- AMFANIN KARAS GA FATA
Yadda Ake Amfani Da Karas (Carrots) Domin Magance Gishirin Fuska Da Kuma Gyaran Fata
Barkanmu da safiyar yau juma'a. Kamar yadda aka sani cewa karas na dauke da sinadarin bitamin A domin gyara ido da kuma ganin mutum. Bayan haka, akwai abubuwa da yawa da karas ya ke yi domin inganta fata. Domin sanin mahimmancin karas, shi ya sa a yau na kawo muku yadda za a yi amfani da shi domin magance cututtukan fata da dama.
A cikin kwanakin nan insha Allahu posting dinmu zai tafi ne game da fata, domin kuwa ita ce uwa sha kallo a kowacce irin kwalliya a wurin baƙar mace ko fara.
Yadda Gurji Yake Gyara Fata, Tayi Kyau Tayi Haske
Ga kadan daga cikin jerin amfanin da Karas Keyi;
1. Cin karas na sanya fata sheki da laushi ga kuma gyara ido domin yana dauke da sinadarin bitamin A da wadansu sinadaren gyara jiki.
2. A markada karas sannan a sha ruwansa domin magance tabon fuska da kuma sanya ciwon fata warkewa da wuri.
3. Karas na daya daga cikin abincin da ke rage tsufan fata da wuri. Don haka ana iya markada shi a shafa a fata ko kuma a sha a kalla kullum a rana.
4. Shan JUS din karas (markadadden rowan karas), musamman lokacin zafi na magance tabon rana da yake fesowa a fuska. Sai a ga fuska ta yi dabbare-dabbare launi daban-daban. Yana da kyau a yawaita shan jus din a lokacin zafi.
5. Rashin cin kanwa a abinci na janyo gautsin fata, don haka sai a shan jus din karas domin samun fata mai sulbi.
6. Domin sinadaren da karas ke dauke da su, yana taimakawa wajen magance kurajen fuska da sauransu. Fesowar kurajen na faruwa ne idan an rasa sinadarin bitamin A a fata. Don haka sai a ci karas. Amma yawan cin karas na iya canza launin fata.
Idan an ji ciwo za a iya shafa dakakken karas a wurin domin yana taimakawa wajen warkar da ciwo.
A markada karas sannan a zuba madara da zaitun kadan da zuma, sannan a kwaba a shafa a fuska na tsawon mintuna 30. Hakan na magance fesowar kurajen fuska.
Post a Comment