Abubuwan Da Yakamata Kowacce Uwa Tayi Akan Yayanta.
Kowacce Mahaifiya yana da kyau ta kiyaye wadan nan abubuwan da zan zayyano domin inganta rayuwar yayanta. Mahaifiya, mahaifiya ce amma wata ta tafi wata, haka kuma kowacce Mahaifiya tana son ganin yaranta sun tashi cikin karamci da biyayya da girmama mutane. A takaice dai kowacce Mahaifiya tana son ganin yaranta sun rayu cikin ingantacciyar rayuwa. Duk mahaifiyar da take son ganin rayuwar yayanta cikin inganci to dole sai ta kiyaye wasu abubuwa kamar haka;
1. Mahaifiya Mai Kunya; yana da kyau ki kiyaye duk wani abu na rashin kunya, kada ki yi a gaban yayanki, domin idan kika yi, to yaranki ma haka zasu ta so sunayi, domin kuwa hausawa ma na cewa duk inda saniyar gaba tasha ruwa to ta baya ma nan zata sha. A wannan zamanin yadda social media ya yawaita wasu matan TikTok suke yi, to idan yaranki suka taso yan TikTok waye abin zarginki? Don haka dole ne kiyaye duk wani abu na rashin kunya.
2. Mahaifiya Mai Son Karatu; ki kasance mahaifiyar da ke son ganin yaranta na karatu. Akodayaushe a kowane hali a ko ina idan lokacin karatu yayi lallai ki tabbatar da yaranki sun tafi makaranta. Kada ki kasance uwar da take son ganin yara a gabanta a kowane lokaci kice ke baki son rabuwa da su. Bari su je makarantar boko da ma islamiyya.
3. Mahaifiya Mai Girmama Mijinta; a lokacin da yaranki suka taso kece ta farko da zasu Fara gani, sai kuma mahaifinsu. Idan kika gaza yi masa biyayya a gabansu su ma haka zasu taso su gaza yi wa kowa biyayya, amma idan kin kasance mai girmama mahaifinsu haka zasu taso cikin biyayya da girmama manyansu.
4. Maifiyata Mai Tsawatawarwa Yaranta; Idan har yaranki su ka janyo magana ko wani rikici ya hadasu da yaran unguwa kada ki kasance mai shige musu ko da kuwa suna da gaskiya, idan ba haka ba kuwa tun suna yaran zaki ga kuskuren shige musu saboda kullun cikin janyo magana suke, amma idan kika kiyaye hakan sai kiga har girmansu ba ruwansu da shiga sha'anin da ba nasu ba balle har su dauko miki magana.
5. Mahaifiya Mai Ibada; ki kasance mai kula da ibadar yaranta kuma kema ki kasance mai yawaita ibada. Ice tun yana danye ake tankwara shi, idan ya bushe ba zai tankwaru ba. Idan yaranki suka kasance masu ibadah wannan har mutuwar ki zaki ji dadi domin kuwa kin koya musu yadda zasu samo miki rahama a wurin Ubangiji.
Abubuwan da Yakamata kowacce Uwa ta yi suna da yawa amma dai ana son kowacce Mahaifiya ta kiyaye wannan.
Allah ya bamu ladan kiyaye yaranmu
Post a Comment