Sunyi Min Illah Hausa Novels Na Lailat Adam

 𝗦𝗨𝗡 𝗬𝗜 𝗠I𝗡 𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛.



𝗦𝘁𝗼𝗿𝘆/𝗪𝗿𝗶𝘁𝗶𝗻𝗴:𝗟𝗮𝗶𝗹𝗮𝘁 𝗔𝗯𝗱𝘂𝗹𝗹𝗮𝗵𝗶.


𝗣𝗿𝗼𝗳𝗶𝗰𝗶𝗲𝗻𝘁 𝗪𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿 𝗔𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗶𝗼𝗻.


Kokarin azawa akan tafarki,shi ne abu mafi muhimmanci da yakamata marubuta su kware akai,mu proficient writers association za mu yada wannan manufa.



_____________________________

𝗣𝗮𝗴𝗲 1_𝗘𝗻𝗱


Kwance take tana ta juye-juye wata irin muguwan sha'awa ke damunta ko barcin ta kasa yi,duban ta ta kai kan agogon bangon da da ke ɗakin taga ƙarfe biyu ne na dare 2:00pm.


Waya ta ɗauka tare da nemo wata number,ta danna kira sai da ta kusa katsewa kafin aka ɗaga"Hello kawata"akace daga wancen ɓangaren. 


Saida ta gyara kwanciyar kana tace "ƙawata na kasa barci sauƙi nake nema wallahi,littafin nan da kika turoman sai yanzu na gama karanta shi,gaba-ɗaya jina nake acikin yanayi, gashi banidamafita kuma nakasa bacci, don Allah fada min miye zanyi nasamu sahida".


Dariya tayi tace"ai dama na faɗa miki marubuciyar'yar harka ce,ta san yanda zata ɗora mutum kan network.


"Yanzu dai ba wannan ba,miye mafita dan ni kam bazan iya barci acikin irin

 wannan halin ba,kawai so nake naji irin abinda jarumar littafin nan taji"


Cikin dariya da kai daga ji kasan ta mugunta ce tace"kin ga yanzu dare ne,kuma wannan gayen da ke ɗebe mana kewa ya ɗan yi tafiya,amma ga wani video nan zan tura miki,ki ɗan rage zafi da shi,idan kin kasa kuma kawai kiyi kamar yanda kika saba kafin goben mu ga yanda za'ayi"bata jira cewarta ba ƙit ta kashe wayan tana dariya,dan alƙawali ta ɗauka sai ta lalata tarbiyyar ƙawarta ta,saboda ita ma bata da ita.


Da sauri ta buɗe datan,ta kuwa turo mata videon,kallo ta fara amma dai babu alamar gamsuwa dan ita a aikace take buƙatar yanayin, ba kallon ba.


Dubanta ta kai kan ƙanwarta da ke barci kusa da ita hankalinta kwance,matsawa tayi ta fara shashshafa mata jiki dan samun sauƙi a cewar shaiɗaniyar zociyarta.


Cikin barci take jin wannan al'amari,tana buɗe ido kuwa taga yayarta ce da wannan aiki"aunty sauda yauma wani littafin kika sake karantawa?".


Idanunta a lumshe ta ce "eh ƙanwata ki taimaka mani daga yau shikenan bazan sake ba" "to ai kullum haka kike cewa aunty sauda da wannan rayuwar kiyi aure mana zai fiye miki ai".


Ita dai bata ce komai ba,dan a matuƙar matse take,biye mata tayi har ta samu natsuwa,kamar yanda suka saba sannan suka kwanta,dan kusan kullum abinda ke faruwa kenan. Saudat ada can baya yarinya ce mai natsuwa da kamun kai, amma dalilin kawar banza, da karanta littaffan banza yasa ta lalace, wanda lalecewar ta har ya shafi kanwata, domin wani lokacin da ita take rage zafi idan tayi banzan karatunta.


Wani lokacin kuma su samu yaron da kawarta ta hadasu ya rage mata, shi kuwa yaro a sama ya samu mata har biyu, wannan shine tsuntsu daga sama gasasshe, bashida damuwar komai kullum cikin shiri yake zama, da sun kirashi zai amsa kiran cikin nishadi.


Yau tun safe sauda ke ta amai babu tsayawa,hakan yasa ummanta ɗaukarta suka nufi asibiti.


