Yadda Zan Kare Kaina Daga Muguwar Kishiya
Wai ke da kike da Manzon Allah, to har akwai wani ƙazami can da zai iya burgeki?
A wannan zamanin an yi wayewar da yakamata kowa ya ɗau haske waɗan nan ƙazaman bayan ƙarya ba abinda suke yi wallahi.
Eh tabbas akwai masu aiki da aljannu, to amma Allah ya haramta yarda dasu, kuma ko shi aljanin Allah bai bashi sanin me zai faru gobe ba wallahi. Amma abin takaici haka wata mace zata zuba zunzurutun maƙudan kuɗi a gaban wani ƙazami wai don ya faɗa mata idan har ta bari kishiya ta shigo gidanta to zata hanata rawar gaban hantsi, zata rabata da mijinta, zata rabata da mijinta. Wannan duk abu ne da zai faru gobe Allah ne kaɗai yasan me wannan kishiyar taki zata zo da ita. Amma haka wata mace zata zan kashe kuɗi tana ba wannan ƙazamin ita Ala dole so take ayi mata abinda Allah bai mata ba.
Babu wani wanda ya isa yayi abinda Allah bai yi ba. Wannan ne yasa ake kiransa da Ubangiji. Shi Giji ai sunan boka ne kafin kan mutane ya waye su gane wane ne Allah, to a lokacin da suka gane sai suka ce ga Uban-Giji wato ma'ana wanda ke yin abinda yafi na boka Giji kenan, Allah Subhanahu Wata'ala kenan.
Domin biyan buƙata ko kowacce iri ce, to ki yi istigfari da salatin Manzon Allah kafin ki roƙe shi, sai kuma ki ɗauka a ranki duk abinda ya faru muƙaddari ne daga Allah, insha Allahu babu wata kishiya ko wani mugu da ya isa ya cutar dake.
Post a Comment