Yar Kwangila Page 16 TO 20 By Mubarak A Kamba Sadaukarwa Ga ArewacinNaija News Team


 YAR KWANGILA.

_(hatsabibiyar yarinya)._



Mubarak A. Kamba


Zamani Writers Association



(We're Here To Educate, Motivate and Entertain Our Readers).



PAGE 16 TO 20



‘Ina son ki saurare ni da kyau da akwai labarin da zan baki wanda ya faru ne tun kina ‘karamar yarinya misalin kina firare matakin ‘karshe. Wannan labarin da zan baki ya faru akaina kuma ya faru da ke ma.’ Jin ya kawota cikin labarin ya sa ta nutsuwa ta mi’ka dukan hankalinta tana saurarensa. Yayin da ya ajiye kofin da ke hannunsa shi ma ya tattaro hankalinsa ya yi shirin bata labarin da ya dad’e yana mararin bata.


Ya cigaba da cewa, ‘A wasu shekaru da su ka wuce abubuwa maras dad’i sun faru a lokacin mahaifiyata na raye kafin Allah ya kar’bi rayuwarta. Mu biyar ne a d’akinmu, maza biyu da mata uku ni ne na biyu a d’akinmu mace ce a farko haka nan kuma mace ce ‘karshe, yayin da abokiyar zaman mahaifiyarmu ke da ‘ya’ya uku namiji ‘daya da mata biyu. Wasu daga cikin mu takwas d’in nan suna karatu ne a jami’a wasu kuma su na karatu ne a secondary matakin ‘karshe. Muna cikin farin ciki ba wata matsala ko kad’an a tsakaninmu kwatsam wata jarrabawa ta fad’o mana. ‘Daya daga cikin ‘ya’yan mahaifiyarmu ta kamu da son wani d’an iska wanda shi ne yayi sanadiyar tarwatsewar dukan farin cikinmu. A jami’ar da suke karatu ba wanda bai san su ba sun yi suna sosai har ana musu la’kabi da suna Romeo and Jullet. Maryam ta kamu da son sa sosai ba kad’an ba har tana ji a ranta idan aka rabata da shi ba zata iya rayuwa ba. Suna tsaka da yin soyayyarsu wata rana ta gabatar da shi gidanmu a matsayin wanda za ta aura. Mahaifinmu yayi farin ciki kuma yayi mata al’kawarin ba wanda zata aura face shi wanda take so wato Nasir, amma sai dai ni nasan shi farin sani ba shi da tarbiya ko kad’an kuma ya san nasan haka, amma duk da haka bai sa ya daina cigaba da yaudararta ba. Nasir ba shi da wani aiki ingantacce wanda ya fi lalata ‘ya’yan mutane, domin kuwa aikinsa d’aukar ‘yan mata aje da su gari zuwa gari da sunan sana’a ta hanyar fakewa da rawar solo. Cikin nutsuwa na sanarda mahaifiyarmu wanda Maryam take so ba tsararta ba ne na fad’a mata irin halinsa don haka ni ba zan goyi bayan ta aure shi ba ita ma mahaifiyarmu ta nuna ba zata yarda ‘yarta ta auri d’an iska ba. Jin haka ya sa mahaifinmu ya fara fushi da mu har da mahaifiyarmu yana cewa mun mai da shi mutumin banza. Tun daga wannan lokacin farin cikin gidanmu ya tarwatse komai ya lalace. Rayuwa na cigaba da kasancewa cikin ‘kunci Nasir da Maryam suka bar gari da nufin zasu je wani garin a d’aura mu su aure. A wannan lokacin ba inda ba mu shiga ba a fad’in ‘kasar nan wurin nemanta amma ba ita ba labarinta, hakan nan muka ha’kura wannan ne yasa mahaifiyarmu ta kamu da ciwon zuciya kullun mu na asibiti neman magani. Bayan wasu shekaru Maryam ta dawo gida d’auke da juna biyu cike da nadamar bijirewa mahaifiyarmu. Ciwon Mama ya ‘kara yawaita kodayaushe aikinmu bai fi nema mata magani ba, amma da ya ke wa’adinta ya cika bata ‘kara ko kwana d’aya ba ta ce ga garinku nan. Allah ya ji’kan Mama da rahama. Mahaifinmu kuma, ya d’auki matarsa guda