Innalillahi wa'inna ilahirraji'un ummansu sauda ta ambata tare da faɗuwa ta suma,bayan jin abinda likita yace,wai sauda tana da ciki har na wata 2.


Ummi ce ƙanwar sauda ta kira mahaifinsu a waya ta sanar da shi halin da ake ciki,cikin tashin hankali ya nufo asibitin,ya tarar da umman ta farfaɗo hakan yasa suka tarkata suka nufi gida cike da tsantsan tashin hankali.


Sauda kuwa kuka kawai take tare da nadama marar amfani,ji take dama bata zo duniya ba,yau itace da ciki batare da aure ba, gashi yanzu bata san yyaro zai anshi cikin ko yaya, son zuciya da biyewa ƙawarta da karatun littattafan batsa gashi SUN YI MATA ILLAH.


Shaƙeta umma tayi tana kuka tana cewa"kin bani kunya sauda kin cuce mu cuta mafi muni,idan aure kikeso miyasa baki faɗa min anyi miki aure ba,shine zaki haɗa mu da abin kunyar da zai ta bibiyar rayuwar mu".


Ganin tana nema tayi kisan kai yasa abba ya karɓe ta tare da cewa"mu bi komai a hankali,mai afkuwa ce dai ta riga ta afku,ta faɗa mana waye yayi mata cikin".


Kuka sauda take tana faɗin"dan Allah kuyi haƙuri ku yafeman abba,wata ƙawata ce ta fara kwaɗaitar da ni karanta littafin batsa,duk wani sabon littafi idan ya fito zata turoman shi,har ta kai ta fara jana muna zuwa wurin wani yaro dan mu dinga gwada yanda akeyi a kowane littafi da muka karanta,duk kuwa ranar da ba muje ba in dai na karanta wani littafin idan narasa natsuwa ta,itace take turoman videos na banza na kalla,ko kuma na nemi ummi kamar yanda ƙawar tawa ta bani shawara,tun ummi bata yadda,har ta kai tana yadda saboda tausayi na da take ji,dan har kuka nake yi mata, shine kawai nasan yataba mu'amala dani." Ta karasa maganar cikin matsanan cin kuka da kunya.


Sun matuƙar shiga cikin tashin hankali da jin wannan labari sosai da tunanin wai duk suna cikin gidan wannan badaƙalar ta ringa faruwa,amma suka kasa fahimta,lalle sun cika iyaye marassa kula da amanar da Allah ya ba su.


Abba yayi musu nasiha mai ratsa zociya,tare da nusar da su akan irin littafin da zasu karanta idanma karatun ya zama dole,tunda akwai marubuta ɓata gari,akwai kuma na kirki masu yi domin wa'azantarwa.


Sannan kuma ya dakatar da umma daga ƙudirin zubar da cikin da takeyi,inda yace"kuskure ne akan kuskure kike shirin aikatawa, domin alhakin zai zama biyu ga zina ga kuma kisan kai.


Anan take ummi ta faɗawa iyayenta tana so suyi mata aure,dan gudun faɗawa irin halin da yayarta ta ke ciki a yanzu,basu wani ja ba suka amince duk da ƙananun shekarunta.


Ita kuwa sauda ta cigaba da rainon cikinta,yayin da labari ya zagaye unguwa cewa sauda tayi cikin shege,hakan yasa ko ƙofar gida ta daina fita saboda tsokanarta da akeyi.


Daga baya ne suke samun labarin ƙawar sauda ta kamu da cuta mai karya garkuwan jiki(HIV) ranar da labarin ya riske Saudat tayi kuka sosai, tare da godiya ga Allah, da Allah yasa ita nasa ya tsaya a haka, cikin zuciyar tace ashe ni nawa nafila ne, ita wannan hadda cuta, lalle na yarda duk wanda ya taka dokar Allah bazaiga da kyau ba...


Allah ya kiyashe mu da aikin dana sani.


𝗔𝗹𝗵𝗮𝗺𝗱𝘂𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵𝗶

𝗟𝗮𝗶𝗹𝗮𝘁 𝗔𝗯𝗱𝘂𝗹𝗹𝗮𝗵𝗶✍️

Post a Comment

Previous Post Next Post