Amfanin Habbatus Sauda Wanda Yakamata Matan Aure Su Sani

 



Amfanin Habbatus Sauda Wanda Yakamata Matan Aure Su Sani. 

Duk wata mace mai neman magungunan mata domin karawa kanta ilmi da lafiya ta san cewa Habbatus Sauda tana da matukar amfani ko da bata san amfanin nata ba. To Yau dai bayanin ya zo ne akan Habbatus sauda.


Habbatus Sauda ta na da sunaye daban-daban daga turanci da yaren larabci har da na Hausa. Turawa na kiranta da suna, "The Blessed Seed." Wato kwaya mai albarka. Yayin da Larabawa ke kiranta da suna, "Habbatul Baraka." Da yarenmu na Hausa kuma mu ka kirata da suna Habbatus Sauda. 


Kamar yadda yake kafin kowane ciwo kafin saukarsa Allah S W A ya saukar da maganinsa, Habbatus Sauda na daga cikin maganin cututtuka da dama wanda daga ciki za mu lissafo wasu. 

Amfanin Habbatus Sauda Sun Hada Da; 


1. Maganin Ciwon Kai. Habbatus Sauda tana maganin ciwon kai sosai da sosai har kusan ma za ta iya fin kowane maganin ciwon kai. Yadda ake amfani da ita domin samun warakar ciwon kai, shi ne; A Samu Habbatus Sauda sai a haɗa da ruwan Kal ana sha akai akai wani lokaci kuma ana digawa a hanci, Insha Allahu komai zai zo da sauki sosai. 

2. Maganin Tsutsar Ciki. A damu Habbatus Sauda a haɗa da ruwan Kal ana sha kamar nuna ciwon kai, shi ma zai yi maganin ciwon Tsutsar Ciki. 


3. Kara Karfin Garkuwar Jikin Dan Adam. Masana ilmin Habbatus Sauda sun bayyana cewa mai yawan amfani da Habbatus Sauda zai kasance mutun mai karfin garkuwar jiki. 


4 Rashin Lafiya Akai - Akai. Wanda ya ke yawan ciwo idan ya samu Habbatus Sauda ya haɗa da ruwan madara yana sha kullum a kowace safiya cokali uku, Insha Allahu zai samu waraka. 

https://www.arewacinnaija.com.ng/2022/08/yar-kwangila-page-26-to-30-by-mubarak.html

5. Mai Fama Da Gyambon Ciki (Ulcer) idan ya samu garin Hulba da garin Habbatus Sauda da kuma Zuma ya hade su wuri ɗaya ya gauraye yana sha akan lokacin cin abinci zai samu waraka da yardar Allah. 


6. Tsakuwar Koda Ko Mafitsara. Ana amfanin Da Habbatus sauda da kuma Zuma maras hadi a zuba ruwan zafi a ciki ana sha, duk mai irin wannan cutar da yardar Allah zai samu sauƙi sosai.


7. Maganin Asma. Habbatus Sauda tana maganin Asma sosai. Yadda ake wannan haɗin shi ne a samu man Habbatus Sauda a na digawa a cikin ruwan shayi ko ruwan zafi adadin shekarun maras lafiya adadin digon man Habbatus sauda, da yardar Allah za a samu waraka. 


8. Maganin Zubar Gashi. Wasu matan na fama da lalurar zubewar gashi. Masu fama da wannan cutar su samu man zaitun da man Habbatus sauda su markade wuri daya suna tsefe gashin kansu da shi, a tabbar ya kama gashi sosai.


9. Maganin Kunar Wuta. Kamar yadda take maganin Gyambo hakan take maganin wuta idan mutun ya kone. A samu Habbatus sauda ana shafawa akan gyambon ko kuma inda mutun ya kone Insha Allahu za a samu sauki sosai. 


10. Maganin Gyaran Fata. Koda amarya ce ke idan kika samu garin Habbatus sauda da kuma man zaitun sai ki hade su wuri ɗaya kina shafawa a fuskarki. Ina mai tabbatar miki ko ranar aurenki zaki iya yiwa kanku kwalliya ba sai kin kira kowa ya miki ba saboda fatarki zata yi kyau sosai.


Akwai magunguna da yawa wanda Habbatus sauda ke yi kuma tabbas suna da tasiri. 


1 Comments

Post a Comment

Previous Post Next Post