DANA SANI ƘEYA CE
na
shamsiyya abubakar
ummu yasmin page1️⃣
kwance take akan gado hannun ta riƙe da wayar ta kirar infinix hot11 wani littafi ne ya ɗauke mata hankali tayi zurfi sosai cikin karatun tanayi tana matse cinya
ke fauziyya ta jiyo muryar mahaifiyar ta, a firgice ta miƙe tana amsawa' mahaifiyar ta kalle ta cikin takaici tace yanxu ke abunda kikeyi daidai kenan kullum kina nan karance karancen banza da wofi ko aikin ma kin dena tayani
tayi wani far da ido tana kallonta,kiyi hakuri umma me zan miki yanxu, cikin takaici tace tashi kikai min kuɗin adashe na banaso ace naci kuɗi bana zubi to ta amsa tare da miƙewa ta zura hijab ta karɓi kuɗin ta fita
tafiya take a nutse ya tare ta a hanya ta kalle shi tayi murmushi shi ɗin saurayin tane kowa yasan su tare
ya kalle ta yace ina zuwa tace wallahi aike na umma tayi to ko zan raka ki ne? ah ah nagode, shikenan sai nazo anjima Allah yakaimu fa faɗi a takaice sbd ganin shi yana kara sawa ta shiga yanayin da take ji mara daɗi
fauziyya yarinya ce mai tarbiyya amma sakamakon karance karancen littafin batsa yana neman canza akalar rayuwar ta don koda yaushe tunanin ta anya zata iya jurewa bazata ba hashim damar da ya daɗe yana nema a tare da ita ba saidai tsoron ta ɗaya tasan tana kaunar hashim amma ansha kawo korafi kanshi yana neman mata kuma kowa yasani ita kanta tasha ganinshi da mata kala kala kuma da ya mata karya akan yan uwanshi ne saita yarda tana kaunar shi kuma kullum wutar sha awar shi kara ruruwa take a zuciyar ta don shi ɗin cikakken namiji ne wanda babu macen da zata kalle shi bai mata kwarjini ba shiyasa kullum take sha awar shi musamman da take ƴan karance karancen nan so da yawa tasha daga waya don ta sanar dashi ta amince akan kudurin shi sai zuciyar ta ta hanata
koda ta dawo gida sai ta iske kawarta zainab zaune tana jiranta da fara a tace laah yaushe kikazo, zainab ta kalle ta sama da ƙasa tace tun daxu mana ta kama hannun ta suka shiga ciki
wallahi zainab dama inason ganin ki akwai abunda ke damuna kwana biyun nan wani mugun sha awa ke daga min hankali
mtsww tsoki zainab taja ta kalle ta tace dole sha awa ya dameki bakida aiki sai karatun littafin batsa ga littafai nan masu darussa ni bakya ganin irin wanda nake karantawa hankali na kwance ba tashin hankali kuma babu zunubi amma ke bakyaso sai na batsa ke kika sani ai
wayar ta ce ta ɗauki kara tana dubawa taga lambar hashim ne ta kalla tayi shuru kaman bazata daga ba kwanan nan yana yawan damunta akan zasuje duba wata matar abokin shi data haihu
ke ni bari na wuce cewar zainab ta kalli zainab ta ɗauke kai,au yauma babu ko ƴar rakiyar to ai shikenan haka ta miƙe tabar ta wajen tana tunani kala kala ba tun yanxu ba hashim ko hira suke yana yawan son taɓa ta kuma adah bata so amma yanxu abun yana matukar mata daɗi musamman da tafara karance karancen nan,
wanka tayi tayo sallar magrib anata kiraye kirayen isha,i tana idar wa aka aiko hashim na kiranta koda ta fita magiya yake mata akan dan Allah suje ta gaida matar abokin shi
hashim wallahi baza a barni a gida ba kayi haƙuri,haba fauziyya yanxu fa zamu dawo ba wanda zai san ma munje harmu dawo kinji pls baby a take ya narkar mata da zuciya tace to naji na amince amma karmu wuce minti ishirin, yauwa koke fa
motar shi ya buɗe mata ta shiga suka wuce koda sukaje gidan ba kowa tsit yake tuni tafara zare ido tana tunanin anya ba karya ya mata ba ta kalle shi tace to ina mutane gidan yayi dariya irin ta yan bariki yace haba kekuwa ke kullum soyayyar gidadawa kike nuna min shiyasa na miki karyar haka don muzo nan mu more ke sai kace ba wayayya ba murmushi tayi lokacin da ya matso kusa da ita yakai hannu kan nata hannun tuni ta manta da tarbiyyar da aka ɗora ta akai domin dama tayi nisa cikin irin wadannan tunanin tunda ta fara karatun littattafan batsa ba abinda take so illa namiji kusa da ita shiyasa baisha wahalar shawo kanta ba tuni ta bashi haɗin kai
