Abubuwan Da Yakamata Mace Mai Ciki Tayi Domin Inganta Lafiyarta Da Na Jaririnta

 Abubuwan Da Yakamata Mace Mai Ciki Tayi Domin Inganta Lafiyarta Da Na Jaririnta 



HANYOYIN INGANTA LAFIYA TA JIKI A GIDA CIKIN SAUKI MUSAMMAN MASU YAWAN KIBA DA NAUYIN JIKI KO KUMA MASU CIKI 


Akwai nau'ukan abinci da su ke kunshe da sinadaran gina jiki kuma wanda su ke taimakawa mace mai ciki don samun ingantaccen lafiya kamar kara karfin kashi, kariya daga cututtuka, karfin gani na ido ko kuma su bayar da kwanciyar hankali da nutsuwa ga mai amfani da su.

Ga jerin nau'ukan abinci kala uku wadanda su ke taimakawa wajen rage nauyin jiki saboda da yawan mata masu ciki na kukan jikin su ya mu su nauyi ta yadda ba kowane irin motsi su ke iyawa ba.

1. ALKAMA
Alkama ta na kunshe da sinadarai wadanda su ke taimakawa mai amfani da su tsawon yini da su ke bunkasa ingancin kayan cikin sa da karfafa su wajen kone daskarerren maiko.

2. KAYAN ITATUWA (Kayan marmari)

Babu wata matsala don mutum ya sha maiko don idan har za ka sha maiko kuma ya sha dan itacen kayan maramari to ba shi da wata matsalar jin nauyin jiki. Su kayan itatuwa irin su inibi, abarba, gwanda, kankana, lemon bawo da na tsami su na dauke ne da da sinadarin Oleic acid wanda ya ke kone duk wani maiko da ke cikin mutum sannan kuma ya bunkasa lafiyar jinin jikin mutum.

3. KIFI

Yin amfani da tsokar kifi ita kadai ba ta rage nauyin jiki, sai dai ta na da sinadarai na PROTEIN wanda su ke taimakawa wajen kara lafiyar jiki, inganta yalwar jini a jiki da taimakawa wajen mayar da tsokar rauni da mutum ya samu.

Ita tsokar kifi tana da sinadarai na gina jikin dan Adam kuma duk yawan amfani da mutum zai yi da ita ba za ta kara masa nauyin jiki ba saboda babu maiko wanda daman maiko shine abu mai assasa jikin mutum ya yi nauyi.

Allah ka bawa mata masu ciki ikon sauke abinda suka dauka na tsawon wata tara 


Post a Comment

Previous Post Next Post