Yadda Ake Magance Warin Kashi Ko Kuma Warin Jiki


 Maganin Warin Jiki Ko Kuma Warin Kashi. Yadda Zan Magance Warin Ƙashi.


Da akwai mutane ma su fama da irin wannan matsalar, wasu cuta ne wasu kuma ƙazamta ne. Budurwa ta Cikakkiya yar kwalisa yar boko amma tana fama da wannan warin. Wata kuma matar aure ce amma saboda Warin Kashi sai mijinta ya kyamaceta ya daina kulata wanda duk wannan yana faruwa ne saboda rashin kulawa da tsaftar jiki ko kuma rashin lafiya.

Wata Sabuwar Garabasar MTN Mai Suna MTN Pulse Points. Suna Bada Kyautar Data Mai Yawan Gaske

Danna NAN Domin Karantawa 


Kamar dai yadda yake nau'i biyu ne na tsafta da na cuta. A matsayinki na cikakkiyar macce ba sai an fada miki ki yi tsaftar jikinki ba domin magance wannan matsalar na warin jiki, amma warin jiki nau'in ciwo yana da kyau ki tashi tsaye neman magani. To Insha Allahu ki jarraba wannan da zamu kawo miki domin magance wannan matsalar ta warin kashi ko kuma mu ce warin jiki.


Ki fara tafasa ruwan zafi sannan ki zuba garin magarya kadan kimanin cokali biyu a cikin ruwan da Kafra daya sai kuma Kanunfari a ruwan zafi sai a tace ana wanka da shi tunda safe har zuwa yamma kowane lokaci yakasance ana wanka dashi. A wurin wankan a kiyaye duk wani sassa wanda ke iya fitar da wari a gyara da kyau. Gashin hammata kuwa a dinga tsigewa kamar yadda addini ya tanadar. Bayan an gama wanka a kiyaye da turare masu kamshi Insha Allahu da wannan za a kammala duk wani matsalar warin jiki.


Post a Comment

Previous Post Next Post