Girman Kugu Ba Tare Da Kin Kauce Hanya Ba
Ina masu neman karin ‘Hips. ’ Ina son a fahimci cewa girman kugu halitta ce, wasu matan har kauce hanya suke yi, su je a saka musu kugun roba. Kun ga akwai alamar kauce hanya a nan ke nan. Akwai nau’in ababen da mace za ta rika ci, sannu a hankali, kyan diri da halittarta za su kara fitowa, ita ma za ta rika ji ta kara cika, ta yi kyau.
Masana a wannan fannin, sun bayar da shawarwarin amfani da
Abarba,
Ayaba,
Gwanda,
Kankana,
Zuma,
Madarar ruwa.
A kan hada su waje guda, a markada su, har sai sun zama ruwa, sai a dan kara zuma da madara. Bayan wannan, mace za ta rika sha a koda yaushe. Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe, ki hada da ganyen Alayahu, ki zuba Tumatiri da Albasa, ki yi kwadonsu, ki rika ci. Haka nan za ki rika yin wadannan kayan lambun da ki ka markada, sai ki rika sha misali da asuba ko da sassafe kafin ki fara cin komai. Insha Allah za a dace.
Dangane da bayani kan abubuwan ni’ima. Kamar kullum mukan bayyana cewa a yawaita samun
ruwan Rake,
ruwan Kankana,
ruwan Kwakwa,
sai a matse su, a hade ruwan guda. Ki rika sha so uku-uku a rana.
Uwargida, kina iya yin wani hadi na musamman, wanda shi kansa maigida zai iya amfani da shi, hakan ma yana kara dankon soyayya da fahimtar juna. Misali, ki samu
Alkama,
Danyar Gyada,
Waken Soya,
Aya,
Madarar ruwa,
sai ki jika ki markada su, ki tace, idan ya zama gasara sai ki rika damawa kamar yadda ake dama Koko, sai ki zuba madara ta ruwa, ki yi kamar sati biyu kuna sha. Da yardar Allah za a dace.
Haka kuma ga wadanda suke neman hanyar samun waraka daga kaikayin gaba, har ma a wasu lokutan suke fitar da ruwa mai wari, sai su tanadi, Miski daya, Zuma kamar cokali biyu, Man zaitun cokali biyu, sai su hada su guri daya, a samu ‘yar Auduga, a goga abubuwan nan da aka hada da zarar an idar da sallar Asuba, sannan a nemi ruwan dumi, a kama ruwa da shi. Sai ki dauki Audugar da ki ka goga wancan hadin a jiki, sai ki tura audugar ciki kadan, ki bar shi har tsawon awa hudu, ko fiye da haka, sai ki cire. Sannan ki kama tsarki da ruwan dumi. Idan kuka yi ta maimatawa, har tsawon sati guda, insha Allah duk wata cuta da warin gaba za su kau. Allah ya sa mu dace.
Batun sirrin gyaran jiki, ya kamata mu sani cewa jikin mace na bukatar kulawa a kullum. Ya ke ‘yar’uwa, kina iya samun Lalle, ki jika shi, bayan ya kwana, ki tace ruwan ki zuba Humra da Turare, sai ki yi wanka bayan kin yi wankan, kina iya tafasa Lallen, ki zuba a roba ki zauna a ciki kamar na mai jego, wato ‘Sit bath, ’ ki dan zauna a cikin shi na dan lokaci, wannan sirrinsa shi ne fatar ki ba za ta taba lalacewa ba, kuma kariya ce ga saurin takurewar fata. Yana maganin cututukan gaban mace kuma yana kara tsuke mace. Bayan haka, yana maganin basir da kuma karin ni’ima ga mace.
Akwai wani nau’in sinadarin karin ni’ima wanda yake da saurin bayar da sakamakon da ake bukata, wato ‘Sharp-sharp, ’ kamar yadda masu hikima ke cewa. Ki samu danyen Zogale ki hada da Cocumber, ki markada su, sai ki zuba madarar ruwa, ki adana sai ya yi sanyi. Sannan an fi so a rika sha da maraice. Allah ya taimake mu.
Akwai kuma hadin sabulun tsarki da kan ki za ki hada, kun san yin tsarki da sabulun wanka yana kawo wa mace matsala, saboda irin sinadaran Chemicals din da ake hada sabulun yana da hatsari ne ga dan Adam, musamman mata, amma wannan hadin sabulun za ki yi tsarki da shi cikin kwanciyar hankali, ba tare da wata damuwa ba, kuma bayan haka yana maganin cututuka na kaikaiyin gaba, da sauransu.
Da farko, zai ki nemi sabulun Zaitun, amma fa wanda aka rubuta Zaplan a jikin kwalin, kada a ba ki mara kyau. Sai ki nemi Bagaruwa, ki daka ya yi lukwi, ki zuba a roba sai ki yanyanka sabulun zaitun din kanana a kan garin bagaruwan, ki dauko Miskin da kika hada tare ki Kwaba shi da ruwan Hulba, ki kwaba su sosai har sai ya yi kauri. Sai ki zuba a roba mai kyau ki rufe, ko kuma ki samu turmin ki ‘yar karama, ki daka sabulun a ciki. Sai rika wanka da abinki, kina tsarki da shi. Kwararru a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa irin wannan Sabulun ba shi da wani hadari ko ‘Side effect’ ga mace, kuma zai kara tsuke mace, sannan ta rika kamshi da ni’ima
Shawara gareku. Mata
idan kina da sha'awar hips din ki su kara girma bayan wannan hadin da na fada zaki siyan maganin da aka hada dan kara kara samun girman hips dan kara zaman lpy azaman takewar aure bugu da kari ma bawai matan aure ne kadai zasu iya amfani da kayan gyaran hips ba yan mata da dazawara ma zasu iya amfani dashi dan gyara ba wai sai matan aure ba ko wacce ma zata iya gyara kanta da ingantattun magungunan musulunci wanda aka yarda dasu kuma ba su da illah wasun kuma Suna tsoron amfani da wasu magungunan amma suna tsoro abunda zaije yadawo ga lafia jiki dan suna ganin ana tura hotuna a kafafen sadawar mata da yawa sunyi amfani da maganin gyaran hips sun sami matsala to yar uwa shidai magani kala kala ne akwai mai kyau akwai mara sa kyau yawancin wanda ake nunawa cewa yakawo matsala yawanci na turawa ne ba na musulunchi ba anan nake kira da yan uwana mata indai kina son gyaran hips zaki iya yi kuma kada kiyi wani dar aranki indai kintabbatar da ingancin magani zaki sayaa kiyi amfani dashi amma ki tabbatar da na islamic ne bana turawa ba allah yasa mudace ubangiji yatemakemu Baki dayah ameen
Post a Comment