KUSKURENA
By
Muhammad B.Ahmad
Dedicated to auntyna
( Rukayyat ikra) Allah y saka da mafificin alkhairi ya kareki daga dukkanin sharri
PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION
"The ability to guide is what all writer can have,we proficient writers will share those qualities"
Page 1 to end
Na'ura mai kwakwalwa(computer) ce a gabana nake ta maida wa mutane amsar sakonnin da suke turomin ta kafofin sada zumuta, wanda hakan ya zamemin jiki kullum kasancewata ta marubuci. zafin da idona kemin yasa na fahimci cewa dare yayi batare da na ankara ba 1:20am agogon dake jikin computer ta ya gwada min hakan shi yayi daidai da shigowar kira cikin wayata boyayyen number ce aka kirawoni da ita, hakan ya sani shakkar dagawa, wanda a da bahaka bane hakan ta fara faruwa ne tun sanda na fara rubuta batsa a cikin littattafai na lokuta da dama kirane na zagi ko kuma wa'azi,
Amma nayi biris da kunnena sakamakon karin mabiya da nake samu ta kafafen sadarwa da kuma maziyarta a shafina na yanar gizo kiran ne ya kara shigowa a karo na biyu daga kiran nayi batare da nayi magana ba muryar mace naji wadda bata da maraba da ta 'yata fadila katse kiran nayi saurin yi na shiga kokwanto kiran ne ya kara shigowa a karo na 3 Daga wa nayi domin in kauda kokwanton dake raina sallama nayi ta amsa min amma cikin rudani naji ta ambaci sunana hakan shiya tabbatar min da cewa da 'yata nake waya cikin hanzari na yanke wayar,zuface take karyomin ta koina duk da sanyin Ac dake duka na, da wane ido Zan kalli 'yata a matsayina na mahaifinta, ita kuma da wane ido zata kalleni a amatsayinta na 'yata, duk a dalilin kuskurena na rubutun batsa. Kashe computer ta nayi na kwanta bacci barawo ne kawai ya daukeni a wannan daren, rashin baccin da na samu shi yai sanadiyyar makarata a masallaci bayan dawo wata na shiga dakinta na biya na tayar da ita samun wayar ta nayi a yaushe bisa saide drower budewa wayan nayi sakamakon ita ba ma'abociyar saka lambar sirri(security) bace a wayar ta ina budewa kan shafi na na gani hakan shi yake nuni da tana karantawa baccin ya dauke, ta fitowa nayi daga shafin na duba call log number ta na gani ta social media hakan shi ya kara tabbatar min da 'yata ta fada tarkon karanta labarai na rubutun da nake, mayar mata da wayar nayi yadda ta ajjiyeta na bugi pillown data dora kanta akai farkawa tayi dauke da adduar tashi daga bacci a bakinta, magana nayi mata akan tayi sallah ta cemin "a'a" cewa nayi ta tashi tayi na fice daga dakin na koma dakina zauna wa nayi na fara tunani akan abinda nakeyi duk da nasan ba abun alkairi nake rubutawa ba, in na mutu a wannan yanayin ya ya zanje na riski ubangijina the worst thing ma tsinuwar danake sha kullum da Allah yaisa ga 'yata ta fada tarkon hakan.
**
Tashi tayi tayi sallah ta zauna yin azkar daga nana ta fada tunani anya kuwa kunnuwanta daidai suka jiye mata in har abbanta ne bazai zo ya tashe ta ba Kuma lokacin da tayi kiran baccine a idonta kai gaskiya bashi bane abbana bazai taba yin hakan ,ba wata zuciyar ta bata amsa tunani ta fara yi in ta mutu tana wannan halin ko in abbanta ya kamata ko ummanta da wane ido zata kallesu wayar ta ta dauki akan side drawer ta goge duk wani abu dake Alaka da haramci tayi istigfari da kuma adduar Allah ya kara kare sauran Alummar musulmi daga wayan nan miyagun mutane wanda basa yada alkairi sai akasin haka,*
Ta bangarena kuwa layin social medias dina na zare daga cikin wayata na karyashi tare da goge duk wani rubutun da nayi wanda ya sabawa Sharia istigfari nayi tare da addu'ar shirya gamasu hali irin nawa na son zuciya da biyewa rudinta, bacci na koma sai da matata ta tasheni domin 8:30am kasantuwar yau weekend ba aiki wanka nayi bayan na shirya na fita dining duk sun hallara ni kawai suke jira,i"na kwana abbana" fadila tacemin kallonta nayi nayi mata murmushi tare dace "hope kin tashi lafiya yar abbanta" "lafiya lau abbanah" serving dinmu matata tayi muka fara breakfast hakan shi ya kara tabbatar wa fadila da cewa lallai bani bane ta kira jiya domin dataga canji a gareni,
Wannan ne ya kara bani damar godema Allah da ya bani ikon farga tunda wuri kuskuren da na ke aikatawa bai shafi rayuwar diya ta,tunda ga lokachin na kara kusanci daga ubangiji,da nasiha ga dukkan wanda nasan suna cikin irin wannan mumman diba'ar,dan nayi abokai sosai masu taya ni,da kuma wanda suma aikin su kenan rubutun batsan'
Kuskuren da na yi shi ya kara Mani karfin imani da kuma kara tattalin rayuwar yarana ta hanyar yawan kansu ajikina da kuma wa azi akai akai,
Da wannan na dage babu dare abu rana ina kara neman gafaran ubangi da gode masa abinsa boye Mani wannan babban kuskuren da ya so ya faru gare ni,da wanann nake kara jan hankalin dukkan masu wanann mugun halin na rubutun batsa su ji tsoron Allah dan Ni naga babban kuskure da aya akansa,
Sai mutum ya gyara sannan shima za a gyara masa,tunda ganan na zama wani babban shaharran uztazi mai yawan abaton Allah abisa dukkan lamurran rayuwata,kuma ina kara wayar ma mutane da kai akan su gyara su dai na,dan Ni na ga nawa kuskuren,
Nayi tunanin raba ta da wayar hannun ta,sai nayi zurfin tunanin raba ta da wayar za ya tabbatar mata da cewa tabbas Ni ne maihaifinta taji murya na,sai na bar mata wayar amman akai kai nakan masu nasiha cikin sigar da za su gane su kuma fahimta,.na kan sa mahaifiyar ta tana dan duba wayar ta,akai akai dan karda ta koma ruwa,shiyasa akace idan ka aika ta alkhari alkairi shine za ya bika,Ni dai ga babban kuskuren da na yi ta sana din rubutun batsa,wanda har yanzu abun bai dena Mani yawo acikin kwakwalwar kai na ba...
Alhamdulillah
Post a Comment