Hadin Ganyen Lemun Tsami Gwaiba Da Kuma Citta
Da farko dan Allah ayi hankuri idan mun yi post a tsaya cikin natsuwa a karanta a fahimta,idan ba a ganeba sai ayi tambaya amma ba dalili bane sai mun yi post wasu ke ta damunmu da kiran woya a dole su basa iya karanta dogon rubutu sai a yi masu bayani ta baki, wallahi ba zamu iya ba.
A nemi ganyen lemun tsami da ganyen goiba sai a wanke da kyau a jefa citta kwara daya,sai a tafasa da kyau,har sai sun tafasu.
Za a tsaye a tace a sha rabin cup.
Maganin ciwon ga6o6in jiki,
ciwon kafafuwa,
ciwon gadon baya,
ciwon kafadu da ciwon jiyojin jiki.
Maganin zazza6i waton fever ,a sha ruwan a yi suraci da ganyen.
Mai fama da tsohuwar shawara a jiki komai dadewarta,a sha rabin cup kullum da safe bayan an ci abinci,har sati biyu.
Maganin Typhoid a sha ruwan a yi wanka da sauran da duminsu,safe da yamma.
Mai fama da ciwon kasusuwan jiki.
Mai fama da matsanancin tarin da aka rasa gane ko wane iri ne.A sha safe da yamma.
Mai fama da tsutsar ciki shi ma zai tafasa ya rinka shan rabin cup da safe kamin a karya.
yawan kamuwa da malaria a tafasa a sha sau biyu ko uku amma kada a sha maganin asibiti a lokacinda ake shan wannan maganin.
Fitsarin jini sai a tafasa ganyen lemun dana goiba da jar kanwa kada a tafasa da citta.Za a sha a sanda za a konta bacci.
Cutukan daji,a tafasa a zanka sha kadan kadan a duk sanda ake bukata a kalla dai sau uku ga sati.
Mai fama da tarin asma ya jarraba wannan maganin.
Da fatar za a shere bamu yafe hakkenmu na ayi editing ba Wanda yaiyi hakan shi da Allah.
Post a Comment