suka yi ‘kasar waje har yau Allah bai sa ya dawo ba. ’ Ya sa hannunsa yana matse hawayensa da suka zubo tamkar ana yayyafi. Tausayinsa yakamata idanuwanta suka ciko da ruwa ta yi wani zaman nutsuwa tana saurarensa ya cigaba da cewa, ‘irin wannan al’amarin ne ya faru a gidanku. Mahaifinki yana da mata guda wacce ita ce mahaifiyarki. Ta haifeku ku uku ne kamar yadda a ‘dakinmu mace farko haka nan kuma mace ce a farko sai namiji da ke bi mata sannan ke autarsu. Sadik, Ummulkhairi da kuma ke Nana Fatima. Sunan mahaifiyarki ne aka saka miki wannan ne ya sa suke kiranki da Nana. Yayarki Ummulkhairi yarinya ce kyakkyawa mai cikar kamala da nutsuwa ga tarin ilmin boko da na zamani. Wani d’an attajiri ne wanda ba shi da tarbiya ya ke sonta haka nan kuma wani d’an talakawa ke sonta wanda shi ne take so. A cewarta ‘ya’yan masu kud’i basa ri’ke aure don haka ba zata iya rayuwar aure da irinsu ba. Ganin bata sonsa ne ya sa aka tare ta a kan hanyarta zuwa islamiyya aka tare ta aka yi mata fyad’e sannan aka yi mata allurar bacci wanda hakan ya sa ta fita hayyacinta.’ Bata san lokacin da yawu ya sar’ke ta ba. Ta yi wani ‘kufa idanuwanta cike da hawaye, ganin ya san wannan labarin da aka dad’e ana ‘boyewa ne yayi matu’kar bata mamaki. Kwatsam ta je fa masa ayar tambaya ba tare da ta yi shirin yin haka ba. Yayi murmushin ‘karfin hali hawayensa na cigaba da tararowa. ‘ranar da muka je asibiti neman maganin mahaifiyarmu. Tana kwance kan gadon asibiti ta samu labarin abin da ya sa aka kawo mahaifinku hakan ya sa ba’kin ciki ya ‘kara d’arsuwa a zuciyarta ciwonta ya ‘kara yawaita, har yaci ‘karfinta ta kammala ba’kuncinta. Dalilin mutuwar mahaifinki kuma lokacin da aka yi wa yayarki Ummulkhairi fyad’e ya zurfafa bincike ya gano aikin wannan d’an attajirin ne don haka sai yayi ‘ko’karin ‘kararsa a kotu. Abin takaici bai yi nasara ba a kotu domin kuwa an nemi da ya kawo hujjoji da kuma shaidu wanda bai samu ko d’aya ba daga ‘karshe a ka yanke ma sa hukuncin tarar kud’i ma su yawa wai yana zargin wanda bai aikata abin da ake zargi ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa ba’kin ciki yayi masa yawa har ya kamu da ciwon zuciya Allah ya kar’bi rayuwarsa cikin salama domin kuwa ya mutu yana ambaton kalmar shahada. Allah ya ji’kansa da rahama ya gafarta ma sa idan tamu ta zo kuma Allah ya sa mu cika da imani.


‘Ameen summa ameen.’ Ta fad’a Hawayenta na zubowa tana sharewa. ‘Usman ka d’auko mata ruwa a freezer kafin nan...’ Alh. Yusuf ya fad’a. Usman da ke cikin d’aki zaune ya yi saurin d’auko mata ruwan gora kamar yadda aka umurce shi ya kawo mata. Cikin mamaki ta mi’ke tsaye tana cewa, ‘Usman! Kai ne a gidan nan? Me ya kawoka?’ kafin Usman yayi magana mallam Salihu ya fito daga d’ayan d’akin ya ce, ‘Kada ki yi mamakin ganin Usman mu duka mun had’u ne a nan kawai saboda cikar wani burinmu.’ Hankalinta yayi matu’kar tashi ta yi ma sa wani irin kallon mamaki, wanda mamakin ne ya hana ta furta ko kalmar A. Mallam Kabir dake gefe zaune kan kujera ya ce, ‘Nana ki nemi wuri ki zauna sai ki ji me dalilin taruwarmu a nan. Idan zaki cigaba da mamakin wannan duniyar to kuwa har mamakinki ya ‘kare ba zaki daina ganin abubuwan mamaki ba.’  


