Yar Kwangila Page 21 TO 25 By Mubarak A Kamba Sadaukarwa Ga ArewacinNaija News Team

 


YAR KWANGILA.

(hatsabibiyar yarinya)


By

Mubarak A. Kamba


Zamani Writers Association

(We're Here To Educate, Motivate And Entertain Our Readers).

PAGE 21 TO 25

Kowanensu ya samu wuri ya zauna akan manyan kujerin da ke jere a d’akin. Kafin fara wata magana yasa aka kawo musu lemu. ‘Ga abin sha ku fara.’ Nana ta ce mu fara da abin da ya tara mu tukun sannan a yi ta abin sha.’ ‘Hakane kuma, amma sai dai ban tsammaci haka daga gare ki ba, meyasa kika dawo, kuma su wad’an nan ‘kawayen naki me ya ke tafe da su?’ Ajiyar zuciya ta yi ta ce, ‘Eh hakane nasan ba zaka yi zaton zan dawo na kar’bi tayinka ba, to amma bayan da na bar nan samu d’aya daga cikin kawayena muka zanta. Ita ce ta ‘kara bud’emin kai na fahimci komai. Tabbas yakamata. Kawayena kuma sun ji za su iya ayi wannan aikin da su.’ Murmushi yayi ya ce, ‘Naji dad’in wannan tunanin da kukayi, to amma sai dai ina son ku sani wannan aikin ba kamar girka wani abinci ko wanke-wanke ba ne da kowacce mace zata iya.’ Kafin wani ya sake wata maganar Na’ima ta yi saurin kar’ban maganar ta ce, ‘Ba mu zo nan ba har sai da muka mika rayuwarmu akan wannan aikin.’ Ta nuna Fadila da d’an yatsa ta ce, ‘wannan sunanta Fadila mahaifinta attajiri ne ba abin da baya yi mata wanda ranta yake so, amma a dalilin kasancewarmu aminan juna ya sa ta biyo mu. Wannan kuma sunanta Zainab yanzu haka ta fara karatu a jami’a kuma tana matakin farko, amma duk da haka ta yarda zata bada ranta domin yaki da azzalumai.’ 


‘Shi kenan ba damuwa, amma ku d’auka wannan kwangila ce, akodayaushe zan ba wa ‘kawarku Nana kud’in kowane aiki, yayin da ita kuma zata biya ku hakkinku.’ Nana ta gyara zama cikin azzama ta fara maganar kamar cikin fushi ta ce, ‘ba don haka muka....’ bata ‘karasa maganar ba Na’ima ta dakatar da ita ta hanyar d’aga mata hannu ta ce, ‘Is ok Nana koma ya ne ba damuwa za mu yi duk yadda kake so.’ Zainab da Fadila da sauran duk suna zaune suna sauraran su. Mallam Kabir ya ce, ‘Ni na kosa ban ji yadda za a kunno kan lamarin ba, yakamata abar wannan maganar mu san me ya dace na gaba, ko ya kake gani Likita?’ ‘To lallai dai kam ya fi wannan muhawarar da kuke yi.’ Likta ya fad’a. Na’ima ta ce, ‘an gama da wannan muhawarar yanzu kuma tsari na gaba shi ne yakamata mu bijiro da wani aiki wanda zai kau da idon mutane akanmu, domin idan har muka cigaba da tafiya a haka to tabbas mutane za su tuhumemu, kuma aikin dole yakasance aikin maza da mata ne.’ ‘to indai haka ne, me zai hana mu yi aikin shirin film, ina ganin ma ta wannan hanyar ma za mu iya wani aikin ba tare da an samu wata matsala ba.’ Fadila da ta kasance mai son zama ‘yar film ce ta bada wannan shawarar. Na’ima da Nana da kuma Zainab suna dariyar farin cikin samun wannan shawara daga gare ta suka hau yi mata tafi, sauran ma suka biye mu su aka cigaba da tafawa har sai da Alh. Yusuf ya dakatar da su ya ce, ‘Eh tabbas wannan shawarar mai kyau ce, idan muka fara shirin film ba wanda ya zai yi wani mamakin ganinmu a tare. To amma sai dai wani hanzari ba gudu ba.’ Kafin ya cigaba da magana sai da yayi ajiyar zuciya wanda hakan ya sa hankalinsu ya kara karkata a wurinsa. Ya cigaba da cewa, ‘mace ba kamar namiji ba ne da zai iya fita da shiga gidansu a duk lokacin da ya so. A ganinku mahaifanku zasu barku ne ku yi sana’ar film?’ Tambayar da tasa kowanen su yayi tsit ya fada dogon tunani.

