Yadda Ake Sarrafa Dabino Domin Karin Ni'ima

 



Yadda Ake Amfani Da Ya'yan Dabino Domin Karin Ni'ima 

A ilmin kimiyya shi dabino yana da tarin sinadarai da jiki ke bukata. Kusan vtimins irin vitamin A Calcium iron menerals B complex da irinsu amino acid dukansu Dabino nada su. Shi kansa dabino ruwan cikinsa yafi aiki shiyasa nakeson kawo maku yadda ake amfani da shi ruwan dabinon domin ku ma'aurata da masu shirin auren, amman kada budurwa ko saurayi wanda bai tashi aure ba yayi.

Ni'imar Dake Cikin Kowacce Rana Kamar Dai Ranar Juma'a 

Tayaya zan sarrafa dabino domin samun ingantacciyar ni'ima?


Da farko dai Zaki samu abubuwa kamar haka. Garin minannas, madarar ruwa sai kuma shi dabino.


√ Da farko zaki samu dabino, Ki bare dabinonki rabin kwano, ko dai yadda kika ji zaki iya nemowa mai yawa haka sai ki jika da ruwa Idan ya yi luguf sai ki markada a ‘blander’ Zaki ganshi da kauri kirtif. Sai ki ajiye a cikin pridge


 ko kuma wajen da ke da sanyi wanda ba zai lalace ba. Duk lokacin da za ki sha saiki debi cokali biyu ki zuba a kofi, ki juye madarar ruwa gwangwani daya, ki sa garin minannas karamin cokali ki juya sosai, Idan ya yi kauri da yawa ki kara ruwa kadan ki koma juyawa, ki shanye duka. Bayan awa uku da shankii za ki tsinci kanki cikin wani yanayi na lutsutsu da son kasancewa da maigidanki Za ki ji dadin da ki ka dade ba ki ji ba._

Maigida kuwa zai gamsu da ke sosai, kuma idan an yi dace da ciki za a samu lafiyayyen jariri ko jaririya.


Allah ya taimaka 


ArewacinNaija News 

Post a Comment

Previous Post Next Post