Bakar Rana Hausa Novels Na Fateemah Shu'aibu Abdullahi (Bushra)

 *BAK'AR RANA*



                 

               *NA*

*FATEEMAH SHU'AIBU ABDULLAHI*

               ( Bushrah )




*PROFICIENT WRITER ASSOCIATION*



 Saurayi ne ajin farko mai k'asaita da isa duk inda ya waiga k'amshin da ke tashi jikinsa sai yasa an kalleshi,,da taƙama ya ke tun karan hanyar gidan wata dattijuwa da ke cikin wani ɗan lungu,yara ne ke ta faman masa oyoyo sa sakamakon yarda yake k'yautata masu.

Hanyarsa ta shiga gidan wani dogon lungu ne kafin ya kai ka farfajiyar gidan kalmar "innalillahi Wa innah ilaihir raji'un.......!".Take fita daga bakinsa sakamakon nishi da sabbatun da ke fita daga tagar wani ɗaki,cikin wani irin razana wanda ya kawar masa da hankalinsa ya ma mance gidan su waye ya shigo,bai ko kalli wanda ke zaune afalon ba,ƙoƙarinsa kawai ya kai ga inda yake jin wannan nishi.Su Innah Laraba ne ke kallon ikon Allah,,wanda tayi kwance abunta kai da ka ganta kasan bariki ya zauna mata ajikinta,,babbar waya ce ahannun ta tana latsawa sauran 'yan matan suma suna latsa nasu.

Wannan na kutsa jiki wannan man tusa hannunta cikin hijabinta,,ita kuwa Innah Laraba shewa take tana sunbuɗa ma wata marubuciya albarka,wai ita adole tana goyon bayan mai rubutun batsa.

Wani shafi ne gabanta da ya d'auki dukkan salon baitikan ciki da asalin yarda ake ma'amula da mata da maza take duba wa,bud'ar bakinta keda wuya sai faɗin"Yasmeen zo ki ga wani sabon salo tabbas yau gayena za ya ɗauki sabon salona..".Murmushi Yasmeen tayi ta amshi wayar Innah Laraba tana turawa anata wayar tayi murmushi tayi d'akinta abunta.

A razane ya tura ƙofar wanda tuni sunyi nisa basa jin kira bare kuma ya tabbatar da su waye akwance kuma mai suke aikatawa domin kuwa duhun ɗakin yayi yawa.



Inna Laraba ce ta ankare ta tuna da cewa yau fa Afrah tana da baƙuwa babbar aminiyarta tun daga jihar Sokoto,,sai alokachin ta tuna da cewar ta ga wucewar Saleem ko magana bai masu ba,,tambayar kanta take mike faruwa ne kuma miye silan da yasa Saleem ya mata abunda bai tab'a yi ba..?

A'isha da take gefen dama saman sallaya tana ta bitar alƙur'ani,tana kallon ikon Allah.

Da saurin ta nufi inda makunni wutar ɗakin take,ƙoƙarin kunnawa take yi sai Allah ya haneta.


Cikin fushi da zafin rai Shaheed ya ciro wayarsa ya haska haskenta daidai saitin da suke suna nishi ba ma su san duniyar da ake ciki ba.Ihun Innah Laraba ta saka,tayi kansu kamar mahaukaciya tana duba Afrah da k'awarta,gaba d'ayansu haihuwar uwarsu suna ta nishi suna jan zanin gadon ɗakin sun gama fita hayyacinsu,,k'aran karatun ne ke tashi na wani karatun littafin batsa da ake yaɗashi abisa faifan yanar gizon zumunta wanda sai da kuɗi za ka shiga ka saurara,,sun kunna suna ji suna aika baɗalansu.!

