YAR KWANGILA.
(hatsabibiyar yarinya).
Mubarak A. Kamba
Zamani Writers Association
(We Educate, Motivate and Entertain Our Readers).
Sadaukarwa; Ga ArewacinNaija News Team
Jinjina Ga; Abokina Muntasir Shehu
PAGE 10 TO 15
Tafiya take amma hotonsa yake mata gizo a ido. Duk lokacin da ta ganshi sai ta yi wani tsaki tare da kokarin mantawa da lamarin, kuma hakan ya gagareta. Da haka dai har ta isa gida bata daina tunaninsa ba. Isarta gida ta tarar da Umma bata nan ta fita unguwa. Ganin Umma bata gidan ya kara tayar mata da hankali don gani take idan Umma na nan zata iya samun damar mantawa da shi.
Tun da suka bar asibitin bai kara yin wata magana ba har suka isa gida. Isarsu gida jama’a suka fara tarbo shi ciki kuwa har da makada da maroka tamkar dai wani dan sarki ne ya shigo gari. Haka ake yi masa akowane lokaci idan ya zo, kuma ana yi masa hakan ne a dalilin kasancewarsa mutun mai kyauta. A yau kam sai ya bawa jama’a mamaki saboda bai tsaya sauraren kowa ba. Idan ya kawo wurin jama’a sai ya wuce su kamar bai san da su ba har ya ‘karasa ciki. Hajiya Hauwa dake zaune a cikin babban falonta tana jiran shigowarsa ta zo da gudu tana masa maraba. Karamar yarta wacce bata fi shekara sha daya ba ta zo da gudu ta rungume shi, tana fadin, ‘oyoyo uncle.’ Ya ‘dauke ta sama yana cewa, ‘Fanan, wai ke ce kika girma haka?’ Yana wasa da ita don nasarar boye abin da ke ransa, amma duk da haka fuskarsa bata ‘boye ba. Kallo daya Hajiya Hauwa ta yi masa ta so gane abin da ke faruwa da shi. ‘Babu walwala a tare da kai, babu wani murmushi, ba annuri ko kadan a fuskarka. Ba haka nasan ‘kanina yake ba. Me yake faruwa ne? Ko ba’a nan ka so sauka ba ne Faruk?’ ta fada tana masa wani kurarren kallo.
Sai a lokacin ne ya kirkiri wani murmushin karya ya ce, ‘Aa Babbar Yaya ba wani abin da ya faru kawai dai gajiye ne, kinsan yadda tafiyar jirgi take a wasu lokutan duk sai mutun ya ji kansa wani iri.’ ‘Eh haka ne kam, to amma dai wannan yanayin naka baya kama da na masu gajiya.’ ‘Babbar yaya gaskiya fa nake fad’a miki gajiya ce kawai.’ ‘Well is ok get in, ya jama’ar England ko ma in ce ya turawa?’ ‘Kowa ma na lafiya, Babbar Yaya zan yi wanka yanzun nan ina so naje gidansu Gwaggo Fati na kosa ban ganta ba.’ Sai da ta yi shiru sannan ta ce, ‘To ba damuwa, idan ka dawo ka fadamin me ya ke damunka.’ Murmushin karya yake ta maimaitawa wanda karara yake bayyana abin da ke kasan zuciyarsa. Ya wuce a dakin da yake sauka a duk lokacin da ya dawo da tafiya. Ya samu an gyara komai na dakin sai kamshin turaruka daban-daban ke tashi.’ Abinci da abin sha da kuma kayan marmari nau’uka daban-daban a kan wani kyakkyawan karamin tebur dake tsakiyar dakin. Daya daga cikin manyan katafaren kujerin da suka ci kusan rabin dakin ya zauna kanta tare da dora kafarsa daya kan daya. Tunanin Nana kawai yake yi ya rasa me dalilin wannan tunanin yanata maimaita maganganu shi kad’ai a cikin d’akin. ‘Meyasa nake ganin ta a idona, me ya sa, me ya..?’ A dan ‘kan’kanin lokaci ya ji kansa wani iri.
