Sabuwar Garabasar MTN Pulse Points 2022

 

Wata Sabuwar Hanyar More Kyautar Mtn Mai Suna MTN Pulse.


Wannan wata kyauta ce da mtn su ke bayarwa ga duk wani mai aiki da plan ɗin su na MTN Pulse. 


Kamar yadda kowa ya sani yanzu siyar da data ya zama wani ruwan dare wanda a kodayaushe mutane suna cire kudinsu su siya. A madadin kudin da kuke kashewa wurin siyen data MTN sun fito da wata sabuwar hanya wacce idan ka loda katin zaka samu kyautar data da su kuma ka yi kiran waya dasu. Tayaya. A duk lokacin da mutun ya loda kati to zai samu kyautar Pulse Points Wanda da shi zaka yi data kuma katin da ka loda na nan, amma fa wannan kyautar ta kamfanin MTN ne kawai kuma wanda yake cikin MTN kawai zai samu wannan kyautar.


Yadda Zan Koma Tsarin MTN Pulse.

Domin shiga tsarin MTN Pulse ka danna *406* sai ka yi reply da 1. Da zarar sun baka damar shika MTN Pulse to yanzu kuma sai more kyautar Pulse Points. 


A duk lokacin da ka loda kati kuma ka yi kira da su to zasu baka kyautar Pulse Points Wanda zaka iya siyan kowacce irin data da su. 


Yadda Zan Duba Ko Na Samu Points

Domin sanin ko ka samu Pulse Points ka danna *406*7# sai ka yi reply da 4.



Idan ka ga ka samu Points da yawa sai kawai ka sai yi data da abinka. 


Tayaya Zan Samu Kyautar Mtn Pulse? 

Wannan tambaya ce da wasu masu amfani da MTN su ke yi, to ga hanya mafi sauki.

Ita dai da da MTN Pulse Points ana samunta ne idan a ka loda kati kuma akayi kira da katin da aka loda. 



Idan ka bincika wayar yan uwanka ko abokanka kaga suna da Points zaka iya siyan data da su a sai ka tura kanka amma fa tare da iznin su. 


Yadda Zan Turawa Data Ga Layina.


Ka danna *131*7# sai ka yi reply da 1.




Post a Comment

Previous Post Next Post