koda komi ya kammala nadama ce cike fal cikin ranta wani mugun tsanar hashim takeji har cikin ranta inda yadinga magiya yana bata hakuri haka suka dawo gida ko kula shi batayi ba tayi shigewarta gida tana tafiya a hankali gudun kar agane tun daga lokacin tadena daga wayar shi ko yazo bata fita
bayan wata uku tafara jin sauye sauye a jikinta wanda bata gane hakan meke nufi ba a take takira kawarta abokiyar shawarar ta suka ɗunguma asibiti gwajin farko likita ya tabbatar mata da tana ɗauke da juna biyu innalillahi tashin hankalin da ta shiga ba a magana kuka take sosai inda zainab keta bata hakuri haka suka dawo gida hankali tashe koda ta sanar ma hashim sai cewa yayi in zata zubar ta turo acct number ya saka mata kuɗi inkuma zata haifa ne zai fara tara na rago kit ya kashe wayar sa
kalman ya mata ciwo amma haka ta danne zuciyar ta ta tura mai saƙon account number din don bazata taɓa bari ta haifi ɗan shege ba a gaban iyayenta haka ya turo kuɗi suka kama hanya ita da zainab hashim ko bin takansu baiyi ba inda yaketa masifa akan daga taɓa ta so ɗaya sai ciki sai kace wata kaza
basu sha wahala ba wajen ganin likita inda suka sharara ma mahaifiyar fauziyya karyan zasuje dubiya asibiti kawarsu ba lafiya, koda likita yakaita ɗakin da za a cire ciki sai duk hankalin ta ya tashi tafara kuka doctor ya kalleta yace ki kwantar da hankalinki lafiya lau za ayi agama just 15minute ma mungama
faɗin azabar da tasha ma ɓata lokaci ne saidai an samu gagarumar matsala inda fauziyya tayi sheme sheme a wajen babu numfashi take likitan yafara salati shidai bai taɓa yin aikin nan ansamu matsala ba amma fa yana ganin kaman yarinyar ta mutu take yaji zufa na keto mishi ta ko ina innalillahi wa inna ilaihirrajiun
a kiɗime, kokarin ceto rayuwar ta yafara yanata jero adduoi Allah cikin ikon sa ta farfaɗo tana numfarfashi allurai ya mata a take barci yayi awon gaba da ita nan ya fito zainab ce ta tare shi tana tambayar shi doctor ya kawata ya kalle ta yayi murmushin wahala yace alhamdulillahi mungama lafiya amma tana barci saita farka anjima sai in bata magunguna ku wuce zainab ta saki numfashi tace to doctor nagode,yasa kai yafice yana nazari sosai aran shi tabbas dole ya ɗauki shawaran yayan shi akan dena harkar nan ta cire ciki kar wataran ya shiga uku
awa biyu ta kwashe tana barcin wahala kafin ta farka aka basu magani koda suka dawo gida mahaifiyar ta ta tambaye su ya taga fauziyya wani iri take sukace mota ce ta bige ta amma me motan yakai su asibiti an bata magunguna nandai mahaifiyar ta jajanta amma ƙarƙashin zuciyar ta zarginsu takeyi
haka fauziyya ta cigaba da jinya a haka har aka saka ranar auren zainab da wani saurayinta abdallah haka rayuwa ta cigaba kullum fauziyya ba lafiya ga hashim gabadaya ya fita batun ta kota kira baya ɗauka a haka har tasamu wani saurayi mai suna jamilu saidai anayin aure inda ta fara samun matsala da yajita ba cikakkar budurwa ba sannan kullum ciwo kara gaba yakeyi
kwance take akan kujera 3sitta duk jikinta ba daɗi ga mugun ciwon mara da yake yawan matsa mata tun bayan cire ciki da tayi yaudai ya matsa lallai saiya kaita asibiti haka ko akayi suna zuwa likita ya kalle ta yayi mata gwaje gwaje
a take gabanta yafara faduwa yace mata gaskiya kinsamu matsala da mahaifar ki bazaki taɓa haihuwa ba sai wani ikon Allah innalillahi wa inna ilaihir rajiun abunda ke fita daga bakinta kenan wani jiri ke kwasan ta haka suka dawo gida yanata zafga mata masifa nan ya fice yabarta tana kuka
kullum mahaifiyar ta nasihar da take mata kenan kiji tsoron Allah fauziyya ki riƙe mutumcin kanki ki riƙe maraicin ki amma ina ta biyewa sha awar karatun batsa gashinan abunda yaja mata ta share wasu hawaye masu ɗumi na danasani
haka mai gidanta jamilu yace bazai zauna da juya ba inda ya auri yar uwarsa nafisa, nafisa na girmama fauziyya sam batada matsala a haka harta haifi ƴarta mace tasa mata suna fauziyya kuma ta bata ita kyauta kasancewar ita bazata haihu ba haka jamilu yacigaba da basu kulawa don yana matuƙar jin tausayin rayuwar da fauziyya ta jefa kanta. ALHAMDULILLAH..
Post a Comment