Danna Nan Domin Karanta PAGE 5 TO 10
Bayan ta dawo daga unguwa ta zo ta same ta a dakinta ita kadai sai surutu take yi. A bakin kofar dakinta ta yi tsaye na kusan minti uku amma Nana bata san ta shigo ba. ‘To ko dai aljani ne shi? Amma idan aljani ne me ya sa nagan mutane a bayansa kamar dai wani dan siyasa? Na rasa me dalilin da yasa na ke ganinsa cikin idona?’ tambayoyi kawai take maimaitawa wanda ba mai amsa mata. Sai daga baya mahaifiyarta ta ce, ‘Tunanin wa kike yi da har kike masa zaton aljani ne?’ ras ta ji wani iri, zuciyarta na amsa luguden uku sau uku a kidime ta mike daga kwanciyar da take akan wata tsohuwar tabarmarta. Ta na yin zaune kuma ta bita da kallo, golden eyes dinta kamar zasu fito. Ganin ta canja yanayi ta shiga na firigici ya sa ta sakar mata fuska. Murmushi ta yi ta ce, ‘Nana tambayar ki na ke yi waye wannan da ki ke wa kallon aljani?’ ‘Ba.. ba.. wa.. wani fa Umma Likita ne ya...’ ‘ya yi me? Me Likitan yayi Nana yau kuma ni din ce zaki boyewa wani abu da ya shafi rayuwarki? To shi kenan bakomai ba ni maganina.’ Ta karbi maganin tare da cewa nata dakin. ‘Oh my God! To wai ma mene ne na boyewa Umma wannan lamarin? Ba zai yiyu in boyewa mahaifiyata dan wannan abun ba.’ Ta yi saurin mikewa ta bi bayanta. A daidai lokacin ta balla magani zata kai baki ne ta gan shigowarta ta yi tsaye. Bayan ta gama shan magani ta kama hannunta suka zauna a tare. Cikin tattausar murya ta soma yi mata magana a natse. ‘Nana ina son ki sani duk duniyar nan baki da wacce zaki fadawa wata damuwarki da fini, kada ki manta duk duniyar nan ni kadai ce mahaifiyarki, me ya sa ki ke son boye min? Kin ga kada ki damu ki fadamin wane ne wannan da kike wa zaton aljani ne shi?’ wasu hawaye suka fara tararowa kan kumatunta, sannan ta fara magana. ‘Nasani Umma bani da tamkarki, kuma ban taba boye miki wani abu da shafi rayuwata ba. Amma na rasa dalilin da ya sa nake jin shakkar fada miki wannan.’ ‘Uhmmm Nana kenan to koma mene ne fada min kawai kada ki damu, zan fada mafita akan kowane irin al’amari ne.’ Da kyar ta samu damar magana. ‘Wa... wani ne da muka hadu da shi a asibiti.’ Tana fadar haka ta ja linzamin bakinta ta yi shiru, wanda
hakan ya kara jan hankalin Umma ta ce, ‘Ina jin ki, me yayi miki?’ ‘Na kasa mantawa da shi Umma, duk abin da na kalla shi nake gani, shiyasa ma na ce ko aljani ne.’ Murmushi Umma ta yi tare da ajiyar zuciya ta ce, ‘To wannan kad’ai ne abin d’aga hankali? Tukunna ma me ya had’aku?’ ganin yadda Umma ta saki jikinta akan zancen ne ya bata karfin guiwar jin dad’in magana. ‘Kawai dai na shigo kwana ne muka had’e da shi magungunan dake hannuna suka watse wanda a tare muka tsintse, to shi ne Umma na kasa mantawa da shi komai nake yi shi nake gani.’
‘To kin ga kawai ki d’auka d’an sa’bani ne ya shiga tsakaninku kuma ya wuce, don haka sai ki manta kawai.’
Za tayi magana kenan ta katseta ta hanyar d’auko wata magana. Ta ce, ‘Nana yau fa kwana hudu kenan muka ‘kara a cikin wata d’aya a gidan nan, kin manta hayar gidan nan mu ke yi?’ ‘Aa Umma ban manta ba, amma dai ina ce masu gidan ne zasu zo karban kud’i da kansu ba wai mu ne za mu kai mu su ba ko?’ ‘Eh haka ne kam, gani na yi mun ‘kara kusan kwanaki hud’u kuma ba su zo kar’ban kud’in ba.’ ‘Ai kuwa dole za su zo tunda ba kyauta suka ba mu ba, kuma ba mantawa su ka yi ba.’ Suna tsaka da yin maganar ne su ka jiyo muryar almajirinsu Usman yana sallama ya shigo da robar bararsa a hannu Nana ce ta fito ta ganshi. Hararensa ta yi, tana jin haushinsa ta ce, ‘Wato dai Usman ba zaka daina baran nan ba ko?’ Kansa a ‘kasa ya ce, ‘Baaa baa bara naa na fito.’ ‘Ba wurin bara ka fito ba kuma na ganka da wannan shegiyar robar?’ zai sake yin wata magana kenan ta d’aga masa hannu tana cewa, ‘Dakata mallami korafinka ba zai kar’bu ba. Na fad’a maka duk lokacin da kake bu’katar abinci kazo gidan nan ba zan rasa abin da zan baka ba.’ Kafin nan Umma ta fito ta same su tsaye suna wannan. ‘Usman kai ne a gidan namu yau?’ ta fad’a tana kallonsu. Yayi murmushi tare da gaida ita sannan ya fad’a mata ana musu sallama. ‘Nana ki je ki ga wa ke sallama.’ Ya fi wannan fad’an da kike wa d’an bawan Allah. ‘To Umma.’
