Yadda Ake Ƙarawa Gashi Tsawo Da Baki Ba Tare An Kashe Wasu Kudi Masu Yawa Ba

Yadda Zaki Gyara Gashin Kanki Yayi Kyau Yayi Ƙyalli Ba Tare Da Kin Kashe Wasu Kudi Masu Yawa Ba. 




Shi dai gashin kai sanin kowacce mace ne shine tushen kwalliya wanda ke gwada kyan kan mace. Idan mace ta rasa rashin kai komo tayiwa kan kwalliya ko daurin dan kwali ba zai zauna da kyau ba, saboda haka ne mukayi nazarin kawo muku waannan hadin wanda zai taimaka muku wajen gyara gashin kai, ba tare da kinsha wahala ba.


Abubuwan Da Ake Bukata

Dankalin Turawa

Shampoo

Blender

Kwai 

Albasa

Vitamin E


Yadda Ake Hadawa;


Da farko zaki bare dankalin turawanki saiki yayyanka shi, sai kuma albasar ita ma ki yayyankata, sai ki kawo blender dinki saiki nika albasar da kuma dankalin turawanki waje guda, idan ya nuku sosai saiki tace ta ki fitar da dusar saiki dau ruwan dashi zaayi amfani. 


Domin Wanke Fuska Tayi Kyau

Bayan kintace saiki dauki ruwan saiki dauko kwai  saiki fasa a kai ki juyashi sosai yada kwan zai hade sosai da wannan ruwan da kika tace,


Sai kuma ki kawo Vitamin E dinki shima kisanya a ciki saiki kuma juyawa sosai yadda vitamin E din zai gauraye ko ina a ciki. Bayan kin tabbatar ya juyu saiki barshi har tsawon awa daya.


Shike nan ya hadu saiki shafe gashin naki sosai dashi. Bayan kin tabbatar kin shafe ko ina dashi saiki barshi har tsawon awa 1, saiki dauko man shampoo dinki ki wanke kan naki dashi. To insha Allahu kashin kanki zai koma kamar haka.

Post a Comment

Previous Post Next Post