La’kwas ta koma ta zauna tare da zabga uban tagumi tana cigaba da sauraren su. ‘Idan har za a bar ire-iren wad’annan mutanen na cigaba da rayuwar su cikin walwala to ya ya rayuwar ire-irenmu zata kasance?’ Alh. Yusuf Ya jefa mata ayar tambaya yana kallon ta tare da jiran amsarsa. Cikin wani yanayi na marairaicewa ta amsa ma sa da kalma d’aya tana cewa, ‘’Kunci da rashin walwala.’ ‘kenan ta ya ya za a iya magance wannan matsalar?’ ya sake tambayarta. Kafin ta amsa yayi saurin amsa mata ya ce, ‘Ba wanda zai iya magance ire-iren su face ma’aikatan gwamnati.’ Murmushi Mallam Kabir ya yi kana ya ce, ‘An kashe mahaifinta ne a dalilin yun’kurin sa na kai ‘karar wad’an da yake tuhuma, amma duk da haka ba wani abu da su wad’an nan da muke sa ran za su iya ‘kwato mana ‘yancinmu su ka yi.’ Jin haka ya sa ruwan Hawayenta su ka ‘kara yawaita.


A lokacin da kowa ya yi shiru ne Mallam Salihu ya ce, ‘Wannan ne ya sa muka had’u a nan domin bijiro da wata hanyar dakatar da wad’an nan tataccin mugayen. Wannan ‘kudirin namu ba zai cika ba har sai kin amince, nasan zaki tambaya ta wace hanya. Hanyar ita ce kamar yadda suke yi su na yaudarar mu haka nan za mu yi mu yaudare su. Ke ce! Ke ce!! Ke ce!!! Nana ke kad’ai ce wacce zata iya wannan aikin.’ ‘Ni kuma? Abin da gwamnati ta kasa yi ni me zan iya yi? Yadda mu ka yi ha’kuri muka bar su da Allah ko yanzun ma ha’kuri za mu cigaba da yi, domin kuwa d’aukar hukunci da kai ma laifi ne. Ni kad’ai ce wacce mahaifiyata ke kalla ta ji wani sau’ki a ranta, idan wata matsala ta faru da ni ya kuke so ta yi?’ Mallam Salihu zai yi magana ta dakatar da shi ta hanyar d’aga masa hannun. ‘Ka da ka ce komai, idan su ba su san wacece mahaifiyata ba, kai ka santa dan Allah ku yi ha’kuri ba zan iya wannan aikin ba.’ Ta fad’a tare da ficewarta waje tana kuka. 


Da fitar ta waje ta nufi hanyar gida. Ta tsallake titi kenan ta ga wani mai mota ya tsaya a gabanta. Caf ta yi tsaye tana jiran fitorsa ko wata maganarsa. A lokacin da take share hawayen da ya wanke mata fuska ya fito daga mota ya yi tsaye a gabanta. Likita ne ta gani tana mamakin yadda bata ganshi a wancan zaman ba sai a yanzu. Ya kalleta yana jin tausayinta ya ce, ‘Ina son ki zo mu je asibiti in nuna miki wani abu da zai baki mamaki.’ Ba ta yi wani dogon jayayya ba ta shiga matarsa suka wuce asibitin da ya ke aiki. Wani d’aki in da maras lafiya suke ya shiga da ita. Wata ‘karamar yarinya wacce bata fi shekara sha bakwai ba ya nuna ta da d’an yatsa a yayin da take kwance mahaifiyarta na gefen gadonta tana mata fifita ya ce, ‘Inna ina son ki yi mata bayanin matsalar wannan yarinyar ta ki dake kwance kan gado.’ Mahaifiyar yarinyar da a ke magana ta fashe da kuka tana ‘ko’karin yi mata bayani, amma ta kasa yi. Likitan ya ce, ‘ki yi ha’kuri Inna ba na tambaye ki ba ne don tuna miki wannan abin ba’kin cikin ba ne sai don ina son share wa wannan yarinyar wata tantama ne.’ Daga nan ya fita zuwa wani d’akin Nana na biye da shi duk inda ya shiga. Sai da suka shiga kusan d’aki biyar sannan ya wuce da ita ofis d’insa. Bayan ya zauna ita ma ta nemi kujera ta zauna. Ya soma yi mata karatun ta nutsu, yana cewa, ‘dukan wad’an nan ‘kananan yaran an yi musu fyad’e ne. Shin haka za mu zuba ido muna kallon yadda wad’an nan mugayen zasu cigaba da lalata mana rayuwa? Ba zai yi yu ba, wallahi ba zai yi yu mu zuba ido muna kallo ana kashe mu ana wala’kanta mu ba. Mun za’be ki wacce zata taya mu aikin nan ne saboda kina d’aya daga cikin ire-iren mu, da akwai wad’an da kodayaushe za su iya ta ya mu aikin, amma muka za’be ki saboda ki d’auki fansar kisan ‘yar uwarki da a ka yi. Ka da ki ta’ba tunanin wani mummunan abu zai faru dake mun riga da mun tsara komai ba wani abu da zai faru dake da yardar Allah.’

