barci a kullum na taimaka wa fata sosai.


A rika shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka da dare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gaba daya da man kadanya domin samun fata mai laushi mai sheki.


A samu ayaba da nono ko kindirmo a kwaba a waje daya sai a shafa a fuska ko fata na tsawon minti 20 sannan a wanke da ruwan dumi.

A yi amfani da daya daga cikin abubuwan da na lissafo. Kada a hada duka a jiki, amfani da abubuwa da yawa a fata yana haifar da kuraje a fata.


A shafa zuma a fatar jiki baki daya sannan a bar ta na tsawon minti biyar zuwa 10 kafin a shiga wanka a kullum.


Post a Comment

Previous Post Next Post