Shaheed da atake yaji wani irin takaici mai ratsa dukkan jikinsa,afusace yayi kan Afrah da wani mahaukacin mari,wanda sanadin marin yasa jini ya fara tsiyaya ahancinta,,jayo Nauwara k'awarta yayi ya fara ƙwallo da ita yana faɗin"wallahi na kuma ganin 'ƴan iskan k'afarki cikin gidanan wallahi sai nayi sanadin rabaki da ƙafafunki,,irin kune masu rusa tarbiyyar da iyaye suka jima suna gina ma yaransu,har gidanku sai na shigo na gaya masu iskanci da kike yi shiyasa kullum kinan manne da ita..!".

Duk da Nauwara tasha wuyan dukan da yayi mata bakinta bai rufe ba,bata fasa magana ba, "Malam ka daina aibanta mani tarbiyya idan da wanda ya lalatamu ai bai wucce Innah ba,dan kuwa itace kamfanin duk wani littafin batsa,babu k'afar yanar gizon da bata sani ba,k'arshe ma har rubutawa itama tanayi da kanta,,in dai ka ganta afalo rik'e da waya.".Tana dariya ta cigaba da cewar"toh abinda take aikatawa kenna,kullum sai ta rink'a nuna mana wai an waye yanzu,gara musan hakan tun kafin muyi aure mun goge kenan".

Salati da sallallami Innah Laraba ta fara hankalinta atashe cikin kad'uwa tace"ni za ki jama sharri ƴar nan duk barikancina da tukaranci na ai bana koyawa nawa wannan lalatan ba..!".

Halima da ke tsaye tana sauraransu ta ƙaraso,cikin murmushi ta tace,"Innah Laraba kiji tsoron Allah,ko yanzu sai da kika gwada mani wannan shafin da kika saki,kawai ni dai Allah yasa nayi hankali ba kamarsu ba shiyasa nakan kai hankalina nesa sosai dan karda na fad'a halaka na ɓata tarbiyyata,,A'isha wadda kika tsana kike jifarta da bin maza gashi ita kuma sai Allah ya kimtsata,wayar ma bata ko ƙaunar mai dangwalawa ta fison k'arama tana wasanta da ita tana game na d'an maciji ,babu wanda bana ankare dashi acikin ko,daman nasan wannan ranar zata iya zuwa,,Shaheed wlh koda auri Afrah sai dai ka auri sauran wani dan kuwa banga lugun da basa shiga ba,haka kuma banga kalan iskancin da ba suyi ita da Zulai ba,,har kamasu nayi,naja masu kunne sosai da sosai amman hakan sai ya zamana izgilanci gareni,daga nan nasa musu ido saboda kana matsa masu Innah zata hauka da faɗa ita ga mai jikoki..!".

Abun yayi masifar d'aure masa kai sosai,ganin bai taɓa ankara da hakan ba,sai da yanzu yana tunano wasu abubuwan daga Afrah,wanda take son ta rink'a kama masa hannu da nuna wasu abubuwan idan ya zo gurinta..

"Tir da wannan mugun halin naki Laraba wallahi wallahi na fasa auren wannan jikartaki,wacchan wadda kika maida bora mara kima itace matata da ikon Allah,kuma acikin satinan za'ayi komi zan ɗauketa gaba d'aya daga ƙasar mu koma Ingila da zama,babu ita ba ku zan zame mata gatan duniya na share mata hawayen maraici,ɗiyar kishiya ai inda arziki ɗiyarki ce,,ke ɗiyar taki ɗaya da ta rasu tabarki da jikarki ga haƙƙin abunda kika aikata nan ya koma maki tun baki yi nisa ba,yara ƙanana duka shekara sha biyar amma sun fantsare gaba ɗaya,wallahi tir da mata masu irin halinki,yanzu kinga sai ki d'aukesu ki koma chan saudiyyar ku dasa alak'ar iskancin daga inda kika tsaya..".

Rufe bakinsa keda wuya muryan mahaifiyar Zulai ta fara "Aini wallahi tallahi billahil azim kotu ce zata rabani da Laraba,dan babu abinda ban ji ba,yanzu haka Zulai duk tabi yaran maƙotana tana b'atawa ƙananan yara gasunan anzo turkeni an kamasu alungu suna fadin Zulai ce,,wallahi Laraba yau hukuma ce zata mana iyaka dake..!".