Daga nan ya d’auko wasu takardu a ‘kar’kashin desk d’insa ya dam’ka mata ya ce, ‘Wannan takardun gidan da kuke zaune ne, idan baki manta ba na ta’ba fad’a miki cewa Alh. Yusuf ba abin da ba zai iya yi miki ba, saboda haka ga takardun gidanku ba haya kuke yi ba. Idan kin koma gida ki yi nazari sosai a kan wannan.’ Tasa hannu biyu ta kar’bi takardun cike da mamaki Hawayenta na ‘kara zubowa kamar ba zasu ‘kare ba. Mamakin ne ya hanata furta komai ta fito waje tana ta sake-saken me zata ce da Mahaifiyarta. Wata zuciya na fad’a mata ya fi kyau ta sanar da mahaifiyarta koma me zai faru ya faru, wata zuciyar kuma na fad’a mata kada ta yi hakan. Daga ‘karshe ta yanke shawarar ta je gidan ‘kawarta Na’ima ta sanar da ita abin da ke faruwa. Hakan ta yi bata yi ‘kasa a guiwa ba ta hau adaidaita sahu sai gidan su Na’ima. Bayan ta yi sallama ta sami mahaifiyarta na aika-aikacen gida suka gaisa. Daga can d’aki Na’ima ta ji yo muryarta suna gaisawa da mahaifiyarta ta fito da murmushi a fuskarta. ‘Shegiya wai ke ce yau a gidan namu, tabbas ruwa baya tsami banza, mu shiga ciki in ji abin da ke tafe dake.’ Ta kama hannunta su ka shige d’akinta. Su na shiga ciki Hawayenta suka cigaba da zubowa. ‘me yake faruwa na gan ki haka, kada ki fad’amin abin da hankalina ba zai d’auka ba. Fatan Umma na lafiya.’ Na’ima ta fad’a yayin da take ri’ke da hannunta ‘Lafiya ‘kalau Umma take Na’ima ina cikin wani hali na rasa ta ya ya ma zan yi miki bayani.’ Ta fad’a tare da direwa kan katifa. Na’ima ta yi wani murmushi duk da ganin Nana na zubar da hawaye ta ce, ‘Ai tunda har Umma na lafiya to komai ma mai sau’ki ne, idan kika fad’a mata koma mene ne damuwarki na tabbata Umma zata iya share miki hawayenki.’ ‘Be serious mana Na’ima ba zaki gane ba ne idan har ba na miki bayani ba.’ Nana ta fad’a. ‘To wai me ke faruwa ne ki yi min bayani mana.’  


Assalamu alaikum masoya wannan littafin ‘YAR KWANGILA.