Sai can daga baya Nana ta saki wani numfashi tana hure iskar dake cikin bakinta ta ce, 'Wannan ba zai zama matsalarmu ba insha Allahu. Da zarar mun bar nan zamu yi ƙoƙarin fahimtar da su, kuma da yardar Allah zasu fahimcemu." 


"Lallai haka ne, Iyayenmu ba zasu zame mana matsala ba, matuƙar dai Allah na tare da mu, to amma duk da haka yafi kyau idan muka sake fito da wata dabara bayan wannan domin kuwa waƙa ɗaya bata kai safiya.' 'Idan aka samu matsala ta ɓangaren iyaye to zan ɗauke ku aiki a kamfani na duk da yake bana son a fahimci komai har a kamfanin nawa.' Kamar jiran ake ya sauke aya aka danno masa kira ya dubi wayar ya ga wata baƙuwar number ce. Cikin shamaki ya ɗaga wayar tare da karawa. 'Na samu labarin ka haɗa sabon gang domin cimma burinka. To ina son ka sani ita ɗinyar makaho tafi kyau ta nuna a hannunsa, haka kuma don ganin hadari kada ka watse ruwan randarka.' Tun kafin Alh Yusuf ya mai da masa martani ya katse kiran. 'innallillahi Wa'inna ialaihi raj'un.' Abin da ya faɗa kenan wanda ya yi matuƙar ɗaga hankalinsu. Da guda gudansu suka fara jifa masa ayoyin tambaya wasu kuma na ta maimaita kalmar subhanallahi. Nana ce kaɗai hankalinta a kwance.


"Babbar Yaya za su kashe min amini, wallahi sai da naji wani iri da suka ce ya mutu." Babbar Yaya ta yi murmushi ta ce, "Ka shiga ruɗu ne kawai Faruk, amma kam ai yadda za ayi Sultan ya mutu ba a kiraka an sanar da kai ba." Dukansu su kayi dariya suna tafawa. Ya yi musu wani uban harara. Daya daga cikin su ya ce ku tashi mu je. Su ka bar shi nan suna masa dariya a yayin da su ke fita shi kuwa sai hararensu ake Babbar Yaya kuwa ta mai da hankalinta kan karatun da take yi.


Daki ya shiga ya ɗan zauna kan kujera jim kaɗan ya koma kan dogon tunanin da yake kafin su same shi. Nan take bacci yayi awon gaba da shi. Da misalin ƙarfe biyu da rabi ya farko daga baccin da yake. Kansa yake jin yana masa nauyi, don haka ya miƙe ya wuce ban ɗaki.

Bayan ya shiga ban ɗaki yayo wanka ya fito ya wuce ƙaramin ɗakin da yake shiryawa. Ya ciro wani kaftan da hula mai kalar kaftan ɗin ya saka. Bayan ya gama shiryawa ya ɗauko wani turare mai zazzafan ƙamshi tamkar turaren almusƙi ya fesa. Nan take ɗakinsa ya gauraye da wani daddaɗen ƙamshi wanda ke matuƙar sanyaya zuciya. Bai wani ɓata lokaci ba ya dawo babban ɗakinsa inda yake bacci ya ciro wayarsa dake maƙale da caja. Miss called takwas ya gani a shafin wayar. Ya duba ya ga sauran miss called ɗin na abokinsa Sultan ne. Bai wani ɓata lokaci ba da murmushi ɗauke a fuskarsa ya danna masa kira. Jim kaɗan abokin nasa ya ɗaga wayar ya faɗa masa ga shi nan fitowa su haɗu a restaurant. 


