Abubuwan Da Ke Haddasa Warin Gaba Da Kuma Yadda Za Iya Magancewa

 Wani sa'in al'aurar mace kan yi wari. Ko da a ce kina lura da jikinki da kuma al'aurar, za ki iya fuskantar wari mara dadi a wasu lokutan. Abun damuwa ne idan kin fara jin warin sosai kuma a kullum.



Abubuwan Da Ke Haddasa Warin Gaba Da Kuma Yadda Za Iya Magancewa 

Farkon abun da za ki tambayi kanki idan kina zargin warin al'aurarki ba daidai ba ne shi ne; To yaushe ne warin kan zama daidai ba matsala? Al'aura na da wari na musamman, kuma kowace mace na da nata.

Ana iya kwatanta warin al'aura mara illa da "ɗan bashi-bashi" ko "ƙamshin nama." Jinin al'ada na iya haifar da ɗan wari mai kamar ƙarfe mai tsatsa na ƴan kwanaki kadan.

Jima'i ma na iya canza warin na ɗan lokaci.

A tsarin yadda aka halicci al'aurar mace tana iya wanke kanta da kanta ne. Idan kuka bar al'aurarku a yadda aka halicec ta, to za ta dinga tsaftace kanta ta kuma yaƙi ƙwayoyin cuta masu kai mata farmaki.

Amma idan kuka lura da wani wari daban da wanda kuka saba ji, to da alama akwai matsala.

Wari mai ƙarfi, da kaikayi, da sauyin launi da kuma sauyin yanayin ruwan da ke fitowa daga al'aura na daga cikin alamu cewa akwai matsala.

Yawanci wannan wari na al'aura ko da marar illa ɗin ne ya kan damu mata da dama.

Ga dai wasu hanyoyi bakwai da za su rage tsananin warin da al'aura ke yi, ya kasance ko da za ta yi wari na al'ada wato marar illa, to ba zai yi tsananin da zai dame ki ba.

Lokaci-lokaci, kuna iya bukatar dan taimako kadan don kawar da wari. To ga dabarun da za su iya taimaka muku a kawar da warin al'aura da ba a saba gani ba.

Mun tattauna da wata mayashiyar likita mai wayar da kai a arewacin Najeriya kan kula da lafiyar mata Dr Nai'ma Idris da kuma duba wasu mujallun lafiya. 

Hanyoyi uku da za ku iya magance warin al'aura

1. Kula da tsafta

Wanke tsakiyar ƙafafunki. Ku samu dan ƙaramin tsumma ki goge al'aurarki, zai iya taimakawa wajen wanke matacciyar fata da zufa da kuma datti.

Za ku iya amfani da sabulu mara ƙarfi ku wanke wajen al'aurar, ban da cikinta.

Kar ki wanke can cikin al'aurar da sabulu don yana iya kashe ƙwayoyin halittar da ke kare wajen daga kamuwa da cututtuka. Gara kawai ki yi amfani da isasshen ruwa ki ɗauraye cikin.

Al'aura tana tsaftace kanta da kanta.

Ku guji amfani da sabulu mai kamshi, kamshin sabulun da sinadiran da ke cikin sabulun na iya sauya yanayin lafiyar al'aurar. Amfani da ruwa zalla ma ya isa ya wanke al'aurar mace.

2. Ki guji sa turare a wajen

Dole sai kin guje wa sanya turare a al'aurarki. In har so kike ki yi ƙamshi sai dai ki dan shafa a tsakanin cinyoyinki, amma sa wa a cikin al'ura illa ce sosai da ka iya jawo maki wata cutar.

3. Sauya ɗan kamfai a kai-a kai

Idan kuna yawan amfani da kamfai da aka yi da siliki ko leda ko na roba to lokaci ya yi da za ku koma amfani da kamfai na zallar auduga mai laushi.

Auduga mai laushi na taimakawa wurin bai wa al'aura iska kuma tana yin aiki mai kyau wurin kawar da gumi da ruwa daga jikinku.

Yawan danshi zai iya sa ku kamu da ƙwayoyin cuta da za su yi wa al'aurarku illa.

Sannan ya kamata ku kula ta hanyar yawan sauya kamfai da siket saboda idan suka yi datti kuma kuka maimaita su to akwai yiwuwar su haifar da warin al'aura. Sanin lokacin ganin likita

Idan wannan warin yana tare da alamun da ba ku saba gani ko ji ba, ya kamata ku guji yin magani a gida, ku tuntubi likitanku.

Misali, idan warin al'aurarku ya fi na al'ada ƙarfi kuma ku ka lura cewa yana kara ƙarfi, to kuna bukatar ganin likita.

Haka nan, idan kun ji al'aurarku ta fara wari kamar na "kifi" wannan dalili ne na zuwa ganin likita. Wari mai muni alama ce ta kamuwa da cutar al'aura.

Wadannan warin na iya zama alamun matsala. Kuna iya bukatar likitanku domin ya rubuta magani ko hanyoyin magance matsalar.

Ba za ku so ku jinkirta magance matsalar ba domin cutar al'aurar da ba a nemi maganinta ba kan iya janyo matsalar rashin haihuwa idan ta daɗe ana fama da ita.

Wani ruwa da ke fitowa daga al'aurar mace na iya zama na ka'ida. Idan kun lura da sauyi a launin ruwan, misali, launin da ku ka saba gani fari ne ko bai da kala amma sai ku ka fara ganin wani launin daban, to zai iya yiwuwa kun kamu da cuta.

Yawanci kaikayin al'aura ba matsala ba ce, amma idan ku ka fara jin kaikayin ya fara yawa ko kuma ya fara zafi da radadi, to alama ce na babbar matsala.

Hanyar magance sake fuskantar warin al'aura

Da zarar kin kawar da warin al'aura wanda ba a saba ji ba, ki kiyaye wadannan shawarwari domin hana wata matsalar:

Kula da cin lafiyayyen abinci mai sinadiran gina jiki. Yawaita cin ƴaƴan itace, da kayan lambu. Abinci mai kyawu yana samar da lafiyayyen jiki, kuma hakan ya hada da al'aurarku.

Kasance mai yawan shan ruwa. Shan ruwa mai yawa yana da amfani sosai a dukkan jiki ba sai ga fata ba kawai.

Yana iya taimakawa ga lafiyar al'aurarku, kuma, ta hanyar karfafa gumi mai kyau da sakin ruwa.

Ku guji wanke al'aurarku da sabulu, likitoci sun bayar da shawara a kan kada ku yi kuskuren wanke cikin al'aurarku da sabulu.

Za ku yi zaton cewa sabulu zai wanke al'aurar da kyau amma sabulu kan iya janyo cuta. Ku bar jikin ku ya yi aikin da ya kamata, saboda al'aurarku na wanke kanta.

Ku rinka wanke al'aurarku kafin saduwa da kuma bayan saduwa. Jima'i da kuma shigar abubuwa na daban, kamar man shafawa da maniyyi daga kwaroron roba kan iya janyo wanzuwar ƙwayoyin cuta.

Ku daina yin amfani da matsattsun kaya. Tufafi masu matsewa ba su barin al'aurarku ta sha iska. Samun isasshiyar iskar oxygen na da mahimmanci ga lafiyar al'aura.




Post a Comment

Previous Post Next Post