 Mubarak A. Kamba wato ni marubucin wannan littafin ina mai baku ha’kuri a bisa tsaiko na kawo muku shi a kan lokaci. Bayan wannan kuma ina son in fahimtar da mai karatu ya fahimta cewa ana cikin wannan maganar a koma kan wannan ne domin tsara muku littafin ba don wani abu ba. Idan mai karatu ya lura zai ga idan a ka soma wannan sai a koma wannan to duk ana yin hakan ne domin ‘kara inganta muku shi cikin tsari. Fatan kun fahimtar bissalam.





Idan da akwai wata kyauta da zaku yi min domin saka ni farin ciki, to ba zata kai ku yi min comment ba. Dan Allah ku yi comment da ra’ayinku akan wannan littafin, idan ya burgeku ko kuma sabanin haka. Haka kuma kada ku manta da Like, wannan ne kad’ai zai karamin karfin guiwa wurin cigaba da kawo muku cigaban wannan littafin.

‘Ki nemi wuri ki zauna kafin nan, domin zaki iya yankewa ki fad’i a ‘kas.’ Ba tare da yin musu ba Na’ima ta nemi kujerar d’aya daga cikin kujerin da ke cikin d’akin ta zauna sannan ta tattaro dukan nutsuwarta ta mi’kawa Nana. ‘Ina jin ki yanzu, yi min bayani ta yadda zan gamsu.’ ‘zan kuwa yi miki kamar yadda kika bu’kata, amma da sharad’in wannan maganar zata kasance sirri a tsakanina dake.’ Fad’an haka ya sa Na’ima ta ‘kara nutsuwa tare da cewa, ‘Wannan shi ne al’kawarin da ba zan gaza cika miki ba. Fad’amin abin da ke faruwa.’ Sai da Nana ta goge ruwan hawayen da ke tirarowa a kan kumuta sannan ta fara ta bata labarin dukan abin da ya faru a tsakaninta da waccen majalisar ta Alh. Yusuf da ma’karabansa.’ 

‘Babbar magana!’ Na’ima ta fad’a a lokacin da ta ke mi’kewa tsaye. Ta ri’ke baki tana mamaki. Ta d’auki tsawon mintina tana nazari. Daga ‘karshe ta yi wani murmushi wanda ya gamsar da Nana ta samo mafita. Komawa ta yi ta zauna cikin sanyin jiki. ‘Nana ina mai tabbatar miki da cewa wannan wani babban aiki ne wanda ba ke kad’ai ya dace ki yi ba.’ Na’ima ta fad’a. Nana kuwa ta yo mata ‘kuru da ido tana son jin cigaban maganar. Da Na’ima ta fahimci hakan kuwa ta cigaba da cewa, ‘Nima dai na ta’ba tunanin ya kamata a samu wasu mazan ko mata wad’an da zasu yi irin wannan ‘ko’karin, amma Allah da ikonsa sai ya dawo da aikin a gare mu.’ Tana magana murmushin fuskarta na ‘kara fad’ad’awa. Ganin haka ya ‘kara tada hankalin Nana, a fusace ta mi’ke tsaye zata fita Na’ima ta cafke hannunta. ‘ki sakarmin hannu, kafin na zo nan sai da na yi dogon tunani wacce ko wane yakamata na fad’awa wannan damuwar tawa, shi ne har zaki raina min...’ bata ‘karasa maganar ba ta fashe da kuka har sautin kukanta ya kai a kunnen mahaifiyar Na’ima dake d’akinta. Da sauri ta yo d’akin da suke ta same su tsaye a tsakar d’akin. ‘Me yake faruwa kike kuka Nana?’ ta tambayeta wanda hakan ya sa ta ‘kara fashewa da wani sabon matsanancin kuka ta fita waje tana cigaba da share hawaye. Tabarsu nan suna wa juna kallon kallo. ‘Me ya faru da ita take kuka fatan dai ba ciwon mahaifiyarta ba ne ya sake motsawa.’ Fadin haka ya sa Na’ima ta d’an saki fuska don dama tunanin me zata fad’a idan ta tambayeta take yi. ‘Eh haka ta ce min, ina ga zai fi kyau in je gidan in ga abin da ke faruwa Umma.’ ‘Eh to kuma hakane, amma kada ki jima don yanzu duk inda Babanki yake yana kan hanyarsa ta dawowa ki hanzarta ki dawo ki yi masa kunun tsamiyar don shi ne abin da zai fara tambaya nasan da hakan.’ ‘To Umma.’ Na’ima ta fad’a ta yi saurin saka hijab d’inta ta bi bayan Nana. Ta hanyar da tasan Nana ke bi idan zata zo gidansu ta bi don so ta yi ta had’u da ita kan hanya, amma sai dai aikin gama ya gama tun-tuni ta isa gida. 


