Abinda Na Shuka Hausa Novels Na Aysha Alhassan Dan Fulani




 ABIN DA KA SHUKA...





PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


The ability to guide is what all writer can have,we proficient writer will share this quality.





Aysha Adam Alhassan dan Fulani



Gajeren Labarin



  Numfashina na shiga kokawar ja da ƙyar, saboda yadda ya ke ƙoƙarin barazanar barin jikina, hawaye masu ɗumi suka fara kwaranya a kwarmin idona kamar an buɗe indararo.

   Kalaman ƙawata Wasila suka shiga amsa amo a kunnuwana kamar a yanzu take mini su 'Duk abin da za ki yi a rayuwa ki tabbatar kin yi mai kyau da inganci. Ina tsoron kada watarana ki ɗauki wuƙa ki daɓawa cikin ki. Kada kuma saƙon da kike aikawa ya dawo zuwa gare ki.'

   A lokacin ban ɗauka maganarta zata iya zama gaskiya ba, domin ina sahun mutanen da suke tunanin ƙoƙarin su zai sa su kare kan su, kamar dai yadda na zama ɗaya daga cikin mutanen da suke cewa idan jifa ya tsallake kan su to ya faɗa kan uban kowa.

  

  Na ƙara fashewa da kuka mai yawa ina girgiza kaina "Kaicona! Kaicon wannan rayuwar tawa!"

    "Ki daina ɓata hawayen ki a banza, indai kuka ne yanzu kika fara yinsa, ki gama anan, kuma ki jira abin da za ki tarar a ranar gobe. Domin Allah kaɗai yasan yaran da kika zama silar lalacewar rayuwar su. Yanzu ki jure wannan zafin na duniya ne. Ga wannan kuma takardar ki ce, na sake ki saki uku. Ba zan iya zama da macen da ta zama silar lalacewar rayuwar 'yata ba." Kalaman mijina suka zama kamar sauƙar mashi a ƙahon zuciyata, abin da ya faru da ni ya zama kamar sharar fage ne a kan abin da ya aikata mini.

  Ashe kuskure nake ta yi? Ashe ban sani ba na daɗe da kashe rayuwata wajen neman birge mutane da son nema yi musu gwaninta.

   Wasu hawaye masu ɗumi suka sake sauƙa a idona a lokacin da na ga mijina da na shafe tsawon shekaru ashirin tare da shi ya ja ƙofa ya fita ya bar ni, fitar da take nuna mini cewar ya fita a rayuwata har abada kenan, ban kuma iya tsayawa na dakatar da shi ba saboda nauyin haɗa ido da shi ma nake ji.

   A lokacin faɗan iyayena ya sake dira a kunnuwana suna tirr da Ala wadai da ɗabi'ar da ta zama shamakin raba igiyar aurena da mijina.

  A lokacin na ji inama dai ace mutuwa ce ta ɗauke ni, inama ace a lokacin da na yi mummunan gani numfashina ya bar gangar jikina. To amma idan na mutu a irin wannan lokacin na ce wa Ubangijina me? Me na samu a duniyar me kuma na tara na fuskantar sa? 

   Wani magiji mai ƙarfi ya haska a idanuwana inda ya dawo mini da jiya zuwa yau, rayuwata ta jiya ta ci gaba da haskawa a cikin idanuwana a lokacin da gangar sheɗan ke kaɗa mini shi da mabiyansa ina musu rawa.


***

 Sunana Hassana Adamu Hussaini, tun ina matashiya nake karance-karancen litattafan Hausa, har zuwa lokacin da na yi aure da mijina Abdullahi, yakan kawo mini su ina karantawa litattafai ne masu ɗauke da darasi da wayarwa da mutane hankali a kan zamantakewar rayuwa. 

  Har zuwa lokacin da na haifi yarana guda huɗu, Zulfa'u ita ce ɗiyata ta farko wadda nake matuƙar so da ƙaunarta, sai ƙannenta uku maza. Kasancewarta mace na ɗauki ƙauna da kulawa na ɗora a kanta.

  A lokacin zamani ya ci gaba da sauyawa har zuwa lokacin da rubutu ya koma a waya, marubuta da dama suka fara sharafinsu a yanar gizo, a lokacin na ji nima ya kamata na zama marubuciya, sai na fara rubutu mai kyau, sai dai kururuwar mabiyana da yadda suke zuga ni a kan na zuba gishiri da magi a kan rubutuna ya sa na karkata akalar alƙalamina daga neman mutuntaka zuwa neman ɗaukaka.

  Kafin wani lokaci sunana ya fara yaɗuwa a media, har zuwa lokacin da na fara wani shahararren littafina mai suna Manyan Mata. Wanda ya kasance tsagaren lasbiyan na ke nunawa, kuma hakan ya samo asali ne da fina-finan banzan da nake sauƙewa duk saboda kururuwar mabiyana da son birgesu.

  Zan iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu a lokacin, domin dubu ɗai-ɗai nake siyar da littafin, wasu kuwa masu son zama a zaure na musamman har dubu uku suke biya nake tura musu sau uku a rana.

   Labarina ya jijjiga duniyar sama, ko na ce yanar gizo, domin na samu mabiya ba adadi, gefe guda kuma na samu masu zagina da masu yi mini nasiha a kan na ji tsoron Allah. Ƙawata Wasila na ɗaya daga cikin mutane masu mini nasiha amma na kawar da batunta gefe kamar yadda na fara zagin masu zuwa mini wa'azi, mabiyana na zuga ni da cewa hassada suke mini.

