Cikakken Bayanin Yadda Zaki Dadi Da Mijinki Cikin Jindadi

 Abunda Yasa Kake Daukan Lokaci Bayan Kayi Zuwan Kai 




Cikakken Bayanin Yadda Zaki Dadi Da Mijinki Cikin Jindadi 

Maza da yawa suna son sake ci gaba da saduwa da matansu bayan sunyi zuwan Kai na farko. Amma hakan yana citura sai zuwa bayan wasu mintuna wasu kuma sai ma an kai sama da awa 24.

Akwai mazan da suna iya yin zuwan kai har sau biyar ba tare da sun sauka daga kan matansu ba. Irin wadannan maza bincike ya nuna Kashi 30 ne cikin 100 na maza dake da irin wannan halittar.

Kamar yadda aka samu irin wadannan kason cikin maza, haka ma ake dasu cikin mata, akwai macen da idan ta gamsu sau daya bata bukatar namiji sai bayan wani lokacin. Akwai wata sai ta kawo sama da biyar sannan take sanin tayi Jima'i.

Dukkanin masu irin wadannan halittar babu wani matsala dake damun su. Illa kawai haka halittarsu na Jima'i yake. Yayin da kuma suka nemi takurawa kansu yin fiye da abunda halittarsu bazai iya dauka ba, suna iya cutar da kansu.

Bisa al'ada irin yadda halittar mazakuta yake bayan yayi zuwan Kai. Mutum yana bukatar akalla mintuna 10 zuwa 20 domin baiwa azzakari hutu da kuma damar sake maido da sinadarin dake maido da kuzarin namiji.

Sai dai ga sabbin ma'uarata maza wasu lokutan suna iya daukar lokaci mai tsawo kamin Azzakarin nasu ya sake samun karfi. Hakan yana faruwa ne saboda rashin sabo da yi. Amma da zaran sun saba lokacin zai rika raguwa akai akai.

Ga wadanda suka saba Kuma suke jimawa kamin ta sake mikewa bayan zuwan Kai. Wannan yana iya yiwuwa sun samu raunin gaba ne wanda suna iya tuntubar likita domin neman taimako

Mazan da suke daukan lokaci bayan zuwan kai hakan ba yana nufin cewa basu da lafiya bane ko kuma masu yin ta zarce sun fisu karfin jini bane. Abun a halitta yake ba a lafiya yake ba.

Idan Kana Son Yin Tazarce:

Akwai dabaru ga duk mazan da suke bukatar yin tazarce bayan zuwan Kai na farko, to su tabbatar hakan zai iya masu Wahala ba tare da taimakon kwayoyin kara karfin kuzari ba. Amma akwai hanya mafi sauki wanda cikin karamin lokaci gabansu na iya sake mikewa su ci gaba da Jima'i.

Sai dai kamin maigida yayi tunanin sake komawa ga iyalinsa karo na biyu ya tabbatar dacewa tana da bukatar hakan, wannan ne zai bashi damar yin Shirin koma mata.

Hanya na farko da namiji zai iya ci gaba da Jima'i da matarsa bayan zuwan Kai shine kada ya rabuda matarsa bayan yayi zuwan Kai. Ya bar azzakarinsa cikin farjinta zuwa dan lokaci kadan idan tasan hikimar da Mata suke yi idan azzakari na cikin su zata sake motsa maigida.

Hanya na biyu shine ci gaba da wasanni da juna. Bayan zuwan kai idan ma'aurata na Sha'awar Kari zasu iya ci gaba da tsotsai tsotsai da tabe taben juna. Hakan zai sa cikin karamin lokaci namiji yaji kuazarinsa ya dawo.

Yana na uku shine tsari da ruwan dumi. Bayan zuwan kai idan namiji zai wanke gabansa da ruwan dumi kuma ya wanke kasan mararsa da ruwan dumi kamin ya fito daga ban daki zai ji gabansa ya amsa.

Wadannan hanyoyi sune hanyoyi mafi sauki domin dawowa da karfin sha'awar ka domin saduwa da iyali.

Kada a sabawa jiki da shaye shayen kwayoyi. Kada kuma ace za ayi fiye da abunda jiki zai iya dauka.


Post a Comment

Previous Post Next Post