Ba ta dad’e da shiga gidan ba sai ga Na’ima bayanta. Kallo d’aya zaka yi musu ka fahimci irin yanayin da suke ciki. Koda su ka shiga su ka sami Umma na ‘ko’karin shiga d’aki, amma ganinsu ya sa ta fasa shiga ta dawo ta same su cirko-cirko. ‘Lafiya dai me ke faruwa, na gan ku haka?’ Na’ima ta yi saurin cewa lafiya lau Umma, mahaifiyata ce ba ta da lafiya shiyasa kika gan mu a cikin wani yanayi.’ Ayya fatan dai da sauki? Gaskiya ba dad’i.’ Ta fada sannan ta waigo ta kalli Nana da har yanzu bata ce komai ba. ‘Ki shiga da ita mana, kun zo kun yi tsaye kamar dai marasa gaskiya.’ Murmushi Na’ima tana ‘ko’karin ‘boye mata abin da ke faruwa. Dakin Nana suka shiga. Shigar su ke da wuya Na’ima ta hau azarbabi. Ta inda take shiga bata nan take fita ba. ‘Ki yi tunani Nana wannan abu ne da ya kasance tamkar yaki da rashin adalci. Ina miki magana ne har a cikin raina ba wai da wasa nake miki ba.’ Hankalin Nana kad’uwa ta ce, ‘Wai me kike nufi, kin kuwa san me kike fad’a? Mahaifiyata ta kamu da ciwon zuciya ne a dalilin rasa yarta d’aya, yanzu idan ta rasa ni me zai biyo baya. Gaskiya ni sai dai in ce ku yi ha’kuri ba zan iya wannan ba. ‘ wasu hawaye Na’ima tana tunanin da me zata fahimtar da ita, can cikin garin zurfin tunani ta ci karo da abin da zai karya zuciyarta.’ Shikenan na ji, amma don Allah ina son ki biyo ni ina son zan nuna miki wani abu.’ 


Ta amince da hakan suka fita waje su ka samu mai adaidaita ya d’auke su sai gidan marayu.’ Nana dai na biye da ita cikin tsanaki take mata wani irin kallo. ‘Daya daga cikin ma’aikatan Na’ima ta kira. Wata mata ce wacce bata fi shekara hamsin ba kuma bata gaza arba’in ba ta zo ta same SU ta ce, ‘Lafiya dai ‘yan mata me ke tafe daku ne?’ Na’ima ta ce sun zo ganin marayu ne. Ba tare da wani shamaki ba ta ja su har cikin d’akin yara ‘kanana wad’an da ba su gaza shekara sha biyu ba. A cikin d’akin su ka samu yaran nata wasa cikin walwala suna dariya da alamar ba abin da ke damuwarsu. Ma’aikaciyar ta kira d’aya mai wayo a cikinsu ya zame gun da suke. ‘Wannan ‘karamin yaro ne da aka tsinta akan hanya akodayaushe muna jiran zuwan mahaifansa amma har yau shiru kake ji.’ Daga nan ta ‘kara kiran wata ‘karamar yarinya ta ce, ‘Wannan kuma an yi wa mahaifiyarta fyad’e ne garin haifuwarta mahaifiyarta ta mutu.’ Zata ‘kara kiran wata kenan Na’ima ta fashe da kuka ta ce, ‘Ya isa haka ki bar su dan Allah.’ Daga nan suka fito su ka yo gidan su Na’ima. A cikin d’akinta suka shiga. Cikin tattausar murya ta ce, ‘Yanzu haka za mu kawo ido mu zuba ana ta kashemu kamar kiyashi, haka nan ana amfanin da mu kamar dabbobi. Nana idan ke ba zakiyi ba, ni ki had’ani da su zan yi musu duk yadda suke so. Wallahi a shirye nake na bada raina domin ceto rayuwar al’umma.’ ‘Idan har za mu yi wannan aikin ba shakka zamu samu kudi sosai, duk da yake ba dan kud’in za mu yi ba, kina ganin da me zamu fake ta yadda ba za a ta’ba gane mu ba saboda su kud’i basa ‘boyuwa dole mutane zasu saka mana ido.’ Nana fad’a. Murmushi Na’ima ta yi da taji Nana ta amince ta yi wani irin numfashi sannan ta ce, ‘Wannan su ne suka san me za su yi, amma dai ba zamu bari iyayenmu su san da zamu yi wannan ba domin kuwa idan har suka sani ba zasu ta’ba yarda ba.’ ‘Ba za su sani ba a yanzu, amma fa komai daren dad’ewa za su sani.’ ‘A lokscin da za su sani mun yi nisa da aiki ta yadda ba za ma su iya hana mu ba. Ke dai kawai ki yi ‘ko’karin sanin me zaki fa’dawa Umma.’ Shiru Nana ta yi tana tunanin me zata fad’awa Umma wanda zai kwantar mata da hankali.’ ‘Yakamata mu kira su Fadila da Zainab saboda a tare mu ke yin komai, wannan ma a tare za mu yi.’ Ta katse mata tunanin da take yi. ‘To dama fa ai dole ne tare da su za mu yi, yanzu dai ki yi ‘ko’karin sanar da su ni zan tafi gida zan yi ‘ko’karin shawo kan Umma.’ Daga nan ta tashi suka fita waje ta yi mata rakiya har bakin titi ta tare mata mai adaidaita sai da ta ga shigarta sannan ta dawo gida. A tsakar gida Nana ta samu ta tara kayan wanki ta na wankewa. 