   Kwatsam tafiya ta kama mu ni da mijina, na bar ɗiyata Zulfa'u 'yar shekaru goma sha takwas a gida ita da ƙannenta saboda suna jarabawa a makaranta, mu kuma biki ake a dangin Abbanta.

  Tafiya ce ta kwanaki biyu za mu yi ta, na jaddada musu a kan kula da gidan ita da mai aikinmu Uwale, na ga farinciki kwance a fuskokinsu ban ga damuwa ba kamar yadda Zulfa'u take yi a wasu lokutan.

    Haka muka tafi cike da alhinin rabuwa da yarana, a kwana guda da tafiyarmu kiran Zulfa'u ya shigo wayata, ina ɗauka ta fara tambayata yaushe za mu dawo duk da sanin na sheda mata kwana biyu za mu yi, kamar zan amsa mata a gobe sai kuma wani sashi na zuciyata ya hanani na ce mata zan kirata idan za mu taso, na ji murnarta da walwalarta a lokacin.

  Tunanina ya kasu da yawa na neman dalilin farincikinta da rashin zuwana kamar dai yadda nake neman me ya mantar da ita da ranar dawowar mu.

  

  Washegari ban sanar da ita muna hanya ba, amma tun da muka ɗauki hanya na ke jin gabana na ta bugawa da ƙarfi, na yi ta ambaton 'Inna lillahi wa inna ilahairraji'un!' Sau ba adadi a zuciyata, amma ban daina jin abin da nake ji ba, har zuwa lokacin da muka yiwa gidanmu tsinkaye muka dira da dirawa irin ta masu iko a kan sa, shigar rashin neman a ba da izini kafin a shiga.

   Ƙirjina ya buga da ƙarfi na ji kamar an sa majanyi an jani baya ƙafafuwana suka sandare duk saboda mugun ganin da na yi a falon gidana.

   Ɗiyata Zulfa'u ce tsirara mata kusan shida sun yanyameta kamar za su cinyeta a ciki har da Uwale mai aikina.

   Na buga ƙara da ƙarfi ina nanata kalmar "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un!" Da ƙarfi amma kamar ba su duniyar da za su ji mu.

  Ganin halin da nake ciki Abdullahi ya ƙaraso, abin da ya yi tozali da shi ya sa shi yin bayana yana ambatan "Subhanallahi! A'uzubillah!" Yana rintse idanuwansa da ƙarfi.

  Na yi kukun kura na ɗauki taɓarya na shiga jibgar matan da ke cinye ɗiyata, nan take suka dawo hayacinsu suka fara wawurar tufafinsu, na musu duka lilis kamar zan kashe su, anan na cakumi wuyan Zulfa'u kamar zan kai ta lahira.

   Da ƙyar Abdullahi ya ɓanɓareta a lokacin ta fashe da kuka ta na maida numfashi.

   Bayan shuɗewar mintuna ashirin gidan ya rage daga ni da mijina sai Zulfa'u da Uwale, Abdullahi ya kalle ci cike da takaici "Wa ya koya muku wannan abin?"

  Anan suka yi shiru, har na zabura na sake rarumar waya sai na ji maganar Zulfa'u "A gurin momy muka koya wallahi, littafin da take rubutawa nima ina cikin group ɗin da ta buɗe, na sauya suna zuwa Mom preety." Wayar da ke hannuna ta sulluɓe ta faɗi ƙasa na zauna daɓas a ƙasa kamar mutum-mutumi.

   "Yi mini bayani yadda zan gane." Abdullahi ya sake buƙata.

    "Wayar momy na ɗauka naga rubutun da take na fara karantawa, shine na ji ina son jin ƙarshen, daga bisani na siyo kati na tura mata ta whtspp bayan na sauya sunana nace ina son littafin. Tun da na fara karantawa hankalina yake tashi, har nake son na ga yadda ake yi a zahiri watarana na ari wayarta anan naga bidiyon lalatar na tura a wayata, sanadin haka hankalina ya sake tashi har na tashi Uwale na gwada mata, daga nan muka fara yi."

   "To sauran fa?" Ya sake tambaya.

"A makaranta ne abin ya ciyo ni bayan karanta littafin nata, shine na je hostel nake yi da kaina, har ƙawata Zuby taga haka, ashe itama ta karanta littafin momy shine muka fara yi da ita, koda nace zan kwana a makaranta saboda jarrabawa ƙarya ne, da ƙawayenta ta haɗa ni suma 'yan lesbiyan ne. Shine fa muka jone tare."

    Maganarta ta ƙare a lokacin da numfashina ya ɗauke cak.

  

***

  Ban sake sanin abin da ya faru ba sai a yanzu da na ga mijina da takardar sakinsa, da kuma fita a rayuwata gaba ɗaya.

   Lallai gaskiyar 'yan magana Abin da ka shuka shi za ka girba. Ina tunanin zan lalata yaran wasu ashe har nawa na lalata, yanzu wa gari ya waya? Babu aure babu mutunci babu kima, ga na rasa yarana. Na ƙara fashewa da kuka da danasani wanda na san ba ta da amfani.


  Ƙarshe.

Post a Comment

Previous Post Next Post