Ta shiga d’aki ta d’auko hijab d’inta ta fito. A gefen ‘kofar gidan ta tarar da wata mota ‘kirar 4 0 6 kalar madara mai motar na ciki yana jiran isowarta. Ita ma ta yi tsaye daga bakin ‘kofar gidan tana jiran fitowarsa. Sun d’auki tsawon minti biyar kowane na zaman jiran isowar wani. Da ta ga ba ya da niyyar fitowa ta juya zata koma ciki, hakan yasa shi saurin fitowa tare da ambaton sunanta. Juyowa ta yi ta gan shi tsaye. Ta dawo ta yi tsaye tana son jin abin da zai fad’a. Murmushi ya fara yi sannan ya ce, ‘Ke ce Nana ko?’ ta amsa da Eh ni ce Nana wani abu ya faru ne? Wane ne kai?’ ‘Haba syster wacce tambayar zan fara amsawa, ni mutun ne kuma musulmi kamar ke.’ ‘Ba haka nake nufi ba, ka yi hakuri idan tambayar bata ma dad’i ba. Ni zan koma ciki ina da aikin da zan yi.’ Tana gama fad’in haka ta juya zata koma ciki. Da sauri ya ce, ‘Mai wannan gidan ne ya aiko ni.’ ‘Oh my God! Ka yi hakuri ban waye ka ba ne shiyasa. Ai kuwa yanzun nan muka gama maganar gidan nan tare da Umma.’ Sosai ya ke mamakin yadda ‘karamar yarinya ta iya magana cikin alfahari haka. ‘To yanzu dai mai gidan ne ya ce yana son magana da ke, ki biyo ni muje gidansa.’ ‘Wa! Wai ni? In bika mu je a ina?’ ta zare manyan dara-daran idanuwanta farare tana kare masa kallo. Wani murmushin ya ‘kara yi ya ce, ‘ba wani wurin za mu je ba fa, a gidansa ne, idan baki yarda da ni ba zan iya kiran wayarsa ki ji.’ ‘ka yi ha’kuri ba wai ban yarda ba ne, amma ba zan je ko ina ba. Idan ma wata maganar ce da shi to ka fad’a masa ya zo nan, idan kuma kud’in hayan da mu ke yi ne to bara ma na shiga ciki na kar’bo maka a wurin Umma.’
