Kowa Ya Tuba Don Wuya Ba Lada Hausa Novels Na Ummu Najma

 KOWA YA TUBA DAN WIUYA BA LADA

             


Gajeran labari

       NA

 UMMU NAJMA


PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION


Kokarin azawa akan tafarki,shi ne abu mafi muhimmanci da yakamata marubuta su kware akai,mu proficient writers association za mu yada wannan manufa.


Sauri take ta faman yi don tagama aikinta yayinda gaba-ɗaya hankalin ta nakan wayarta wanda tasa caji, cikin mintunan dabasu huce talatin ba ta gama girkinta, shinkafa da mai da yaji taiye, kwashe shinkafartayi tasa a kula, kana tashiga wanka, shap-shap tayi wankan ta dawo falo tazauna ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya, cikin zumuɗi taɗauki wayanta ta kunna data, don tasan saƙonnin mutane na nan cike, Allah Allah take taga comment ɗin fans ɗinta, yaronta ɗan karami ne, kuma bai cika rigima ba, shi yaro ne mai shan hannu, don haka idan ta ɗungure shi guɗaya yasamu yatsonsa biyu a baki, to zai wini baiyi kuka ba, shiyasa take samun lokacin cin karanta ba baɓɓaƙa.

koda ta buɗe wayarta saƙonni ne kala kala suketa shigowa, wasu a Groups wasu ta private, group guda tazaba cikin tarin groups din, ta shiga inda taga anata zu-zuta littafin da take rubutawa me suna NIDA ƊAN AIKI NA, inda gaba-ɗaya zallar batsa ne a cikisa, masoyan ta nata tunzurata, suna kara fasa mata kai, babu abinda takeyi sai murmushi, tanajin matukar farin cikin itama yau tazama cele, wani sakone ya ɗauki hankalinta, inda wata budurwa a group ɗin ke cewa "wuta wuta mutumniya ta kina bamu nishaɗi wallahi, jiya littafin ki yasani shauki sosai, sai dai banida miji balle ya rage min zafi, haka nayita mutsu mutsu ina sakarwa kaina ruwan sanyi har garin Allah ya wa ye, dariya tayi ta tura mata ɗan kwallage mai alamar gwalo, nan wata ma tace "muna jiran post, don Allah kada a shanƴamu" amsa tabasu da cewa "yanxu ma kuwa editing kawai zanƴi." nan ta sauke data ta fara editing baji ba gani, inda take kara tsaurara harshen batsa a ciki, koda a ka kira sallar azahar kasa tashi tayi har lokacinta ya wuce, mijinta dama idan ya fita sai dare yake dawo gida, shiyasa take samun ciƙaƙen lokacin yin rubutu yanda taga dama.

Aisha kenan, matar aure ce tanada yaro ɗaya, yawan karance-karancen littaffan hausa online da take yi ne yasa mata ra'ayin fara rubutu, dan taga itama tanada nata basirar na fadakar da mutane ta wannan hanƴa, dan haka ta yanke shawarar farawa amma zata boye sunanta ne, dan kada aganeta, da farko ta fara littafinta ne cikin kiyaye doƙokin Ubangiji, inda take anfani da sunan Ummu Nabel, ganin har ta share tsawan lokaci tana rubutu batayi suna ba yasa ta sauya ra'ayi, inda tafara rubuta littafin batsa, da nufin ƙoyarda matan aure kwanciyar aure, cewar jama'ar social media sunfi son na baɗala da tijara, ita kuma gurinta bai huce yau taji duniyar gizo ana maganarta ba. a cikin groups ɗinta kuwa a kwai wata marubuciya mai suna fatima, wadda take rubutunta mai tsafta, cikin kwarewa da tsoron Allah tasha yi ma Ummu Nabel nasiha akan illar rubutun da takeyi, sai dai tayi dariya tace "zan gyara" amma fa ba gyarawan zatayi ba, cikin lokaci kaɗan ta kware a harƙar batsa, tauraron ta na haskawa a kowane groups na whstap

inda a gefe guda kuma take samun masu zagi da tofin Allah tsine, akan irin ɓata musu tarbiyan yara da takeyi.(wanna kenan)

Yau ma kamar kullum anturo littafin NIDA ƊAN AIKI NA a wani group, inda mutane suka shiga muhawara a kan littafn tare da aibanta marubuciyar, wasu na mata addu'ar shiriya wasu kuma akasin haka, cikin hirar tasu wata tace "Allah ya shiryeta idan mai shiryuwa ce, idan ba itace ba kuma Allah ya mana maganin ta ya hukunta cikin gaggawa, kuma insha Allahu yanda ta rubutu wanga baɗala sai ƴaƴanta sunga ni, kuma sun karanta"

kalmar nan ta razana ƙawarta fatima, domin tana cikin group ɗin kuma tana kallon muhawaran dasuke yi, inda ta ɗauki wannan sakon ta turama Ummu Nabel, dariya tayi lokacin da ta gama karanta abunda fatima ta tura mata, kana tace "yarana bazasu gani ba Fateema" bahaka Fatima tasoji ba don haka tace "to kidai bi a sannu dan wani in ya yi addu'a Allah yana amsawa ne nan take."

kafin ta gama littafin NIDA ƊAN AIKI NA sai tafara tallan wani wai ZATA FASHE, inda tace taƙaro walakanci, kuma tace na kuɗi ne 500 kacal, nan fa aka fara tururuwar sayan littafin a duniyar whatsp, tunkan tafara sakin littafin, sosai asusu bankinta ke karɓar sakonni Nera dare da rana, duk wannan abin da takeyi, miji bai sani ba bare yan uwanta.

