Abubuwan Da Ya Yamata A yi Don Rage Kaushin Fata

 Abubuwan Da Ya Yamata A yi Don Rage Kaushin Fata





Akwai abubuwa da dama da suka kamata a yi domin rage kaushin kafa ko rabuwa da shi baki daya. Kaushin kafa yana yawan fito wa mutum ne a lokacin sanyi sakamakon abubuwa kamar; yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi. Akwai nau’o’in mai da dama da ake sayar das u domin magance matsalolin kaushin fata amma yawancinsu suna da tsada. Domin bin hanya mafi sauki wajen magance wadannan matsaloli na fata sai ku karanta abubuwan da na lissafo muku.

A rika diga man zaitun a cikin man shafawa. Yin hakan na sanya fata laushi kuma yana rage kaushin fata.

Lemun tsami da sukari suna taimakawa wajen fitar da fatar da ke da gautsi a jiki sannan suna sanya fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti uku sannan a wanke.

Za a iya kwaba fiya sannan a shafa a jiki a bari na tsawon minti 15 sannan a wanke kafin a shiga wanka a kullum. Ko kuma a hada jus din fiya a rika sha domin magance kaushin fatar daga jiki.

A rika amfani da man kwakwa a fatar jiki. A dora man kwakwa a wuta ya dan yi dumi sannan a shafer fatar jiki kaf da shi na tsawon minti 30 kafin a shiga wanka a kwanta. A rika yin haka kullum.

Shan madara kofi daya kafin a kwanta barci a kullum na taimaka wa fata sosai.

A rika shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka da dare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gaba daya da man kadanya domin samun fata mai laushi mai sheki.

A samu ayaba da nono ko kindirmo a kwaba a waje daya sai a shafa a fuska ko fata na tsawon minti 20 sannan a wanke da ruwan dumi.

A yi amfani da daya daga cikin abubuwan da na lissafo. Kada a hada duka a jiki, amfani da abubuwa da yawa a fata yana haifar da kuraje a fata.

A shafa zuma a fatar jiki baki daya sannan a bar ta na tsawon minti biyar zuwa 10 kafin a shiga wanka a kullum.


Post a Comment

Previous Post Next Post