Yar Kwangila Page 26 To 30 By Mubarak A Kamba Sadaukarwa Ga ArewacinNaija News Team


 YAR KWANGILA.

_(hatsabibiyar yarinya)_

Mubarak A. Kamba

_(ramadan mubarak)_


Zamani Writers Association

(We're Here To Educate, Motivate and Entertain Our Readers).

PAGE 25 To 30



_______________________

Bayan ya ajiye wayar ya dawo kansu. Hankalinsu a tashe ganin tun ba a fara komai ba asirinsu ya fara tonuwa. Murmushi ya yi ya ce, "Kada hankalinku ya tashi koma waye zai sake kira zan san me zan yi."  


"To ai mu kam dole hankalinmu ya tashi, tun tafiya ba ta yi nisa ba wani ya fara sanin me muke saƙawa, gaskiya dole mu kar..." bata ƙarasa ba wayar ta sake sabon ƙara na alamar shigowar saƙo. Sannu a hankali ya duba ya ga wani saƙo an rubuta. "Alh Ina son mu yi waya, amma network ya hanani Abubakar Sale ne ka kirani ta yiyu kai akwai network mai kyau a wurinka." Kafin ya ɗauki wayar ya kirashi sai da yayi ajiyar zuciya. Ai kuwa akayi nasara wayar ta shiga ba tare da matsalar network ba. "Yauwa ina jinka, tambayarka nake ko samu damar haɗa tawagar ne, don akwai wani aiki dake gabana to gudun kada in fara ka dakatar dani ya sa ban fara ba." Abubakar Sale ya faɗa. Alh. Yusuf ya ce, "Yanzu haka muna kan shiri ne ma ka kira, amma yanzu duk inda kake ka yi ƙoƙarin zuwa ka same ni a gidana na unguwar G R A." "To shi kenan gani zuwa yanzu nan." Yana sauke wayar ya yi wani huci tare da kallon su yana murmushi wanda yake ta maimaitawa tun shigowar su.


"Ashe ma abokina ne wanda aikinsa kenan sana'ar Film, saboda haka mun samu wanda zai yi mana Direction na wannan Film da za mu yi don ɓadda kama." Kafin kowa yayi wata magana Fadila ta sake wani irin murmushi wanda ke bayyana irin farin cikinta, domin ita bata da burin da ya fi ta zama ƴar film. 


"Shi kenan muna jiran isowar sa, amma da fatar ba zai ɗauki dogon lokaci ba, saboda yakamata mu tafi gida haka." Na'ima ta faɗa. Mallam Kabiru ya ce, 'Eh to gaskiya ne hakan, amma ku yi haƙuri ya zo a kammala komai." Haka ɗan ɓata lokacin jiransa ya iso ya same su zaune shi kaɗai ake jira. Bayan yayi sallama aka amsa masa ya nemi kujera ya zauna Kamar yadda ya ga kowa a zaune. Alh. Yusuf ya soma magana yana cewa, "Ka yi ta fatar ganin ka sakani a Film ɗin ka, to yau lokacin hakan yayi. Mun gama yanke shawarar yin film domin kawar da kokonto akan aikin da zamu shiga, kuma kai ne zakayi komai na wannan film." 


Cike da farin ciki Abubakar Sale ya sauke wani ɗan numfashi ɗauke da murmushi a fuskarsa ya ce, "To masha Allahu, tabbas na yi farin cikin samun wannan babbar damar da na daɗe ina nema." "Am yanzu ya kuke so a yi?" Ya tambaya. Mallam Kabiru ya mayarsa da amsa kafin Alh. Yusuf ya yi magana. "Wannan ma gaskiya ne, don haka nasan me zan shirya, amma zance na gaskiya, shi Film ba kamar kowane aiki ba ne da mutun ɗaya kaɗai zai iya yin yadda yake so, wasu lokutan labari yakan zo da mutane da yawa wani kuma sai ya zo da ƙalilan, to idan ya zo da mai yawa akwai buƙatar ƙarin ƴan mata da kuma samari ko kuma tsofaffi maza da mata duka baki ɗaya." 


"A'a gaskiya mu kaɗai da ka ganmu mun wadatar ba bukatar a samu ƙarin mutane a ciki, domin kuwa kasan maƙasudin yin wannan film don wata manufa ne ba wai kawai don asalin Film ɗin ba ne." "To to shi kenan ba damuwa, sai dai kuma wani hanzarin ba gudu ba. Dole kowane sai yayi register da ƙungiyarmu ta ƴan Film kafin ya fara shiga a Film, kuma gaskiya kuɗin da ɗan yawa." Abubakar Sale ya faɗa yana kallon Alh. Yusuf. "Kada ka damu zan tura maka miliyan ɗaya nasan dai zata yiwa kowa dake nan register." Kasancewar wannan shine karon farko da Abubakar Sale ya fara ganin miliyan ɗaya yasa shi kakkarwa. Kamar wani tsoho mai shekara ɗari da saba'in harshensa na kakkarwa ya ce, "E eh, eh za zasu yi insha Allahu." Nan take ya rubuta account numbersa ya miƙawa Mallam Kabir ya karɓa tare da cewa shikenan yanzu sai ka tashi ka je ka fara duk wani shiri aiki ya samu domin a kwanan nan zamu fara." 


Ai ko bai tsaya wata-wata ba ya yi saurin fita zuwa shiri kamar yadda aka umurce shi. Bayan ya fita Na'ima ta ce, "Kamar yadda ya fita domin shiryawa mu ma muna buƙatar a bamu damar fita zuwa shiri." Ta yi magana a faɗaɗe, amma ba wanda ya fahimceta face Alh. Yusuf. Hakan yasa yayi murmushi a karo na ba adadi ya ce, "Kowanenku ya rubuta account numbersa ya bawa Kabiru zai turawa kowanenku dubu ɗari." Fadila, Zainab da Nana suka kalli juna cike da mamakin yadda aka fara kashe maƙudan kuɗi tun kafin ma a soma aikin. Kwankwanto ya fara shiga a zuciyarsu. "Wannan ba ɗan mafiya ba e kuwa?" Zainab ta faɗa a ranta. Fadila kuwa ta ce, "Gaskiya wannan da sake, ko shakka babu Yahooboys ne." Haka dai kowanensu ke ta sake-saken a ransa. Nana kam ko kaɗan hakan bai wani bata mamaki ba, domin ta daɗe saninsa.

Kafin nan suka wuce gida kowacen su da na tunanin me za ta faɗawa iyayenta take yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post