‘Lahh! Umma wanki kike yi da wannan jikin naki maras ‘kwari?’ ‘To Nana ya kike so na yi tunda tun safe da kika bar gidan nan sai yanzu kika samu damar dawowa.’ Dariya Nana ta yi ta ce, ‘Ai Umma ki bari kawai ina cikin farin ciki sosai burina ya fara cika.’ ‘Uhmm! To ina jin ki wane burin naki ne ya yi kusan cika? Fad’amin.’ ‘Umma ba na fad’a miki cewa wata rana zan samu aiki a wannan kamfanin na MBLOG ba?’ Murmushi kawai Umma ke maimaitawa tana cigaba da wankinta. ‘Eh kin ta’ba fad’amin haka wani abu ne?’ ta fad’a. Nana ta ce, ‘To na samu aiki a kamfanin, yanzu haka takarduna kawai suke jira in kawo mu su.’ ‘Bana son shashanci! Yau zolayar da kike wa ‘kawayen naki shi ne kike min?’ ‘Wallahi Umma da gaske nake yi, bakin ga d’azun Na’ima ta shigo a nan ba, to maganar da muke yi kenan.’ Umma ta zaro idanu mamaki ya cikata ta ce, ‘To ke Nana a ina kika samu takardun yin wannan aikin bayan takardun sakandire ne kawai kika mallaka?’ ‘Ai Umma da takardun sakandiren ne suke bu’kata, a cewarsu ma nan zuwa gaba zan iya shiga jami’a.’ Umma ta saki wankin da take yi ta rike habar baki ta ce, ‘Ikon Allah to wai shi wannan Kamfanin aikin me suke yi, kuma ke wane irin aiki zasu baki?’ Shiru Nana ta gaza amsa wannan tambayar tana wani kame-kame. Umma ta sake tambayarta a karo na biyu. ‘Wane aiki suke yi, kuma ke me kika yi mu su da har suka dauke ki.’ Da kyar ta samu ta dago ta ce, ‘Nima dai bansan me yasa suka dauke ni ba, amma dai koma mene ne zan sani idan na kai mu su documents din nawa.’ ‘Mene ne docoman kuma?’ Ta fad’a Nana ta kyalkyale da dariya ta ce, ‘Umma kina da abin da dariya, to takardu ne documents.’ Kafin Umma ta sake wata maganar ta yi saurin wucewa d’akinta don gudun kada allura ta tono garma. Tana shiga d’akinta ta fara abin da ta saba. Kuka take yi tana jin wani ‘kololon bakin cikin a zuciyarta. A ranta take ta nanata cewa yanzu shikenan na fara yiwa Umma ‘karya, yanzu me zai faru idan ta fuskanci gaskiya oho.’ ‘yar ‘karamar wayarta ta yi ‘kara da sauri ta d’auko ta duba ta ga Fadila ce ke kiranta. Wani irin fad’uwar gaba ta ji. Ta ce, ‘Na’ima ta sanar da su Zainab kenan, ni wallahi duk ma naji na karaya.’ Ta fad’a ita kad’ai a cikin d’aki take ta subbatu. Bayan ta d’aga wayar ta ce, ‘To shikenan yanzu nan zan fito.’ Daga nan ta wuce d’akin Umma ta d’auko takardunta ta fito ta shirya sannan ta ce da Umma sai na dawo. Umma ta yi mata addu’ar sa’a da fatan nasara, tare da gargad’in ta yi a hankali kada ta yi abin da zai kawo dana sani. Godiya ta yi da sauri ta fita kai tsaye ta nufi gidansu Na’ima. A can ta tarar da su har sun fito ‘kofar gida ita kad’ai suke jira. ‘wai ke tun lokacin sai yanzu kika ga damar isowa ko me ya tsaida ke?’ Tsaki ta yi ta ce, ‘Koma dai me ya tsaida ni ai gani na zo, mu je gidan mu ji me suka shirya ko ma ya tsarin yake.’ ‘Kafin mu tafi yakamata mu yi wa juna al’kawarin wannan aikin da muka shiga ba zamu bar shi ba har sai mun cika burinmu.’ Na’ima tana binsu da kallo a yayin da suke tsaye suna shirin zuwa gidan Alh. Yusuf. Nana ta aika mata wani uban harara ta ce, ‘to ‘yar mazari ai zaki jira dai mu ji yadda suka shirya ko? Idan mu ka yi wannan al’kawarin muka je muka tarar da tsarin da ya fi ‘karfinmu sai ki ce me kuma?’ a lokaci guda suka bushe da dariya. Da alamar Nana ce kad’ai take tsoron wannan aikin da za su yi. Fadila da Zainab kam tun lokacin da Na’ima ta yi mu su bayani suka gamsu kuma suka amince ba tare da wani fargaba ba. 