Yauma kwance take akan gadonta tana rubutu wajen karfe biyu na dare, gefenta kuwa mijinne kwance yana bacci, rubutun sabon littafin ZATA FASHE takeyi, wanda a halin yanzu tanada shafi biyar a aje, tana cikin rubuta badalarta taji kaman an buga mata guduma akai, da sauri ta dafe kan, kana ta kalli gefe inda mijin yake, jim tayi kana ta kauda kai taci gaba da rubutu, da sauri ta jefar da wayar dan wanga karon ba bugu kaɗan aka mata ba, dafe kanta tayi da hannun biyu, a ranta tana tunani gajiya ce da rashin bacci, don haka ta kwanta ta reke kan, sai dai koda ta kwanta barci ya gagareta, saboda tsananin ciwan da kanta ke mata, karfe biyar da rabi mijin ya tashi, ganinta zaune rike da kai yasashi tsaya wa daga shiga Tolet, hannunta ya kama kana yace "Aisha lafiya naganki haka?" kanta kawai ta iya nuna masa tana matsalar kwalla, "ayya sannu" yace mata,kana ya huce ɓanɗakin, saida ya yi alwala ya fito sanan yace "ki tashi to kiyi sallah kisha magani zakiji sauki" batare da tayi magana ba tamiƙe, ba addu'a ba Bismillah ta shiga banɗakin, yana kokarin tada Salla yaji ta ƙwalla wani uban ƙara, a guje tafito tana ihun "wayyo Allah na na shiga uku zasu kashe ni, waiyo kaina zai fashe" da Sauri ya riƙeta gani zata fita waje, sosai hankalin shi ya tashi ganin bakon al'amarin da ke shirin samun matar tashi.

Ranar haka suka wuni a gidan tana ihu, ganin abun yafi karfin shi yasa dole yakira hmahaifiyar ta, koda ta tazo tare suke da malami mai rukiyya, dan yafada mata komai ta wayan, malam yana fara karatu ta fara magana cikin ihu da hargagi, tace "malam karka ƙonamu sonta mukeyi" tsagaita karatun malam yayi kana yace, "sonta kuma? Kun taba ganin soyayya sakanin mutom da aljanna?" Sit tayi tana fizge-fizge, "miya kawo ku jikinta"? cewar malam, "wallahi malam sonta muke nishadi take bamu tana rubuta littafin batsa munajin dadin hakan, shiyasa muka yada zango a jikinta, a take akafara kallon kallo sakanin mijinta da mamanta, rubutun batsa kuma to yaushe ma hakan ta faru,suke tambayar kansu a zuciya, kallosu malam yayi yace "gaskiya wannan matsalar babban ne dole a maida ita gidana, inci-gaba da mata magani ko Allah zaisa a dace."

haka suka tattara da mahaifiyar ta suka dunguma gidan malam, suna tafiya mijin ya buɗe wayar ta saƙo ne kala-kala da miss call masu yawa, lambobin babu suna sai guda ɗaya inda yaga ansa sis Fati, inda take tambayar lafiya ta jita shiru, amsa ya bata akan Aisha batada lafiya tana barar addu'a, haka Fatima tabi duk groups ɗin su tace a saka Ummu Nabel a addua batada lafiya. watansu shidda a gidan malam kafin nan tafara samun sauƙi, ta fara sanin wacece ita tare da tambayar ina ɗanta, inda daga nan malam ya kafa mata sharuɗɗa, kuma yace lallai ta kula da ibada da Azkar safe da marece, kana suka baro gidan malam, sosai nadama da tsoron Allah suka shigeta, ta kuma ɗau alwashin gyara kuskuren ta da zaran ta samu lafiya.

Bayan wata takwas, taji sauki sama-sama, domin kowa yasan shafar jinnu, idan sun shiga jikin dan adam basa fita lokaci guda, to a wannan lokacin ne kuma ta ɗaura ɗamarar yin littafin ta mai suna CUTA BA MUTUWA BA amma tana fara rubutun ciwon ya tashi haka aka kwashe sai wajen malam, inda ya tabbatar musu cewa, indai tanason zama lafiya to ta bar tubutun hausa gaba-ɗaya, dole mijin ya amshe wayarta, haka ta hakura da duniyar whatsap masoyanta kuwa babu wadda ta sake bi ta kanta, sai ma kuɗaɗen su dasuka matsa dole mijin yayita maida musu abunsu, babin Ummu Nabel ya shafe a duniyar whatsp kamar bata doniya, Fatema ce kawai bata rabu da ita ba ALHAMDULILLAH...

Post a Comment

Previous Post Next Post