Danna Nan Domin Ci-gaba Da Karanta Na 16 Zuwa 20
Ganin ta dad’e a waje ne ya sa Umma le’kowa. Ta ce, ‘Nana lafiya me ya tsaida ke tun d’azun nake jiranki.’ Kafin ta yi magana Kabir ya yi saurin rusunawa yana gaida Umma. Ta amsa tana kare masa kallo wanda a cikin ranta tana tambayar inda ta san shi. A haka dai ta fito da tambayar a zahiri, ‘Na kasa tuna inda na san fuskar nan.’ Ta fad’a. Shi kuma ya shiga bata labarin abin da ya had’a su har ta san shi yayin da mamaki ya cika Nana fal. ‘Oh! kai ne wai tabbas an yi haka, ka yi ha’kuri saboda na yi saurin mantawa da kai. In ce ko lafiya dai ka zo, me ya ke tafe da kai?’ yayi mata bayanin abinda ya kawo shi. Umma ta ce, ‘To ai wannan ba damuwa ba ne, Nana ku je kawai wannan d’in Yayanki ne ba abin da zai faru dake idan kina tare da shi, ko kuma ki kira Mallam Salihu ya rakaki.’ Cikin mamakin ta ta’be baki ta ce, ‘Aa Umma zan je ba komai tunda kin yarda da shi.’ Tare suka koma cikin gida suka barshi nan tsaye yana jiran dawowarta. Canja kayan jikinta ta yi ta fito suka wuce. Ba su wani dad’e kan hanya ba sai ga su gidan. Ganin katafaren gida had’add’en gaske ne ya sa ta tsorata. Tamkar dai wata ‘yar ‘kauye ta yi tsaye tana kallon irin kyawon gidan. Saura ‘kiris dariya ta ‘kwace ma sa ya ce, ‘kada ki ji tsoron komai, ai tunda kina tare da ni ba abin da zai faru dake da yardar Allah.’ Ya shige gaba tana biye da shi har suka isa cikin gidan. Wani sabon kallo ya cika idanunta ganin yadda cikin gidan ya tsaru fiye da wajensa. A ranta ta ce, ‘Da alamar gidan ba mace, me ya sa haka, kodai.... kai gaskiya da sake’ ‘karaso ciki mana kada ki damu fa.’ Ya katse tunanin da take yi. Da sannu cikin fargaba ta ‘karasa ciki. Sanyin na’ura mai bada yanayin sanyi (AC) ya tarbota ta lumshe ido tana takawa a hankali har ta ‘karasa ciki. Alh Yusuf ta gani zaune shi kad’ai da alama zaman jiran zuwanta yake yi. Da ganinsa lokaci guda ta soma tunawa da inda ta fara ganinsa wanda hakan ya sa ta tsorace ga baki d’aya. Da ‘karfi ta waiwaya baya da nufin ina hanyar fecewa take, suka had’a ido da Kabir yayi dariya sannan ya ce, ‘Kada ki manta da abin da Umma ta fad’a kuma ta fad’i hakan ne don ta yarda da ni, saboda haka ba abin da zai faru dake. Wannan bawan Allah da kike gani baya nufin komai dake face taimakon rayuwarki da cika miki burinki. Saboda haka ki samu wuri ki zauna, ki saurari me ya ke son fad’a.’ Har yanzu Alh. Yusuf na zaune bai ce komai ba, sai murmushi kawai ya ke yi yana shan abin shansa yana ji a ransa burinsa na daf da cika. Maganganun da Kabir ya yi ne ya d’an kwantar mata da hankali ta ‘karasa ciki tare da zaunawa a ‘kasa cikin tsoro-tsoro duk da yake ta d’an yarda da Kabir. Shi ma Kabir wuri ya nema ya zauna.
Bai dad’e zaune ba abokansa suka shigo su uku. Jabir da Mujahid da kuma Abbas. Yana ganinsu ya mi’ke tsaye suna tafawa cikin farin ciki suke masa barka da zuwa yana amsawa da murmushi a fuskarsa. Bayan sun gama gaisawa kowanen su ya nemi wuri ya zauna. ‘Ina ku ka bar Sultan?’ Faruk ya tambaya yana musu kallon ina amsata. Dukansu su ka yi shiru kowanensu ya ‘ki yayi magana. Ganin sun yi zugum kamar ba mai son amsa masa tambayarsa ne ya sa ya ‘kara tambayar su a karo na biyu. Da ‘kyar Abbas ya yi wani dogon numfashi sannan ya ce, ‘Sai dai ka yi ha’kuri amma Sultan ya riga mu gidan gaskiya, Allah sarki Allah ya ji’kansa da rahama.’ A gigice Faruk ya mi’ke tsaye yana ta maimaita salati.
Cikin jimami ya koma ya zauna yana tunanin irin zamantakewar da su ka yi a lokacin ‘kuruciyarsu. Tare su ka mi’ke tsaye su na ta yi masa dariya suna tafawa. Jabir ya ce, ‘Lallai fa Mujahid ka iya April fool kalli yadda ya rikice a d’an ‘kan’kanin lokaci.’ ‘what!? Wai ku na so ku ce April fool... kai! Amma dai kun shammace ni.’ Nan ya fara bin su da duka suka fita waje a guje ya mara mu su baya sai d’akin Babbar Yaya.
Idan da akwai wata kyauta da zaku yi min domin saka ni farin ciki, to ba zata kai ku yi min comment ba. Dan Allah ku yi comment da ra’ayinku akan wannan littafin, idan ya burgeku ko kuma sabanin haka. Haka kuma kada ku manta da Like, wannan ne kad’ai zai karamin karfin guiwa wurin cigaba da kawo muku cigaban wannan littafin.
Mubarak A Kamba
Post a Comment