Mai adaidaita sahu sukatare ya d’auke su sai ‘kofar gidan Alh. Yusuf. Dan saurayin da suka tarar ‘kofar gidan ba mai gadi ba, amma tamkar mai gadi irin yadda yake tsare ‘kofar gidan. Magana su ka yi masa suna neman Alh. Yusuf. Ganin su kyawawan ‘yan mata ga kuma Nana da ya ga ta shigo gidan last time ya sa shi ankarewa da su. Da murmushi a fuskarsa ya ce, ‘Bari na kira muku shi, yanzun nan ya fita.’


Alh. Yusuf dake cikin motarsa yana tuki zuwa wani wurin wayarsa ta yi ‘kara ya duba ya ga yaronsa ne ke kiransa, ya rage tafiyar motar sannan ya d’aga wayar tare da karawa a kunnensa. ‘ka ce su hud’u? To ko zan iya sanin d’aya daga cikin su?’ Yaron da ke kiransa ya tambaye su, ‘oga na tambayar ku su waye?’ Na’ima ta ce, ka fad’a masa Nana ce.’ Yana jin sunan Nana ya ja burkin motarsa ji kake ‘kiiiii ya yi saurin yowa kwana ya juyo ya dawo. Da yake ba wani nisa ya yi ba nan take ya kawo. A ‘kofar gida ya same su tsaye suna jiran isowarsa. Bayan an bud’e masa ‘kofa ya shiga yayi parking na matarsa sannan ya dawo ya yi musu iso. ‘Bismillah mana mu shiga ciki.’ Ya fad’a yana shige musu gaba suka mara masa baya. Yana ‘karasawa cikin babban d’akin da suke zama ya kira wayar Likita da mallam Salihu da kuma Usman. Ba su d’au dogon lokaci ba suka iso gidan.

Post a Comment

Previous Post Next Post