Amfanin Tafarnuwa A Jikin Matanmu Guda Bakwai

 





AMFANIN MAN TAFARNUWA A JIKIN MATANMU GUDA GOMA


Tafarnuwa tana daga cikin Tsirrai mafiya amfani waɗanda duniya ta daɗe tana amfana dasu. Tana daga cikin abincin masu daɗi a ƙasar Hausawa.


Annabi (S. A. W) ya tabbatar da cewa tana da amfani sai dai ba ya cinta saboda dalilin warin da take dashi.


Wata rana da aka bashi kyautar wani abinci wanda aka hada shi da tafarnuwa, bai ci ba, amma ya aika da abincin a  wajen Abu Ayyub Al-Ansariy (R. A).


Sai Abu Ayyub ya ce "Ya Rasulallahi kai baka son ta, amma ka aiko min, me ya sa?". Sai Manzon Allah (sallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "NI INA GANAWA DA WANDA KAI BAKA GANAWA DASHI". (Wanda shi yana ganawa da Mala'ika Jibriu ne, su kuma Mala'iku basu son duk wani abu mai wari).



Karanta Littafin 

YAR KWANGILA 

Na Mubarak A Kamba 

Page 26 To 30 


Danna nan domin ci gaba da karantawa


Ga wasu daga cikin amfaninta waɗanda masana da masu bincike su ka tabbatar;

CIWON HANTA :

Tafarnuwa tana ba wa hantar 'Dan Adam kariya daga chutattuka. Kuma amfani da ita yana hana kitsen nan na cholesterol taruwa ko ginuwa ajikin hanta, ballantana har a samu matsalar ciwon ciki ko Kumburin Hanta. Masu ciwon hanta su rika shan man tafarnuwa ko garinta wanda aka chakuda da zuma. In sha Allahu Za'a ga abun mamaki wato samun lafiya cikin Qankanin lokaci.


 BASIR: 

Duk wanda ciwo basir yake damunsa, ko yana shan wahala wajen fitar bayan gida, ko kuma masu yin bayan gida da jini, ko masu fama da Kumburin ciki, ko Kaikayin dubura, wannan  albishir ne gareku, sai ku ce dani horo to kafin kuce goron ma gashi, kawai kaje ka samo tafarnuwarka mai kyau. (kamar guda biyu ko uku manya) Ka cire bawon sannan ka bayar a daka maka Fura da ita. Ka samu nono mai kyau kasha wannan furar dashi.. In sha Allahu a wannan ranar ko washegari duk zaka fitar da basir din dake cikinka. Kuma zaka samu lafiya da izinin Allah. Sannan ka rika gauraya Man Tafarnuwar tare da zuma kana sha kullum da safe. In sha Allahu kai da basir kunyi sallama.

 SANYI KO KUMBURIN JIKI:

 Duk mutumin da sanyi ya kumburashi, ko kuma sanyin ya ratsashi, kullum hancinsa ba ya rabuwa da majina, shima ga albishir, ka nemo ganyen Na'a-Na'a ka dafa tare da citta. Sannan ka zuba Man tafarnuwa cokali guda aciki. Ka sanya zuma sannan kasha. Haka zaka rikayi har sati ɗaya haka zuwa kwanaki goma 10. Kuma kana shafa man tafarnuwar ajikinka In Allah ya yarda jikinka zai sabe, sanyin zai fita, kuma zaka samu waraka.

 SANYIN QASHI: 


Yadda Zaki Karawa Kanki Ni'ima Domin Gamsar Da Maigida


Danna nan domin ci gaba da karantawa 

 Masu fama da sanyin ƙashi ko kuma Riƙewar gaɓoɓi (Arthritis) ga naku, Ku samo Man tafarnuwa mai kyau, ku gaurayashi da Man Habbatus sauda, Sannaan a dorashi bisa wuta mai ci a hanakali. Idan yayi kamar minti biyar sai a sauke. Wannan man mai dumi Za'a rika shafawa ajikin ƙafar, ko bayan, ko kwankwaso, ko ƙafar da take ciwon. In sha Allahu ko da ciwon bayan yafi shekara goma ana fama, to za'a samu lafiya da izinin Allah.

HAWAN JINI DA CIWON ZUCIYA: 

 Bincike ya tabbatar da cewa tafarnuwa tana narkar da mummunan kitsen nan na Cholesterol wanda shine yake toshe Kofofin zuciyar Dan Adam, har ake samun hawan jini ko ciwon zuciya. To tafarnuwa tana narkar dashi kuma tana bude duk hanyoyin da suka toshe. Sannan tana tsaftace jinin jikin Dan Adam. Ana so masu fama da hawan jini suyi wannan hadin domin samun kuzari da lafiya. A samo ganyen Zogale danye a dafashi tare da tafarnuwa. Bayan an taceshi kafin asha sai a sanya Man Zaitun cokali guda, asanya zuma sannan asha. Kuma ayawaita cinta a cikin abinci yau da kullum. In sha Allahu za'a dace. 

TYPHOID FEVER (ZAZZABIN HANJI) DA KUMA ULCER:

 Duk masu fama da wannan larurar ga magani nan da yardar Allah,  Ka rika shan cokali guda na tafarnuwa gauraye da zuma kullum da safe, minti 30 kafin breakfast In sha Allahu wannan zai kashe duk kwayoyin chutar dake cikin cikinka. Hakanan masu macijin ciki ko Tsutsar ciki su ma tsutsotsin zasu mutu. Kuma zasu fita da izinin Allah. Su ma masu fama da gyambon ciki (Ulcer) su ma zasu samu saukinta idan suka bi wannan hanyar. Kuma su rika sanya cokali guda na man tafarnuwar a cikin dukkan abincin da zasu ci. Ko kuma arika dafa abincin tare da ita.


CIWON DAJI (CANCER); 

 Duk mutumin da yake fama da ciwon daji ya yawaita amfani da tafarnuwa. In sha Allahu zai samu waraka. Idan kuma ciwon Cancer din akan fatar jikinsa ne, sai ya rika shafawa ajikinsa bayan yasha cokali guda tare da zuma. Idan kuma Sankaran mama ne (Breast Cancer) wanda Mata suke fama dashi, to duk matar da take fama da wannan ciwon ta rika yawan yin girki da tafarnuwa (kamar Jollof rice, ko Pepper Soup, da sauransu). Sannan ta rika shan tafarnuwar wacce aka gauraya tare da Man habbah, kuma tana shafawa ajikin Maman. In sha Allahu zata  samu waraka

Gargajiya Arewa  Tv 

Post a Comment

Previous Post Next Post