Addu'ar Neman Tsari Daga Dukan Wani

 


Addu'ar Neman Kariya Daga Ubangiji Wacce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yake Karantawa

Daga Ushman bin Affan رضي الله عنه yana cewa, lallai Manzon Allah ﷺ yace:-
(Wanda yace
*_بسمِ اللهِ الذي لا يَضرُ مع اسمِه شيءٌ في الأرضِ ولا في السماءِ وهو السميعُ العليمِ
Bismil-lahil-lathee la yadurru ma'as-mihi shay-on fil-ardi wala fis-sama-i wahuwas-samee'ul-'aleem ya fada sau uku,babu wani bala'i ba zai sameshi ba har sai ya wari gari, idan kuma ya fada da safe babu wani bala'i da zai sameshi har sai yayi yammaci). 
@الألباني صحيح ابي داود ٥٠٨٨



A Kiyaye
Ana karanta wannan addu'ar ne sau uku da safe bayan sallar Assuaba da yamma kuma tun daga bayan sallar la'asar har zuwa cikin dare zaka iya karantawa

الشيخ د. عبد الرزاق البدر حفظه الله تعالى:
Yana cewa:-
"Wannan zikiri ne mai girman matsayi a wajen Allah dan haka ya dace ga kowane musulmi ya kiyaye yinsa a kowane yini da safiya, dan ya sami kariya da tsari na musamman daga Allah akan dukkan wani abin cutarwa,..............".
@فقه الأدعية والأذكار ٣/١٢


             Allah ne mafi sani

Post a Comment

Previous Post Next Post