Aunty Hauwa da jin yana ambaton restaurant ta fito ta same shi yana ƙoƙarin fita ta ce, 'Ƙanina ina kuma zaka je?' yana ɗan sosa kansa ga hularsa riƙe a hannunsa ya ce, 'wani abokina ne ke son mu je a restaurant wai yana jin yunwa.' 'to ba inda zaka je, don na gama fahimtar ka tun lokacin da ka zo ƙasar nan ba son cin abincin gidan nan kake ba na yi la'akari da mai yiyuwa don bani ke girka abincin ba ne ya sa baka so, hakan ya sa yau da kaina na tsaya na girka maka irin wanda kake so. Saboda haka ba inda zaka je ka kira abokin naka ya zo nan kuci, ai restaurant ɗin ba abin da suka fi mu da shi." Ganin ranta na ƙoƙarin ɓaci ya sa shi ƙyalkyacewa da dariya ya ce, "Naji daɗin haka babbar yaya ina matuƙar alfahari dake ta yadda kike saurin fahimtata. Nagode, yanzun nan kuwa zan kirashi ya zo ga wanda yafi na restaurant.' ita ma murmushi ta yi ta ce, "to da zai fi kam." Tana gama faɗin haka ta fita yayin da ta barshi nan yana kiran abokin nashi.

Yar Kwangila Page 26 To 30 By Mubarak A Kamba


Danna Nan Domin Karanta PAGE 26 To 30 

Bayan wasu ƴan sa'o'i Sultan ya same shi gida suka shiga dinning hall suka ci abinci sannan suka fito zuwa shagon abokin nashi. Jama'arsa dake ƙoƙarin yi masa rakiya duk inda zai je ya dakatar da su. Yana fada musu cewa shi kaɗai zai je, yau ko bakomai yana son zagaya tare da abokinsa kawai. Haka suka fita su biyu sai shagon Sultan. Ba su dade zaune cikin shagon ba wata budurwa mai siyar da abinci kyakkyawar gaske ta shigo ɗauke da kular abinci. Bayan ta yi sallama murmushi fal a fuskarta ta ajiye kular a tsakiyar shagon tana noƙe kanta a ƙasa don kunya. "Maryam ba na faɗa miki zanje gidan abokina mu ci abinci ba? Ai na ce kada ki kawo" tsabar kunya da ƙyar ta samu numfasawa ta ce, "To ayi haƙuri na kawo, na manta ne sai ku ƙara ci." Tana gama faɗin hakan ta fita bata tsaya jiran ya sake yin wata magana ba.


"Wai Sultan yaushe ne zaka yi aure?, Wannan yarinyar ta daɗe tana fama da sonka a zuciyarta me zai hana ka nemi aurenta, kafin na koma England sai ayi auren nan a huta." "Uhmmm ai wato Faruk ba zaka fahimta ba ne, shi aure abu ne mai son nutsuwa. Wannan ɗan akakun da nake da ai ba zai min kayan aure ba. Gidanmu kuma ba wani hali ne da su ba, to tayaya zan yi aure?" "Sultan kada son abin duniya ya ruɗaka a wannan zamanin tara kuɗi mai yawa yana da matuƙar wahala indai halak ake son tarawa saboda haka kada kace sai ka yi wasu maƙudan kuɗi sannan zakayi aure, masu iya magana na cewa mai raina kaɗan ɓarawo ne, don haka ka jarraba neman aurenta mai yiyuwa gidansu mutanen arziki ne, ba za su nemi abinda yafi ƙarfinka ba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post