Sallama suka ji daga waje wanda A'isha ta fita dan ganin mai sallama,bazawarin Laraba ne ɗauke da takarda ahannunsa.

A'isha tayi masa iso cikin gidan dan tasan ya saba shigowa,,k'walla na tsiyaya a idonsa yana faɗin 

"Allah ya isa tsakanina da ke Laraba,kin cuceni kin cuci iyalina kin cuci yarana!!!Ashe kina ɗauke da ƙwayar cuta baki sanar dani ba!!?Kin yaudareni ta salo da kissa sai da kika sa nayi mu'amula dana sani dake,,toni ba zan kaiki ƙara ba,amman na kaiki ƙara gurin mahaliccina,ban taɓa aikata zina ba sai sanadin haɗuwata dake..!".



Ya fice daga gidan Shaheed ya banka mata wata irin muguwar harara,ya umarci da halima ta haɗa kayanta da na A'isha zaya maidasu gaban iyayenshi da sa hannun limanin unguwa da wasu manyan unguwa.

Inna Laraba da Afrah ban da kuka da dana sanin abunda suka aikata babu abinda sukeyi sai rusar kukan bak'in ciki da nadamar rayuwa,gaba ɗaya Afrah taji wani tsanar Innah Laraba ya mamaye zuciyarta,ta sofko ta fara jifarta da kalmar Allah ya isa,tana had'a kayanta dan barin gidan idanuwanta duk sunyi jajir akan kukan takaici kuma sun kumbura cewa take"Kin cuceni Innah kin gama mani da rayuwata.!Ke kika kawo mahaifiyata duniya amman yanzu kinyi sanadin barin ɗiyarta cikin mugun hali saboda halinki na son zuciya da tsabar bama waya muhimmanci shiyasa duk inda babbar waya take baki bari dole kike nemanta ki siya nima kuma ki bani,,yanzu kinga nayi sabo da abunda ba zan iya fasawa ba,,zan koma gidan karuwai na k'arasa sauran zamana anan..!".Afrah ta k'arasa fad'a hawayen k'unci suna zirara a k'yak'k'yawar fuskarta.



Sallamar 'yan sanda ne mota guda a k'ofar gidan suka kwashi Innah Laraba ba sai ofishinsu.



Afra na fadin "Allah ya k'ara kad'an kenan kika gani sai ma an kamo sauran marubutan batsan tukunan zaku ƙara gane illar abunda kuke rubutawa..".


Tausayi sosai Afrah ta bama mahaifiyar Zulaiha ta kamota tace "Afrah kema d'iya ce kamar kowa,kuma nasan sanadin shak'uwa da wannan waya ya k'ara baki damar shiga wannann yanayin ba zan barki kije gidan karuwai ba,amman insha Allahu zan mai dake gidan babban yayana babban limami ne dake nasarawa,rayuwarki gaba ɗaya zata koma chan kafin na sasanta da dangin mahaifinki kinji 'yar albarka,,ki je ki zauna da asuba za kibi motar farko insha Allahu ke da Zubairu ya ya maki jagora"..



Kuka sosai Afrah takeyi tana godiya tana kuma k'ara nadamar abunda ta aikata da Zulaiha gashi yanzu mahaifiyarta ce tayi mata rana..



Laraba kuwa tasha duka ko'ina jikinta a kumbure tana faɗin "yallab'ai wallahi na jima ina rubutun nan sai na sauya suna dan karda su gane nice keyinsa,nayi littafi babu adadi kuma hatta na karatun rekodin ɗin shima inayi ina amfani da wani abun dan na sauya muryata,,tabbas yau naga illah abunda na rubuta ganin idona tunda gashi jikata da kanta ta tsine mani albarka tayi kuma tir da halina na kuma jefata cikin mawuyacin hali..!Aganina da tunani ta sanadin rubutun batsa zamuyi arzik'i da ita"...


_ALHAMDULILLAHI._

Post a Comment

Previous Post Next Post