AMFANIN GURJI A FATA
Shin ko Kunsan amfanin gurji a jikin dan Adam?
Gurji na dauke da sinadaran magance gautsin fata sannan yana taimakawa wajen sanya fata sheki da laushi. Kashi casa’in da biyar na gurji na dauke da ruwa don haka yana da kyau a kasance wajen cin gurji kada ku yi wasa da cin gurji domin samun lafiyar jiki da kuma maikon da ke toshe magudar gumi wadda hakan yakan haifar da fesowar kuraje wadda sai an dage kafin a rabu da su. Wannan kayan lambun na taimakawa wajen rage kiba ga mace idan har ta kasance cin sa shi kadai da kuma rage cin abinci masu nauyi wadanda ke gina jiki.
Abubuwan Da Gurji Keyi Ajikin Dan Adam
1 Rage Ƙiba Ko Tumbi
2 Fitar Da Ƙurajen Fuska Pimpus
3 Ƙara Hasken Fata
4 Gyara Fata Idan Ta Koɗe
Suna da yawa
Ga yadda ake amfani da shi.
DOMIN RAGE KIBA KO TUMBI; a samu gurji sannan a fere bawonsa sannan a yayyanka shi kanana sannan a zuba a bilinda a markade a markada shi sai a tace ruwansa sannan a zuba cokali biyu na zuma a ciki sannan a zuba a kwalba a jijjiga kwalbar. Sannan a hada da ruwan lemun tsami da citta sai a rika sha yana rage kiba da tumbi.
KURAJEN FUSKA; a markada gurji da ruwa zalla bayan an fere bawonsa sannan a samu auduga a rika shafawa a fuska sau biyu a rana domin magance kurajen fuska da kuma sanya sulbin fata.
HASKEN FATA; a markada gurji sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki a rika shafawa a fuska da wuya kamar sau biyu a rana ya yi a kalla mintuna goma sha biyar kafin a wanke a kullum.
KODEWAR FATA; A markada gurji sannan a zuba kindirmo da garin alkama cokula biyu sannan a kwaba a rika shafawa a inda fatar ta kode sakamakon kunar rana ko yawan shiga rana. A bari a fuska na tsawon mintuna goma sha biyar kafin a wanke.
YAKUNEWAR FATA; a markada ruwan gurjin sannan a samu kwai a cire kwanduwar ayi amfani da farin ruwan a ciki sannan a matse lemun tsami a kwaba a rika shafawa a wajajen da fatar ta yankune. Sannan a bari na tsawon mintuna talatin kafin a wanke. Ana so a rika yin wannan hadin kamar sau biyu a rana a kullum.
DOMIN SAMUN GASHI MAI TSAYi; a markada gurji da ruwa sannan a tsaga gashin kai a shafa a fatar har a cikin gashin kai ya ji sosai. Sannan a samu leda a rufe kan na tsawon mintuna talatin kafin a wanke da man wanke gashi.
Post a Comment